A ƙarshe, Majalisa Ta Amince da Naɗin Janar Christopher Musa a matsayin Ministan Tsaro
- Majalisar dattawa ta tabbatar da Janar Christopher Musa a matsayin ministan tsaron Najeriya bayan kwashe awanni ana tantance shi
- A yayin amsa tambayoyi, Janar Musa ya ce matsalolin tsaron Najeriya ba na sojojoji kadai ba ne, dole ana bukatar hadin kan kowane bangare
- Tsohon sojan ya yi kira da a daina biyan kudin fansa, yana mai cewa tattaunawa da ’yan ta’adda na ba su karfin sayan makamai ne kawai
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Majalisar dattawa ta amince da nadin tsohon hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya a matsayin sabon ministan tsaro.
Ƴan majalisar dattawan sun shafe akalla awanni biyar suna yiwa Janar Musa tambayoyi, a lokacin da suke tantance shi a ranar Laraba, 3 ga Dismaba, 2025.

Source: Twitter
Janar Musa ya amsa tambayoyin sanatoci

Kara karanta wannan
Ministan tsaro, Janar Musa ya ware gwamnoni 6 da suka yi fice a kokarin samar da tsaro
Channels TV ta rahoto cewa, majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Christopher Musa ne kwana ɗaya bayan Shugaba Bola Tinubu ya nada shi a wannan muƙami.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatoci sun yi nazari sosai kan tarihin Janar Musa, gogewarsa a fagen soja, da kuma jawabinsa game da matsalolin tsaron da ke barazana ga kasar.
A yayin tantancewar, tsohon hafsan tsaron kasar ya yi alkawarin yin aiki cikin sadaukarwa domin kare Najeriya daga duk barazana da kuma tabbatar da zaman lafiya.
A cewarsa:
“Kalubalen tsaro ba na sojoji ko ’yan sanda kadai ba ne. Matsalar Najeriya ce gaba ɗaya. Idan mu ka hada kai tare, za mu yi nasara.”
Ya ce yana da niyyar ci gaba da amfani da tsarin hadin gwiwa da ya faro tun lokacin da yake hafsan tsaro, domin kawar da gibin da ya bayyana cewa yana kawo tsaiko ga ayyukan tsaro.
CG Musa ya ba da muhimman shawarwari
Janar Christopher Musa ya yi kira da a samar da cikakken kundin bayanai a Najeriya, wanda zai taimaka wa hukumomin tsaro wajen tantance bayanan mutane da gano barazana cikin sauki.
Ya kuma jaddada cewa dole ne hukumomin kananan hukumomi da na jihohi su zama masu taka rawar gani wajen magance matsalar tsaro, in ji rahoton The Cable.
Ya yi kira da a kawo karshen biyan kudin fansa ga ’yan bindiga, ’yan ta’adda da masu satar mutane, yana mai cewa tattauna wa da su babban kuskure ne.
“Ba a taba cin moriyar tattaunawa da su. Duk kudin da ake basu don fansa sukan yi amfani da shi wajen siyan makamai."
- Janar Christopher Musa.

Source: Twitter
Majalisa ta amince da nadin Janar Musa
Game da jita-jitar zargin kisan gillar masu addinin Kirista a Najeriya, Musa ya ce matsalar ta shafi kowa, ba addini daya ba.
“Dukkanmu mun zama wadanda abin ya shafa. Wadannan miyagu ba su bambancewa. Mutane ne masu shaye-shaye da mugunta, suna hallaka kowa,” in ji Christopher Musa.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Akpabio, ya yaba da irin yadda Musa ya amsa dukkan tambayoyin da aka yi masa, yana mai cewa tun 1999 ba a taba samun wanda ya yi karin bayani sosai kamar shi ba.
Bayan kammala tantancewa, Akpabio ya bukaci majalisa ta kada kuri'ar murya kan amincewa da nadin Musa ko akasin haka, kuma sanatoci suka amince da nadinsa baki daya.
Sabon Ministan Tsaron ya bayyana cewa nan da nan zai fara aiki domin tabbatar da ingantaccen tsaro a kasar.
Rigima ta tashi wajen tantance minista a majalisa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, rikici ya tashi a majalisar dattawa yayin da ake tantance Janar Christopher Musa a matsayin sabon ministan tsaro.
'Yan majalisa sun tashi tsaye cikin fushi, lokacin da wani sanata ya nemi a kyale Janar Musa mai ritaya ya yi gaisuwa ya tafi kawai ba tare da an yi masa tambayoyi ba.
Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio ya yanke hukunci cewa dole ne ya amsa tambayoyin da 'yan Najeriya ke da su, ba don ba ta sonsa ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

