Shugaban Kasa Bola Tinubu Zai Jagoranci Babban Taron Jam'iyyar APC a Abuja
- Jam’iyyar APC ta sanar da ranakun da za a gudanar da babban taronta a fadar shugaban kasa, inda ake sa ran tattauna muhimman batutuwa
- Shugaba Bola Tinubu, Mataimakinsa Kashim Shettima, Kakakin Majalisa da Shugaban Majalisar Dattawa na daga cikin wadanda ake sa ran za su halarci taron
- Jam'iyyar APC ta tunatar da 'ya'yanta da su shirya halartar babban taron da ake tunanin zai tattauna game da makomar jam'iyya yayin da 2027 ke karatowa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jam’iyyar APC ta fitar da jadawalin gudanar da mahimman taruka guda biyu da za a yi a dakin taro na Banquet Hall da ke fadar shugaban kasa, Abuja.

Source: Twitter
A yau The Cable ta wallafa cewa wannan na daga cikin wata sanarwa da sakataren jam’iyya na kasa, Ajibola Bashiru, ya fitar ranar Laraba.
Jam'iyyar APC ta fara shirin babban taro
Jaridar Punch ta wallafa cewa an bayyana cewa za a gudanar da taron farko a ranar Litinin, 15 ga Disamba, 2025 da misalin 6.00 na yamma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta kara da cewa za a kuma gudanar da taron majalisar koli na NEC a ranar a Talata, 16 ga Disamba 2025, da karfe 12.00 na rana.

Source: Facebook
Sanarwar ta ce dukkanin manyan kusoshin jam’iyya da gwamnati za su halarci wadannan muhimman taruka domin tattauna kalulabe da sauran al'amura a cikin jam'iyya.
Ana sa ran cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai jagoranci taron, tare da Mataimakinsa Kashim Shettima, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, da Shugaban Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas.
Manyan APC za su hallara a Abuja
Haka zalika, gwamnonin jihohi da sauran ’yan majalisar tarayya da ke jam'iyyar APC za su halarci babban taron na kasa.
A cewar Ajibola Bashiru:
“Dukkannin kwamitin amintattu, su dauki wannan kira a matsayin cikar tanadin kundin tsarin jam’iyya, bisa ga Sashe na 12.5 na tsarin APC.”
Jam’iyyar ta jaddada cewa wadannan taruka na zuwa ne a lokaci mai matukar muhimmanci, ganin yadda ake shirin sake fasalin ayyuka da tsare-tsaren siyasa na shekarar 2026 da ke gabatowa.
Sanarwar ta kuma bukaci 'ya'yanta su tabbatar sun halarta ba tare da bata lokaci ba, domin muhimman batutuwa da suka shafi makomar APC.
Gwamna mai shirin shiga APC ya ga Tinubu
A baya, mun wallafa cewa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya karbin bakuncin gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja bayan shirin da ya ke na komawa APC.
Shugaba Tinubu ya yi ganawa ta musamman da Gwamna Kefas, wanda ya kwanan nan ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulkin kasar nan, amma aka jinkirta bikin komawarsa.
An soke gangamin taron sauya shekar da aka shirya yi a Jalingo ne a daidai lokacin da aka yi garkuwa da dalibai a jihar Kebbi da kuma wasu mabiya addinin Kirista a Majami’a a Jihar Kwara.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

