Allah Sarki: Mata, Miji da ’Ya’yansu Duka Sun Kone yayin Gobara a Katsina
- An shiga alhini a Katsina bayan wata mummunar gobara ta tashi a cikin gida ta lakume iyali gaba daya nan take
- Abin firgicin shi ne wutar ta tashi ne da sassafe inda ta ƙona mutane guda biyar kurmus, ciki har da mai gidan
- Shaidu gani da ido sun ce gobarar ta fara daga falon gidan lokacin da aka dawo da wutar lantarki da ƙarfi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - Wata mummunan gobara ya faru da safiyar Litinin 1 ga watan Disambar 2025 a unguwar Kofar Sauri cikin garin Katsina.
An ce wutar ta kama wani gida ta ƙone mutane guda biyar kurmus tare da lalata dukiyoyi da ake ƙiyasta ya kai miliyoyin Naira.

Source: Original
Yadda wuta ta cinye iyali a Katsina
Daily Trust ta ce mutanen da suka rasu sun haɗa da mai gidan, Muhammad Habibu, mai shekaru 35 da matarsa, Fatima Muhammad, da ‘ya’yansu uku: Khadija, Abubakar da Aliyu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni sun nuna cewa marigayi Muhammad Habibu ma’aikacin wucin gadi ne a hukumar ruwa ta jihar Katsina kafin rasuwarsa.
Kodayake ba a tabbatar da ainihin musabbabin tashin wutar ba tukuna, mazauna yankin na zargin lamarin ya faru ne saboda ƙarfin lantarki lokacin da aka dawo da wuta.
Yadda gobarar ta faru a Katsina
Shaidu sun bayyana cewa gobarar ta fara ne daga falon gidan, ta bazu zuwa sassan gida tun kafin iyalin su fahimci abin da ke faruwa.
Lokacin da suka fahimci lamarin, wutar ta rufe dukkan hanyoyin fita inda suka rasa mafita har mai afkuwa ta afku.
Wani ɗan’uwa ga mamatan, Kasim Aliyu, ya ce a wajen ƙarfe 3:00 na dare ya ji wata murya tana karanta “Innalillahi wa inna ilayhi raji’un”, sai dai bai san abin da ya faru ba sai daga baya.
Ya ce:
“Mutumin ƙanina ne daga mahaifi ɗaya. Wuta ta kama gidan wajen 3:00 na dare. Ban gane abin da ke faruwa ba sai da aka kirani ƙarfe 4:00 aka ce min ƙanina da iyalinsa sun rasu. Allah ya yi musu rahama.”

Source: Facebook
Abin mazauna yankin ke cewa
Mazauna yankin sun ce sun yi ƙoƙari sosai wajen kashe gobarar amma ta gagara, sun koka da cewa jami’an Hukumar Kashe Gobara ta Katsina ba su iso a kan lokaci ba.
Wani makwabcinsu, Magaji Bala, ya koka kan yadda ake samun matsalar wuta da dare, da dawo da wuta da ƙarfi wanda kan haddasa irin wannan ibtila’i, cewar Daily Post.
Da aka tuntubi Shugaban Hukumar Kashe Gobara ta Katsina, Rabe Audi Kurmuyal, ya tabbatar da cewa ma’aikatansa sun kashe wutar, yana musanta ikirarin cewa ba su isa wajen da wuri ba.
Gobara ta kone shaguna 500 a Kano
An ji cewa wata mummunar gobara ta tashi a kasuwar Shuwaki da ke jihar Kano, inda shaguna fiye da 500 suka ƙone.
Hukumar kashe gobara ta jihar ta tabbatar da cewa shaguna 529 ne suka ƙone gaba ɗaya, yayin da aka shawo kan wutar.
Masu shagunan da abin ya shafa sun bayyana irin asarar da suka tafka na miliyoyin Naira.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


