Wasu Manyan Matsaloli 5 da Janar Musa Zai Fuskanta idan Ya Zama Ministan Tsaro
- Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Janar Christopher Musa, tsohon babban hafsan tsaron Najeriya a matsayin sabon ministan tsaro
- Masana tsaro sun ce wannan naɗin zai kawo haɗin kai tsakanin rundunonin tsaro da sabon tsari na magance matsalolin tsaro a ƙasar
- Legit Hausa ta tattaro wasu manyan kalubale biyar da Janar Musa zai iya fuskanta, ciki har da batun kawo sauyi a ma'aikatar tsaro
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Idan har ba wai an samu wani sauyi ba, to tsohon shugaban hafsoshin tsaron Najeriya (CDS), Janar Christopher Gabwin Musa (rtd), ne zai zama sabon Ministan Tsaro.
Wannan kuwa zai faru ne bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mika sunansa ga majalisar dattawa domin tantancewa da tabbatarwa, kamar yadda Legit Hausa t rahoto.

Source: Facebook
Nadin Christopher ya zo ne kusan makonni biyar bayan ritayarsa daga aiki a ranar 30 ga Oktoba, a cewar rahoton jaridar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilan Tinubu na nada Janar Christopher Musa
A cewar wata maiya mai ƙarfi a fadar shugaban ƙasa, shawarwari daga wasu ministoci da manyan jami’an gwamnati ne suka janyo tunanin dawo da Musa cikin Gwamnati.
Ministoci da jami'an gwamnatin sun ba da shawarar dawo da Musa ne bayan sun yi la'akari da yadda matsalolin tsaro suka ƙara ta’azzara a kasar, musamman Arewa.
Wata majiyar tsaron ta bayyana cewa an bukaci shugaban ya naɗa wanda ya fito daga rundunar soji kai tsaye, wanda ya fahimci yanayin yaƙin zamani, dabarun hare-hare da kariya, da yadda ake tunkarar ƙungiyoyin ‘yan ta’adda.
Wasu sun yi tsokaci cewa kasancewar Musa ya bar aiki kwanan nan ya sanya ya fahimci ainihin kalubalen rundunar soji, tare da sanin karfi da raunin tsarin tsaro da ke akwai yanzu.
Masu sharhi sun yaba da naɗin Janar Musa
Birgediya Janar Mohammed Kabir Galadanchi (mai ritaya) ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa Musa na ɗaya daga cikin manyan hafsoshin da suka fi fahimtar tsare-tsaren yaki da ta’addanci a Najeriya.
A cewar Janar Galadanci:
“Muna bukatar wanda ya san tsarin soji da yadda za a tunkari 'yan ta'adda. Musa ya kasance masanin dabaru, da hanyoyin warware matsalolin tsaro na tsawon shekaru.”
Galadanchi ya ce sababbin hafsoshin tsaro – CSO, COAS, CNS, da CAS – sun yi aiki ƙarƙashin Musa a baya, don haka akwai kyakkyawan fata cewa za su yi aiki da shi cikin sauki, hakan kuma zai taimaka wajen inganta haɗin kai da saurin daukar matakai.
A nasa bangaren, Babban Edita na jaridar PRNigeria, Yushau A. Shuaib, ya ce:
“Janar Musa ya yi fice wajen inganta hulɗa tsakanin hukumomin tsaro, da kuma kasashe makwabta, musamman a lokacin da yake shugaban hafsoshin tsaro na ECOWAS.
Kalubale 5 da ke jiran sabon Ministan tsaro
Idan aka tabbatar da nadin Musa a matsayin ministan tsaro, zai fuskanci jerin matsaloli masu nauyi:
1. Karuwar ta’addanci a Arewa maso Yamma
Yawaitar hare-haren ‘yan bindiga, sace mutane a hanyoyi, da kai-kawon barayin shanu sun zama ruwan dare a jihohi kamar Katsina, Zamfara, Kebbi da Sokoto.

Kara karanta wannan
Tsohon hafsan tsaro, Janar Irabor ya fadi 'yan siyasa masu rura wutar matsalar tsaro
2. Dawowar Boko Haram/ISWAP a Arewa maso Gabas
Duk da an shafe shekaru da dama ana yaki da Boko Haram / ISWAP, har yanzu kungiyoyin suna kai hare-hare a Borno, Yobe da Adamawa.

Source: Facebook
3. Garkuwa da mutane a Arewa ta Tsakiya
Jihohi kamar Niger, Kogi da Kwara sun zama sababbin cibiyoyin ayyukan ta’addanci da masu garkuwa da mutane.
4. Fashi da makami da satar mutane a Kudu
Jihohin Edo, Delta da Ondo na fuskantar tashe tashen hankaluna daga sababbin kungiyoyin masu garkuwa da 'yan fashi da makami.
5. Kalubale a ita kanta ma’aikatar tsaro
Janar Galadanchi ya yi gargadi cewa babban ƙalubalen da Janar Musa zai fuskanta ba wai yaƙi da ‘yan ta’adda bane kaɗai, har ma da “canza tsohon tsarin” ma’aikatar tsaro:
“Ma’aikatar tsaro ta dade tana tafiya karkashin wani tsari da mutane suka saba. Sabon ministan zai fuskanci kalubale wajen kawo sababbin tsare-tsare a ma'aikarar.”
- Birgediya Janar Mohammed Galadanchi (mai ritaya).
Ya bada shawara da a kawo sababbin ma’aikata, tare da kafa kwamitin tsofaffin hafsoshin soji domin ba da shawarwari kan dabarun tattara bayanan sirri da dabarun yaƙi.
Ministan tsaro Badaru ya yi murabus
A wani labari, mun ruwaito cewa, Ministan tsaro na Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus daga muƙaminsa na mukarrabin gwamnatin tarayya.
Badaru wanda ya fito daga jihar Jigawa shi ne babban ministan tsaro a Najeriya da dare kujerar bayan hawan Bola Tinubu kan karagar mulki.
Murabus ɗinsa ya biyo bayan ayyana dokar ta-baci kan tsaro da Shugaba Tinubu ya yi, inda ya bayyana cewa za a ƙara fayyace manufar wannan mataki a nan gaba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


