Tashin Hankali: Mota Dauke da 'Yan Firamare Ta Yi Hatsari, Ta Afka cikin Teku
- Yara huɗu daga garin Egbolo sun mutu bayan motar da ta dauko su ta yi hatsari, ta afka cikin teku a lokacin da suke hanyar makaranta
- Mutuwar yaran ta jefa al'ummar Egbola a cikin tashin hankali, lamarin da ya fusata su har suka toshe hanyar garin suna zanga zanga
- Mazauna garin sun zargi gwamnatin jihar Kogi da watsi da yankin, wanda ya tilasta wa yara zuwa garuruwan makwabta don neman ilimi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kogi - A kalla yara huɗu daga kauyen Egbolo, karamar hukumar Igalamela-Odolu a jihar Kogi, suka rasa rayukansu a ranar Litinin, 1 ga watan Disamba, 2025.
Rahotanni sun bayyana cewa yaran hudu, wadanda dukkansu 'yan firamare ne sun mutu a lokacin da wata babbar motar da suka hau zuwa makaranta ta faɗa cikin kogi.

Source: Original
Lamarin ya faru ne kusan ƙarfe 8:30 na safe, inda mazauna yankin suka shiga ihun neman taimako yayin da suke fito da yara daga ƙarƙashin motar, in ji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fusatattun mutane sun yi zanga-zanga a Kogi
An ruwaito cewa wasu daliban sun samu munanan raunuka daban-daban, hakan ya jefa al’umma cikin tashin hankali da alhini.
Bayan faruwar hatsarin, mazauna yankin sun toshe babbar hanya suna zanga-zanga, suka zargi gwamnati da kin gina masu makaranta a yankinsu, wanda a cewarsu, shi ne ya tilasta yara hawan motocin da ba su da inganci suna zuwa makaranta.
Iyaye sun yi ikirarin cewa yaran su na yin doguwar tafiya a kan hanya mai haɗari zuwa garin Ofuloko domin samun ilimin firamare.
Wani mahaifi da ya rasa ɗansa a wannan sabon hatsarin ya zargi gwamnati da watsi da al’ummar Egbolo tsawon shekaru ba tare da kawo masu wani tsari na ilimi ba.
Mota dauke da dalibai ta afka kogi
Usman Idrisu, shugaba matasa na kauyen, ya bayyana cewa hatsarin ya afku ne lokacin da wata mota da ke ɗauke da kayan gini ta ɗebi daliban zuwa makarantar Ofuloko.
Ya ce motar ta zo dai dai wani hawa, sai ta gaza haye hawan saboda rashin karfin inji bayan ta tsallake wata gada, lamarin da ya sa ta rika dawo wa baya cikin gudu, har dai ta wuntsula ta faɗa cikin kogin da ke ƙasan gadar da ta tsallake.
Usman Idrisu ya ce al’umma sun shiga tashin hankali kasancewar yara huɗu sun mutu, yayin da wasu da dama suka ji munanan raunuka, in ji jaridar nan ta Punch.

Source: Facebook
An roki gwamnati ta gina makaranta a Egbolo
Shugaban matasan ya yi kira ga Gwamna Ahmed Usman Ododo da ya gina makarantar firamare a Egbolo, yana mai cewa yankin na da jama’a masu yawa amma babu wurin koyon karatu.
TVC News ta ruwaito cewa an kai waɗanda suka jikkata zuwa asibiti mafi kusa domin kula da su, yayin da jami’an kiyaye hadurra suka taimaka wajen saukaka cunkoso da ci gaba da aikin ceto.
Rahotanni sun nuna cewa hatsarin ya sake nuni da mahimmancin samar da tsaro da ingantaccen sufuri ga yaran da ke neman ilimi a yankunan karkara.
'Yan bindiga sun je sace dalibai a Kogi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, mutum biyu sun rasa rayukansu lokacin da wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka kai hari makarantar Kiri da ke jihar Kogi.
An ji cewa Shugaban karamar hukumar Kabba Bunu, Barista Zacheus Dare, ya tabbatar da faruwar lamarin a zantawarsa da manema labarai washe garin harin.
Shugaban karamar hukumar ya ce sojoji, ‘yan sanda, mafarauta da sauran jami’an tsaro na ci gaba da aikin farautar ‘yan bindigar a daji domin hana su dawowa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


