Yadda 'Yan Sanda da Sojoji Suka Gwabza Fada Jama'a na Kallonsu a Filato
- An samu hatsaniya tsakanin sojoji biyu da ’yan sanda biyu a wata kasuwa a Ah titin Ahmadu Bello Way, Jos, lamarin da ya jawo tashin hankali
- Shaidu sun ce rikicin ya samo asali ne bayan wani soja ya fusata kan wani dillalin waya, inda rikicin ya rikide zuwa fada tsakanin jami’an tsaro
- Rundunar ’yan sandan jihar Filato ta tabbatar da cewa an shawo kan lamarin, an hukunta wadanda suka yi kuskure, kuma an dauki mataki
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Filato — A ranar Litinin, an ga wani mummunan rikici tsakanin jami’an tsaro inda sojoji biyu da ’yan sanda biyu suka yi dambe a bainar jama’a a wani mashahurin wurin kasuwanci a Ahmadu Bello Way, Jos.
Lamarin ya razana jama’a, musamman ganin cewa rikicin ya afku tsakanin jami’an da ya kamata su kasance masu kula da tsaro da zaman lafiya.

Source: Facebook
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa hatsaniyar ta samo asali ne daga takaddama tsakanin wani soja da dillalin waya a gefen titi, inda abin ya sa wani dan sanda ya shiga tsakani domin hana soja yin abin da ya kudirta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka yi fada tsakanin sojoji da 'yan sanda
Shaidun gani da ido da kuma rubutun wani mai amfani da kafar Facebook, Bello Lukman, sun bayyana yadda lamarin ya fara har ya kai ga amfani da karfi.
Wani shaidan gani da ido ya ce:
“Sojan ya fusata saboda dillalin ya bata masa waya maimakon gyarawa. Ya nemi damke shi amma dan sandan ya hana shi. Dan sandan ya ce ya kai shi ofishin ’yan sanda maimakon ya yi masa barazana.”
Daga nan ne aka ce sojan ya kira abokan aikinsa, wadanda suka iso da motar Hilux cikin hanzari. Rahotanni sun ce sun yi wa dan sandan duka, har suka raunata shi suka kuma kwace bindigarsa.
Wannan lamari ya sa wasu ’yan sanda da ke yankin janyewa daga wurin domin gujewa kara dagula lamarin, yayin da ’yan kasuwa suka fara neman wasu jami’an tsaro su kwantar da tarzomar.
Martanin rundunar ’yan sandan Filato
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, SP Alabo Alfred, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an shawo kan komai. Ya ce an gudanar da bincike, tare da hukunta jami’an da suka saba ka’idoji.
A cewarsa:
“An dauki lamarin da muhimmanci, kuma an hukunta jami’an da suka aikata wannan abin kunya. An dauki matakai domin kaucewa sake faruwar hakan.”
Ya kara da cewa rundunar ’yan sanda ta tabbatar da cewa an warware sabanin da ya faru tsakanin bangarorin tsaro, kuma yanzu komai ya koma daidai.

Source: Facebook
Kakakin rundunar ya kara da cewa kwamishinan ’yan sandan jihar Filato, CP Emmanuel Olubgemiga Adesina, ya yi kira ga jama’a da su cigaba da harkokinsu ba tare da fargaba ba.
Sojoji sun kama 'yan ta'adda sama da 50
A wani labarin, kun ji cewa dakarun rundunar sojin Najeriya ta fitar da sanarwa game da nasarorin da ta samu a kwanaki uku.
Hakan ya biyo bayan luguden wuta da aka yi a jihohi daban daban domin dakile kashe-kashe da satar mutane a kasar nan.
Cikin nasarorin da sojoji suka samu akwai kama 'yan ta'adda sama da 50, kashe wasu da kuma kwato tarin makamai.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


