Majalisar Amurka Ta Sake Tabo Batun Shari'ar Musulunci da Hukumar Hisbah
- Majalisar Dokoki ta Amurka ta sake taso Najeriya a gaba kan shari'ar Musulunci a wasu jihohi a Arewacin kasar
- Ta nemi a matsa wa gwamnati lamba ta soke dokar Shari’a, a kawar da Hisbah, suna zargin suna kara barazanar addini
- Wani ya yi zargin cewa Boko Haram, ISWAP da wasu ’yan bindiga suna amfani da haka wurin tsanantawa Kiristoci
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, Amurka - ’Yan majalisar dokoki ta Amurka sun bukaci gwamnati ta matsa wa Najeriya lamba domin soke dokar Shari’ar Musulunci a Arewacin kasar.
Majalisar ta kuma nuna damuwa game da jami'an tsaro na Musulunci musamman hukumomin Hisbah baki ɗaya kan cin zarafin Kiristoci.

Source: Twitter
Zargin da ake yi kan shari'a, ayyukan Hisbah
Wasu sun yi zargin cewa dokokin Shari’a da ayyukan Hisbah suna taimaka wa kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi wajen gallaza wa Kiristoci da kuma kara rashin tsaro a Arewa, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan
Aski ya zo gaban goshi: Majalisar Amurka ta fara zama da bincike kan 'kisan Kiristoci'
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan bukatar ta fito ne a wani zaman hadin gwiwar Majalisar Wakilai, bayan matakin Trump na sanya Najeriya cikin kasashen da suke da babbar matsala.
Dr. Ebenezer Obadare daga 'Council on Foreign Relations' ya shaida cewa Boko Haram, ISWAP da ’yan bindiga suna amfani da Shari’a wajen tilasta akidarsu.
Ya ce wadannan kungiyoyi suna samun kariya saboda Hisbah da tsarin Shari’a, suna tilasta sauya addini da kuma kai hare-hare ba tare da hukunci ba.
'Dalilin Amurka na taimakawa Najeriya'
Obadare ya ce manufar Amurka ita ce taimaka wa sojojin Najeriya su murkushe Boko Haram sannan a matsa wa Tinubu wajen kawar da dokar Shari’a.
Ya bayyana cewa gwamnati ta fara daukar mataki saboda matsin lambar Amurka, ciki har da hare-haren sama da karin jami’an tsaro a kasar.
Sai dai ya ce har yanzu bai isa ba, ya yi kira ga Amurka ta ci gaba da matsawa Nigeria har sai an samu sahihin sauyi.

Kara karanta wannan
Tsohon hafsan tsaro, Janar Irabor ya fadi 'yan siyasa masu rura wutar matsalar tsaro

Source: Getty Images
Musabbabin neman rusa shari'a a Arewa
Wata sanarwa ta ce an fara shirya rahoto zuwa ga Shugaba Trump da shawarwari kan yiwuwar sanya sharadi ga tallafin Amurka ga Najeriya, cewar TheCable.
Majalisar ta ce dole a rusa Shari’a da kuma rundunar Hisbah don dakatar da hare-haren da ake kai wa wasu Kiristoci.
Trump ya mayar da Najeriya cikin jerin CPC a Oktobar 2025, inda ya yi barazanar dakatar da taimako ko yin amfani da karfi idan ba a dauki mataki ba.
A baya, Majalisar ta gudanar da wani zaman jin ra’ayi kan sabunta kasanshen CPC, inda jami’an gwamnatin Amurka da shugabannin addini daga Najeriya suka gabatar da shaida.
Shawarar Amurka na iya shafar Matawalle
An ji cewa an ce Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle zai iya bin sahun tsohon minista, Mohammad Badaru Abubakar.
An ce akwai yiwuwar cewa Shugaba Bola Tinubu zai sake korar wasu manyan jami’an tsaro bisa bin dabarun tsaro da Amurka.
Majiyoyi daga Fadar Shugaban Ƙasa sun ce Amurka ta nemi a sake tsarin tsaro gaba ɗaya domin kawo karshen masu tayar da ƙayar baya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
