Shugaban Gwamnonin Arewa Ya Ce Sun Ga Uwar Bari game da Rashin Tsaro
- Shugaban gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya, ya ce haɗin kai ya zama dole saboda yadda matsalolin tsaro ke ƙaruwa a jihohin yankin
- Ya bayyana cewa talauci, rigingimun zamantakewa da rashin doka na daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da tabarbarewar tsaro
- Gwamnan ya yi magana kan kafa tsarin haɗin guiwar kuɗi da kuma samar da ’yan sandan jihohi domin ƙara ƙarfi ga yaƙi da ta’addanci
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kaduna – Shugaban gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa lokaci ya yi da gwamnonin yankin za su dage wajen haɗa kai domin magance matsalar tsaro da ta addabi su.
Gwamnan ya yi wannan jawabi ne bayan taron hadin guiwa tsakanin gwamnonin Arewa da sarakunan gargajiya da aka gudanar a Kaduna.

Source: Facebook
A wata tattaunawa da RFI Hausa, Inuwa Yahaya ya ce lamarin tsaro ya tsananta fiye da da, lamarin da ya sa wajibi ne a yi aiki tare da tabbatar da cewa duk wani mai aikata laifi ba shi da mafakar gudu daga wata jiha daga wata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsaro: Gwamnonin Arewa sun ga uwar bari
Gwamna Inuwa ya yi karin haske cewa jihohi irin su Kano, Kogi, Jigawa da Niger waɗanda ba su da tarihi da sace-sacen ɗalibai ko hare-haren ’yan bindiga, yanzu matsalolin sun fara ƙaruwa a cikinsu.
Ya ce hakan na nuna cewa lokaci ya yi da gwamnonin yankin za su manta da bambance-bambancen siyasa su mayar da hankali kan kare jama’a.
Gwamnan ya yi nuni da cewa haɗin kai ba “gwara kai” ba ne, domin manufarsa ita ce ɗaukar matakin da ya shafi Arewa gaba ɗaya.
A cewarsa:
“Haɗin kai ya wajaba a kanmu, ai mun ga uwar bari. Kowa yanzu yana ji a jikinsa.”
Abubuwan da ke jawo matsalar tsaro a Arewa
Inuwa Yahaya ya nuna cewa talauci, rashin ayyukan yi da rikice-rikicen zamantakewa su ne manyan abubuwan da ke hura wutar rashin tsaro.
Ya ce duk lokacin da masu aikata laifi suka aikata ta'asa a jiha guda, sukan tsere zuwa wata, saboda ba a bin su har inda suka tsere.
Ya bayyana cewa idan gwamnoni suka yi aiki tare, to duk wanda ya aikata laifi zai iya kamuwa a kowace jiha ya shiga, saboda tsarin doka zai zama iri ɗaya.
Bukatar kafa gidauniyar kuɗi da ’yan sandan jihohi
Gwamnan ya bayyana cewa babu wani gwamna ko shugaban ƙasa da zai yi farin ciki da matsalolin tsaro da mutanensa ke fuskanta.
Yahaya ya bayyana wani tsari da suke shirin aiwatarwa, inda kowace jiha za ta bayar da gudummawar kuɗi domin kafa gidauniyar haɗin gwiwa don yaƙi da ta’addanci.

Source: UGC
A bayanan da gwamnan ya yi, ya bayyana cewa wannan tsari ya fara ne tun kafin a kai ga kafa dokar samar da ’yan sandan jihohi.
Ya yi korafi cewa duk da gwamna ne shugaban tsaro a jiharsa, ba shi da ikon bayar da umurnin tsaro kai tsaye, wanda hakan na hana aiwatar da matakan gaggawa.
A cewar Inuwa Yahaya, saboda haka gwamnoni suka dage kan kafa ’yan sandan jihohi domin ƙarfafa tsaro a cikin jihohinsu.
Abba ya je inda aka kai hari a Kano
A wani labarin, kun ji cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya kai ziyara kananan hukumomin jihar Kano da 'yan bindiga suka kai wa farmaki.
Yayin ziyayar, gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa a shirye ta ke ta cigaba da ba jami'an tsaro dukkan gudumawar da ake bukata.
Wani babban jami'in soja da ya yi magana a madadin jami'an tsaro ya bayyana cewa suna daukar matakan da suka rage hare-hare a yankunan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

