'Yan Bindiga Sun Sace Wasu Daliban Jami'a bayan kai Farmaki cikin Dare
- Wasu ‘yan bindiga sun afka wa wani gida a Emohua suka sace dalibai biyar na Jami’ar Rivers, lamarin da ya tayar da hankula a jihar
- Hakan na faruwa ne kwanaki bayan dalibai sun koka kan hare-haren kungiyoyin daba tare da neman a mayar da su wani waje na daban
- Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana cewa tana farautar ‘yan bindigar domin ceto wadanda aka sace
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - Wasu ‘yan bindiga da ake zargin mambobin kungiyoyin daba ne sun yi awon gaba da dalibai biyar na Jami’ar RSU da ke Emohua a Rivers.
Lamarin ya faru ne a safiyar ranar Talata, lokacin da maharan suka kutsa wani gidan haya da dalibai ke zaune a kusa da makarantar.

Source: Original
Vanguard ta ce lamarin ya faru ne kwanaki kadan bayan dalibai da ke zaune a kusa da makarantar sun gudanar da zanga-zanga kan yawaitar hare-hare da tsangwama da suke fuskanta daga kungiyoyin daba a yankin Emohua.
Sai dai a wani taron manema labarai kafin bikin yaye dalibai, shugaban Jami’ar RSU, Farfesa Isaac Zeb-Obipi, ya ce ba za a rufe makarantar ba ko a kwashe dalibai.
Yadda aka sace daliban jami'ar Rivers
Wani dalibi da ya sha da kyar, wanda ya bukaci a boye sunansa, ya ce maharan sun afka gidan su ne misalin ƙarfe 2:00 na dare, sannan suka fara harbe kare mai gadin gidan kafin su shiga ɗaki-ɗaki suna fitar da dalibai.
Punch ta wallafa cewa dalibin ya bayyana cewa:
“Ya ruga yana bi na da gudu yana harbi a baya na. Ban san sau nawa ya harba ba, amma na ci gaba da gudu saboda kawai tsira nake nema. Wasu dalibai kusan huɗu ko fiye ba a gansu ba yanzu.”

Kara karanta wannan
Gwamnan Kebbi ya yi magana kan batun biyan 'yan bindiga kudin fansa kafin sako dalibai
Lamarin ya biyo bayan wani hari da ake zargin ‘yan fashi ne suka kai a Rumuji a makon da ya gabata, duk da tabbacin shugaban jami’ar ya bayar cewa ana kara matakan tsaro.
Martanin ‘yan sandan Rivers kan sace daliban
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Rivers, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da sace daliban, tana mai bayyana maharan a matsayin kungiyoyin daba.
Ta ce:
“Wasu ‘yan daba ne suka yi hakan. A safiyar Talata, suka kai hari a yankin Rumuchi/Rumuohia, inda suka yi harbi sannan suka yi awon gaba da mutane biyar zuwa wani wuri da ba a sani ba.”
Ta ƙara da cewa rundunar ‘yan sanda ta tura tawagar musamman don ceto daliban cikin koshin lafiya. A cewarta:
“Mun fara farautar su tun da wuri. Kwamishinan ‘yan sanda ya isa wurin da kansa tare da jami’ai na musamman domin tabbatar da cewa an kubutar da daliban.”

Source: Instagram
Gwamnoni sun hada kai kan rashin tsaro
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnonin Arewa sun hada kai wajen yaki da ta'addanci da ya zama babbar barazana a yankunansu.

Kara karanta wannan
An kashe mutum 2 da ƴan bindiga suka je sace dalibai a Kogi? Gwamnati ta yi martani
Shugaban gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana cewa za su yi aiki tare domin shawo kan matsalar.
Muhammadu Inuwa Yahaya ya tabbatar da cewa sun amince da kafa 'yan sandan jihohi tare da yarda da kafa asusu na musamman domin tara kudin tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
