Tsohon Sanata daga Zamfara Ya Amince Amurka Ta Kawo Farmaki Najeriya
- Kabiru Garba Marafa ya ce babu amfanin 'yancin da Najeriya ke da shi idan aka wayi gari mutanen cikinta sun rasa rayukansu
- Tsohon Sanatan Zamfara ta Tsakiya ya bayyana cikakken goyon bayansa ga barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi na kawo hari Najeriya
- Ya ce duk da ra'yinsa ya sha banban da sauran 'yan Najeriya, amma barazanar Trump ta tashi gwamnatin Najeriya daga barci
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Tsohon dan Majalisar Dattawa daga jihar Zamfara, Sanata Kabiru Marafa ya bayyana ra'ayinsa kan barazanar shugaban Amurka, Donald Trump ta kawo farmaki Najeriya.
Shugaba Trump ya bayyana cewa da yiwuwar sojojin Amurka su kawo dauki Najeriya domim yaki da 'yan ta'adda masu yi wa kiristoci kisan kare dangi a kasar.

Source: Twitter
Kabiru Marafa ya goyi bayan Donald Trump

Kara karanta wannan
"Ba Trump ba ne": Sanata Yari ya gano mutanen da za su magance matsalolin Najeriya
Sanata Marafa ya fito ya goyi bayan shirin Shugaba Trump na Amurka yayin da ake hira da shi a cikin shirin Politics Today na tashar Channels tv ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idan ba ku manta ba Shugaba Trump ya maida Najeriya cikin jerin kasashen da ke tauye 'yancin addini saboda zargin da yake ana yi wa kiristoci kisan kiyashi.
Bayan wannan mataki, Trump ya kuma umarci ma'aikatar yaki ta Amurka ta tsara yiwuwar kai farmaki Najeriya domin kakkabe 'yan ta'adda masu tsattsauran ra'ayin islama.
Donald Trump ya jaddada cewa Amurka ba za ta nafe hannu tana kallo ana kokarin karar da kiristoci a Najeriya ba, don haka dole ta dauki mataki.
Gwamnatin Najeriya dai ta musanta zargin yi wa kiritoci kisan kare dangi, inda ta maida martani da cewa Amurka ba ta samu hakikanin bayanan abin da ke faruwa a kasar nan na.
Me yasa Sanatan ya saba wa 'yan Najeriya?
Da yake tsokaci kan wannan lamari, Sanata Kabiru Marafa, wanda ya wakilci Zamfara ta Tsakiya a Majalisar Dattawa daga 2011 zuwa 2019, ya bayyana goyon baya ga Shugaba Trump.
Ya ce duk da ra'ayinsa ya banbanta da sauran mutane musamman shugabanni a Najeriya, yana mai cewa matsalar tsaron kasar na na bukatar a kawo dauki.
“Ina goyon bayan Shugaban Amurka, Donald Trump, matuka kan wannan barazana da ya yi ta kawo farmaki Najeriya," in ji shi.

Source: Twitter
Duk da ya san ra’ayinsa ya sabawa na yan Najeriya da dama, amma ya bayyana cewa:
"Yawancin ’yan Najeriya suna kallon batun ne daga bangaren 'yancin kasa, kishin kasa, wanda nima ina goyon baya. Amma meye amfanin 'yancin kasa ga mutumin da ya mutu?”
A cewar Marafa, barazanar Shugaba Trump ta matsa wa gwamnatin Najeriya lamba wajen daukar matakan gaggawa kan matsalar tsaro da ke addabar kasar.
Amurka za ta hana wasu 'yan Najeriya biza
A wani rahoton, kun ji cewa Amurka ta fara daukar matakai da nufin kawo karshen kisan kiyashin da take zargin ana yi wa kiristoci a Najeriya da wasu kasashe
Gwamnatin Amurka ta sanya takunkumin hana biza ga duk mutanen da suka jagoranta, suka ba da izini ko suke goyon bayan tauye ’yancin addini a Najeriya.

Kara karanta wannan
Ba wasa: Matakin da Gwamna Abba zai dauka don dakile hare haren 'yan bindiga a Kano
Ta jaddada cewa kamar yadda Shugaba Donald Trump ya fada, Amurka za ta yi duk mai yiwuwa wajen kare rayukan kiristoci a duniya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
