Majalisa Ta Amince da Hukuncin Kisa ga Masu Garkuwa da Mutane da Yaransu

Majalisa Ta Amince da Hukuncin Kisa ga Masu Garkuwa da Mutane da Yaransu

  • Majalisar Dattawa ta amince da tsaurara hukunci a kan mutanen da aka kama da ta'addanci da bai wa masu garkuwa da mutane bayanan sirri
  • Haka kwamitin majalisa ya fara binciken shirin makaranta domin gano yadda biliyoyin kudin da aka ware saboda tabbatar da tsaro
  • Sanatocin Najeriya sun bayyana cewa babu yadda za a rika kashe makudan kudi amma ba a iya kare ma'aikata da dalibai da kyau

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Majalisar Dattawa, ta dauki mataki mai tsauri ta hanyar amincewa da gyaran dokar ta’addanci ta 2022 domin fadada hukuncin kisa ga duk masu hannu cikin garkuwa da mutane.

Hukuncin zai hau kan masu shirya laifin, ko masu daukar nauyi, ko masu kai rahoto, ko masu bai wa ’yan ta’adda mafaka, ko masu jigilar su, ko duk wanda ya san laifin amma ya taimaka.

Kara karanta wannan

Majalisa ta gaji da jira, ta taso Tinubu a gaba kan masu ɗaukar nauyin ta'addanci

Majalisa na son a kashe yan ta'adda
Zauren majalisar dattawan Najeriya Hoto: The Ngerian Senate
Source: Facebook

The Nation ta wallafa cewa wannan kudiri da Sanata Opeyemi Bamidele ya dauki nauyi, ya nemi a daidaita garkuwa da mutane da sauran laifuffukansu a matsayin ta’addanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa ta gyara dokar ta'addanci

This Day ta wallafa cewa majalisa ta ba wa hukumomin tsaro karin ikon bincike, bibiyar kudin fansa, da fatattakar hanyoyin da ake kai masu kayan aiki da bayanan sirri.

A zaman majalisar da Sanata Godswill Akpabio ya jagoranta, ’yan majalisa daga bangarori daban-daban sun nuna goyon bayan hadin kai.

Sanata Godswill Akpabio ya mika kudirin ga kwamitoci hudu domin su gudanar da sauraron jama’a a cikin makonni biyu.

Majalisa ta ce dole a kawo karshen matsalar tsaro
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio Hoto: The Nigerian Senate
Source: Facebook

A kalamansa, Bamidele ya bayyana cewa garkuwa da mutane yanzu ta zama tsarin tashin hankali da aka mayar kasuwanci kuma aka kware wajen aikata shi.

Sanata Adams Oshiomhole ya goyi bayan kudirin, yana mai cewa shirye-shiryen gyara tunanin yan ta'addan ba su aiki gaba daya.

Kara karanta wannan

Mutane masu alaka da zargin EFCC da Tinubu ya naɗa jakadun kasashen waje

Majalisa ta dura a kan yan ta'adda

Haka kuma Sanata Orji Uzor Kalu da Sanata Victor Umeh sun jaddada cewa duk masu hannu a harkar garkuwa—ko bankuna, ko mutane—dole ne su fuskanci sakamakon laifinsu.

Majalisar Dattawa ta kaddamar da bincike kan shirin bai wa makarantu tsaro domin gano dalilin da ya sa har yanzu makarantu ke fuskantar hare-hare duk da makudan kudin da aka kashe tun 2014.

Sanata Orji Kalu ya bayyana cewa sama da yara 1,680 aka sace, makarantu 180 aka kai wa hari duk da wadannan kudi da aka kashe.

A wani bangare, Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa rundunar ’yan sanda na sake fasalta kanta domin kara ceto rayuwar jama'a.

'Yan majalisa sun nemi a tona asirin 'yan ta'adda

A baya, mun wallafa cewa Majalisar wakilai ta tarayyar Najeriya ta umarci gwamnatin tarayya da ta fito fili ta bayyana sunayen duk mutanen da ke daukar nauyin ta’addanci da garkuwa da mutane a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa sun kafa asusun tsaro, za a rika zubin N1bn a wata

Wannan mataki ya biyo bayan muhimmin zaman tattaunawar tsaro da ’yan majalisar suka gudanar a makon da ya gabata domin dakile yawaitar rashin tsaro da ya gallabi jama'a a sassan Najeriya daban-daban.

'Yan majalisar sun nuna babbar damuwa kan karuwar hare-haren ’yan bindiga da kuma garkuwa da yara a sassa daban-daban na kasar, musamman a cikin 'yan kwanakin nan da lamura suka dagule.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng