Majalisa Ta Sa Lokacin Tantance Janar Christopher Musa a matsayin Ministan Tsaro

Majalisa Ta Sa Lokacin Tantance Janar Christopher Musa a matsayin Ministan Tsaro

  • Alhaji Mohammed Badaru Abubakar ya yi murabus daga mukaminsa na Babban Ministan tsaron Najeriya saboda dalilan da suka danganci lafiya
  • Biyo bayan haka, shugaban kasa ya mika sunan Janar Christopher Musa mai ritaya ga majalisar dattawa a matsayin wanda ya zaba don maye gurbinsa
  • Bayan karbar wasikar da shugaban kasar ya aika mata, majalisar dattawa ta sanar da lokacin da za ta tantance Christopher a matsayin sabon Ministan tsaro

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Majalisar Dattawa ta sanya lokacin tantance sabon Ministan tsaron da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zaba don ya rike kujerar.

Majalisar dattawan ta sanya ranar Laraba, 3 ga Disamba, 2025, don tantance Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya) a matsayin sabon Ministan tsaro.

Majalisa dattawa za ta tantance Christopher Musa
Sanatoci a majalisar dattawa da Janar Christopher Musa Hoto: @HQNigerianArmy, @SenateNGR
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ofishin harkokin yada labarai na majalisar ya fitar a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamnati ta yi bayani kan dokar hana acaba, an yi sassauci a wasu yankuna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nadin Janar Christopher Musa mai ritaya ya biyo bayan murabus din da tsohon Ministan tsaro, Alhaji Mohammed Badaru, ya yi.

Majalisa ta karbi bukatar Shugaba Tinubu

A cewar Bamidele, majalisar dattawa ta riga ta karɓi bukatar da shugaban kasa kuma kwamandan sojojin Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya aiko domin tantance sabon Ministan tsaro, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar da hakan.

Ya kara da cewa, za a karanta wasikar a zaman majalisar na ranar Laraba, daga nan kuma majalisar za ta shiga tantancewa nan take, bisa ka’idar da kundin tsarin mulki na 1999 (sashi na 147) ya tanada.

“Ba za mu iya jinkirta irin wannan bukata ba musamman a wannan lokaci da kasar mu ke fuskantar kalubale."
"Wannan batu na da matukar muhimmanci wajen ci gaba da yaki da ‘yan bindiga, masu tsattsauran ra’ayi, ‘yan ta’adda da sauran miyagun da ke barazana ga tsaron kasa."

- Sanata Opeyemi Bamidele

Kara karanta wannan

Jigon APC ya fadawa majalisa mutum 1 da ya kamata a cire a jerin sababbin jakadu

Ya kara da cewa, kasancewar shugaban kasa ya ayyana dokar ta-baci a fannin tsaro, dole bangaren zartarwa da majalisar dokoki su yi aiki kafada da kafada domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa.

“Tantance sabon Ministan tsaro wata hanya ce ta nuna irin wannan hadin kai domin amfanin kasa baki daya.”

- Sanata Opeyemi Bamidele

Za a tantance Christopher Musa a zauren majalisar dattawa
Sabon Ministan tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya) Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Chiristopher Musa zai maye gurbin Badaru

Janar Musa mai ritaya ya bar mukaminsa na babban Hafsan Hafsoshi (CDS) kusan makonni biyar da suka gabata, a ranar 30 ga Oktoban 2025.

Nadinsa ya zo ne sa’o’i kadan bayan Badaru, wanda ya rike mukamin tun 2023, ya yi murabus.

Kafin tsohon gwamnan ya hakura da kujerarsa, an ji yadda Ministan kimiyya da fasaha da ake zargi da badakalar takardu, Geoffrey Uche Nnaji ya yi murabus.

Shugaba Tinubu ya gana da hafsoshin tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da hafsoshin tsaro a fadarsa da ke Aso Rock Villa a birnin tarayya Abuja.

Hafsoshin sun isa fadar shugaban kasa inda suka sanya labule ba tare da an bar ’yan jarida sun halarci zaman ba.

Kara karanta wannan

Bayan nada sabon minista, Tinubu ya shiga taron gaggawa da manyan hafsoshin tsaro

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai shugaban rundunar sojin kasa, Laftanar Janar W. Shaibu, shugaban rundunar sojin sama, AVM Sunday Aneke, da shugaban sojin ruwa, Vice Admiral I. Abbas.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng