Fadar Shugaban Kasa Ta Yi Magana game da Sulhu da 'Yan Ta'adda
- Fadar Shugaban Kasa ta bayyana matsayarta a kan sulhu da 'yan ta'adda ko shiga wata yarjejeniya domin ceto wadanda aka yi garkuwa da su
- Hadimin shugaban kasa a kan sadarwa, Daniel Bwala, ya bayyana akwai lokacin da gwamnatin tarayya ta taba hawa teburin tattaunawa da 'yan ta'adda.
- Bwala ya ce gwamnan Kaduna na wancan lokaci ya taba neman a samar da doka ta kasa da za ta ba gwamnoni da gwamnatin tarayya ganawa da 'yan ta'adda
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan sadarwa, Daniel Bwala, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta na tsayawa tsayin daka a kan manufar.
Lauyan ya nanata cewa gwamnatin tarayya ta yi tsayin daka a kan batun tabbatar da tsaron 'yan Najeriya da kare su daga barazanar 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun bude wa tawagar gwamna wuta a titin filin jirgi? An ji abin da ya faru

Source: Twitter
Hadimin shugaban kasa ya yi bayanin ne a wata hira da ya yi da Channels TV, inda ya ce Bola Tinubu ba zai taba shiga wata yarjejeniya da 'yan ta'adda ba.
Gwamnati ta magantu kan sulhu da 'yan ta'adda
Jaridar The Cable ta wallafa cewa Bwala ya ce Najeriya tana fuskantar matsalolin tsaro masu wahalar sha'ani, wanda wani lokaci ke tilasta wa gwamnati daukar matakan da ba a saba da su ba.
Ya ce:
“A baya, an samu lokacin da gwamnatin tarayya ke tattaunawa da ‘yan ta’adda, kuma na yi tunanin El-Rufai, tsohon gwamnan Kaduna ya taba magana kan manufar kasa a lokacin, inda aka ce jihohi da gwamnatin tarayya na iya shiga tattaunawa da 'yan ta'adda idan ta kama.”
Sai dai ya kara da cewa Shugaba Tinubu ya kawo manufar babu sassauci kan tattaunawa domin wannan na iya zama hanyar tallafawa ta’addanci.
Gwamnati ta fadi illar biyan kudin fansa
Daniel Bwala, hadimin shugaban kasa ya bayyana cewa idan aka biya 'yan ta'adda kudin fansa, za su iya amfani da su wajen sayen makamai maimakon ceto wadanda aka sace.
Bwala ya ce:
“Gwamnatin tarayya ba ta amince da tattaunawa da 'yan ta'adda ba, saboda idan an bi hanyar tattaunawa, za ka tallafawa ta’addanci bisa rashin sani."

Source: Twitter
Bwala ya bayyana cewa a lokuta da dama, hukumomin tsaro na iya ceton wadanda aka sace ba tare da biyan kudin fansa ba.
Ya kara da cewa a wasu lokuta masu gungun jama’a ko shugabannin addini na iya shawo kan masu garkuwa da mutane su saki wadanda aka sace.
“Haka kuma, wasu lokuta jami’an tsaro suna bin diddigin wurin da ‘yan ta’addan suke, amma ba za su iya kai hari ba saboda akwai fararen hula a wurin, abin da ke tilasta su bayar da gargadi wanda daga karshe ke tilastawa masu garkuwa da mutane su saki wadanda aka sace."
An magantu kan biyan 'yan ta'adda fansa
A baya, mun wallafa cewa Majalisar kasa ta yi magana bayan yada jita-jitar cewa gwamnatin tarayya ta biya ’yan bindiga kudin fansa kafin a sako daliban da aka sace a jihohin Kebbi da Neja.

Kara karanta wannan
Nuhu Ribadu ya gana da wakilan CAN da iyayen daliban Neja, an ji abin da suka tattauna
Majalisar Dattawan Najeriya ta fito karara ta karyata zargin, tare da bayyana cewa gwamnati ba ta biya ko sisi ba domin a sako daliban, inda ta ce babu lokacin da aka biya yan ta'adda ko sisi.
Mai magana da yawun Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu, ya ce babu gaskiya a ikirarin da ake yi cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta biya kudi ga miyagun don karbo yaran.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
