Ba Wasa: Matakin da Gwamna Abba Zai Dauka don Dakile Hare Haren 'Yan Bindiga a Kano

Ba Wasa: Matakin da Gwamna Abba Zai Dauka don Dakile Hare Haren 'Yan Bindiga a Kano

  • A cikin 'yan kwanakin nan wasu kauyukan jihar Kano sun fuskanci hare-haren 'yan bindiga da ke shigowa daga makwabtan jihohi
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta sayo kayan aiki domin tunkarar matsalar da gaggawa tun da wuri
  • Ya bukaci al'umma da su rima taimakawa hukumomin tsaro da bayanai masu muhimmanci kan motsin 'yan bindiga

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana shirin gwamnatinsa kan matsalar rashin tsaro.

Gwamna Abba ya ce gwamnati za ta sayi jirage marasa matuka da wasu kayayyakin aiki domin karfafa sa ido da gaggawar daukar mataki a yankunan kan iyaka da ke fuskantar hare-haren 'yan bindiga.

Gwamnatin Kano za ta sayo kayan aiki kan 'yan bindiga
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a ofis Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Tofa, ya fitar a ranar Laraba a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba Kabir ya ziyarci wuraren da aka yi artabu da 'yan bindiga a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai ziyara

Sanarwar ta ce gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da ya duba shirin tunkarar hare-hare na jami’an rundunar Joint Task Force (JTF) a sansanoninsu uku da ke Tsanyawa da Shanono.

Ziyarar ta biyo bayan watanni da dama na karuwar rashin tsaro a kan iyakar Kano da Katsina, inda hare-haren 'yan bindiga ya kara kamari, lamarin da ya sa hukumomi suka kara yawan jami’an tsaro a yankin.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bukaci mazauna yankunan da abin ya shafa da su rika bai wa jami’an tsaro bayanai masu muhimmanci kan motsin 'yan bindiga don dakile hare-hare.

Ya kuma bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da bukatunsa bayan ya sanar da shi halin da ake ciki tare da neman goyon bayan gwamnatin tarayya.

Wani mataki gwamna Abba ya dauka?

Gwamnan ya umarci jami'an rundunar JTF da su kara zage damtse wajen ganin cewa an kubutar da mutanen da aka sace a Tsanyawa da Shanono.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Nasarawa ta ciri tuta kan batun 'yan sandan jihohi

“Mun sani cewa suna kai hare-hare kan al’ummomin da ba su ji ba, ba su gani ba musamman a Tsanyawa da Shanono. An kashe mutane da dama, kuma an yi awon gaba da wasu da dama zuwa daji."
"Za mu sayi jirage marasa matuka da sauran kayan aiki domin sa ido da hanzarta kai dauki a yankunan kan iyaka.”
“Ina tabbatar muku, da ikon Allah, wadanda aka sace za a dawo da su cikin koshin lafiya.”

- Gwamna Abba Kabir Yusuf

Gwamna Abba ya kai ziyara kan hare-haren 'yan bindiga
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Twitter

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce ziyararsa ta yi nufin tantance halin da ake ciki, tattaunawa kai tsaye da jami’an tsaro da kuma karfafa musu guiwa domin ci gaba da aikin ceton rayuka.

'Yan bindiga sun kai hare-hare a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci a wasu kauyukan jihar Kano.

'Yan bindigan sun kai hare-haren ne a kauyuka guda biyu da ke karamar hukumar Shanono da tsakar dare.

Hare-haren 'yan bindiga sun jawo an yi awon gaba da akalla mutane 25 yayin da aka raunata wasu mutum biyu daban.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng