'Yan Bindiga Sun Shiga Uku, NEC Ta Ware Naira Biliyan 100 don Gyara Wasu Cibiyoyi a Najeriya

'Yan Bindiga Sun Shiga Uku, NEC Ta Ware Naira Biliyan 100 don Gyara Wasu Cibiyoyi a Najeriya

  • Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa (NEC) ta amince da gyaran cibiyoyin horas da 'yan sanda, sojoji da sauran jami'an tsaron Najeriya
  • Wannan mataki na zuwa ne bayan kwamitin wucin gadi da aka kafa don binciko halin da cibiyoyin ke ciki ya mika rahotonsa yau Laraba
  • Shugaban majalisar NEC kuma mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ja hankalin gwamnoni kan inganta rayuwar talakawa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta kara zage dantse wajen inganta ayyukan jami'an tsaro a kokarinta na kawar da duk wata barazanar tsaro a Najeriya.

Domin inganta ayyukan tsaro, Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa (NEC) ta ware biliyoyin Naira domin gyara cibiyoyin horas da 'yan sanda, sojoji da sauran jami'an tsaro.

Taron NEC.
Mataimakin shugaban kasa tare da wasu mambobi a taron Majalisar Tattalin Arziki (NEC) Hoto: @stanleyokwocha
Source: Twitter

Majalisar NEC ta amince da ware N100bn

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa NEC ta amince da kashe Naira biliyan 100 domin gyaran cibiyoyin horas da ’yan sanda da sauran jami’an tsaro a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

Ba wasa: Matakin da Gwamna Abba zai dauka don dakile hare haren 'yan bindiga a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NEC ta yanke wannan shawara ne bayan karbar rahoton kwamitin wucin-gadi da aka kafa don tantance halin da cibiyoyin horas da jami'an tsaron kasar ke ciki.

A zaman ta na 154 ta fasahar zamani a ranar Laraba, majalisar ta kuma amince da ware Naira biliyan 2.6 domin biyan kudin masu ba da shawara da za su jagoranci aikin.

A baya dai, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kudurin sake fasalin cibiyoyin horaswa na hukumomin tsaro a taron NEC na 152 da aka gudanar a watan Oktoba, 2025.

Za a gyara cibiyoyin horas da jami'an tsaro

Gwamnan Jihar Enugu, Peter Mbah, wanda shi ne shugaban kwamitin, ya bayyana cewa cibiyoyin daukar horon sun lalace matuka kuma suna bukatar gyara cikin gaggawa.

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, wanda ke jagorantar Majalisa NEC, ya ce gwamnati na da cikakken kwarin guiwa wajen gyara matsalar da cibiyoyin ke fuskanta.

Kara karanta wannan

Wasu manyan matsaloli 5 da Janar Musa zai fuskanta idan ya zama ministan tsaro

Ya kuma bukaci gwamnonin jihohi su tabbatar sun yi amfani da sauye-sauyen tattalin arziki zuwa a matsayin hanyar inganta rayuwa ga al’umma, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Shettima ya jaddada cewa shugabanci na gari ba wai a fadin manufofi masu dadin sauraro ba ne, sai dai a sakamakon da al’umma ke gani a zahiri.

Mataimakin shugaban kasar ya ce:

“Aikinmu ba wai mu zauna mu tattauna kan matsaloli ba ne, sai dai mu warware su. Ba wai mu fadi dalilan kalubale ba ne, amma mu shawo kansu, ba mu yi ta buri ba ne, mu lalubo hanyar ganin sun tabbata."
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima a taron NEC Hoto: @OfficialSKSM
Source: Twitter

Ya kara da cewa dole ne a tabbatar da cewa duk wani sauyi da gwamnati ke aiwatarwa ya bayyana karara a kasuwanni, makarantun yara, cibiyoyin lafiya da kuma gonaki.

Majalisa ta amince da nadin Ministan Tsaro

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar dattawa ta tabbatar da Janar Christopher Musa a matsayin ministan tsaron Najeriya bayan kwashe awanni ana tantance shi.

Rahoto ya nuna cewa Sanatoci sun shafe akalla awanni biyar suna yiwa Janar Musa tambayoyi, a lokacin da suke tantance shi a ranar Laraba, 3 ga Dismaba, 2025.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamnati ta yi bayani kan dokar hana acaba, an yi sassauci a wasu yankuna

Bayan kammala tambayoyi, Akpabio ya bukaci majalisa ta kada kuri'ar murya kan amincewa da nadin Musa ko akasin haka, kuma sanatoci suka amince da nadinsa baki daya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262