Majalisar Wakilai za Ta Fitar da Matsaya game da Kirkirar Sababbin Jihohi a Najeriya

Majalisar Wakilai za Ta Fitar da Matsaya game da Kirkirar Sababbin Jihohi a Najeriya

  • Majalisar Tarayyar Najeriya za ta kada kuri’a kan kafa ’yan sandan jihohi da ba wa kananan hukumomi ‘yancin kai
  • Ana duba batun kujerun mata na musamman da kirkirar sababbin jihohi a kokarin yi wa kundin tsarin mulki garambawul
  • Akwai kudurin ’yan takara marasa jam’iyya ta yadda mutum zai tsaya ba a karkashin kowa ba wajen samun kujera

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Majalisar Wakilai ta sanar da cewa za ta kada kuri’a kan muhimman kudurorin sauya Kundin Tsarin Mulki a ranakun 10 da 11 ga watan Disamba, 2025.

A cikin kudurorin akwai kafa ’yan sandan jihohi, ware kujerun mata na musamman a majalisu, kirkirar sababbin jihohi da ’yancin kai ga kananan hukumomi.

Majalisar wakilai na aiki a kan kirkirar sababbin jihohi
Wasu daga cikin yan majalisar wakilan Najeriya Hoto: House of representatives
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Mataimakin Shugaban Majalisa, Benjamin Okezie Kalu, ya bayyana jadawalin yayin zaman majalisar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Majalisa ta sa lokacin kada kuri'a kan yi wa kundin tsarin mulkin garambawul

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana duba kundin tsarin mulki a majalisa

Trust radio ta wallafa cewa Ben Kalu wanda shi ne shugaban kwamitin sake duba kundin tsarin mulki ya bukaci 'yan majalisa su kasance a zaman da za a yi na sake waiwayar kundin kafin fitar da matsaya a nan gaba.

Ya ce kwamitinsu ya kammala aikin da ya dace a wannan matakin, kuma ana kammala takardun da aka haɗa don gabatarwa a yayin zaman.

A farko an gabatar da kudurori 87, wadanda suka shafi zaben kasa, shari’o’i, tsaro da harkar kudi. Amma bayan sauraron jama’a a jihohi, taron kasa a Abuja, da tattaunawa da kwararru, an rage kudurorin zuwa 45.

Majalisa na duba yiwuwar kebe wa mata kujeru na musamman
Wasu daga cikin 'yan majalisa a yayin zamansu Hoto: House of Representatives
Source: Facebook

A ranar 24 ga Nuwamba, Majalisar Dattawa da ta Wakilai sun yi taro da shugabannin majalisun jihohi a Abuja a matsayin matakin karshe na gyaran kundin mulki.

Kalu da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa da Barau Jibrin, yanzu kuma an mika batun ga majalisun jihohi domin sun kammala aikinsu.

Kara karanta wannan

Gwamnonin Arewa sun kafa asusun tsaro, za a rika zubin N1bn a wata

Majalisa na duba yiwuwar kafa 'yan sandan jihohi

Majalisar na duba a kan batun kafa ‘yan sanda na jihohi, kujerun mata na musamman a majalisu, da ƙarfafa rawar sarakuna a harkokin tsaro.

Akwai kudurin da zai bai wa ’yan kasa damar shiga takara ba tare da jam’iyya ba ta hanyar gyara Sassa 7, 65, 106, 131, 177, 221 da 228.

Ana kuma so a gama dukkannin kararrakin zabe kafin rantsar da wanda ya lashe zabe da sauran batutuwa da suka shafi zabe.

Da zarar an kammala kuri’a, dole jihohi 24 su amince kafin a aika wa shugaban kasa. Duk wanda bai samu goyon baya ba daga cikin kudurorin ba, za a ajiye batunsa.

Rigima ta barke a Majalisar dattawa

A baya, kun samu labarin cewa Sanata Danjuma Goje na jihar Gombe ya yi wa Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, raddi mai zafi kan yadda yake tafiyar da harkokin majalisa gaba-gadi.

Sanata Goje, ɗan jam’iyyar APC daga Gombe ta Tsakiya, ya yi zargin cewa Akpabio ya karya dokokin tafiyar da zaman majalisa bayan an yi zargin yana abubuwa ba tare da bin ka'idar aikinsa ba.

Kara karanta wannan

"Mun san su": Sanata Maidoki ya ba gwamnati zabi 2 kan kawo karshen 'yan bindiga

Lamarin ya faru bayan Akpabio ya tashi mataimakinsa, Sanata Barau Jibrin daga jagorancin majalisa, bayan ya zauna, Akpabio ya kira Sanata Opeyemi Bamidele da wasu don su gana a kebe.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng