Aski Ya Zo Gaban Goshi: Majalisar Amurka Ta Fara Zama da Bincike kan ‘Kisan Kiristoci’

Aski Ya Zo Gaban Goshi: Majalisar Amurka Ta Fara Zama da Bincike kan ‘Kisan Kiristoci’

  • Majalisar Dokokin kasar Amurka ta ci gaba da bincike kan zargin da ake yi na zargin cin zarafin Kiristoci a Najeriya
  • Majiyoyi sun ce yawancin ‘yan majalisar tarayya sun dage cewa ana kai hare-hare musamman kan Kiristoci a kasar nan
  • Manyan ‘yan majalisar sun zargi gwamnati da gazawa wajen kare al'umma, suna sukar hare-haren Boko Haram, ISWAP da 'yan bindiga

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, Amurka - Majalisar Dokokin Amurka ta ci gaba da zaman bincike kan zargin cewa ana nuna wariya ga Kiristoci a Najeriya.

Wannan zargi ya dauki hankalin gwamnati da kungiyoyin kare hakkin addini a kasar inda aka sha musantawa.

Majalisar Amurka tana zama kan zargin kisan Kiristoci
Shugaba Bola Tinubu da Donald Trump na Amurka. Hoto: Donald J Trump, Bayo Onanuga.
Source: Getty Images

Amurka ta fara bincike kan zargin kisan kiristoci

Tashar Arise News ta ce wannan binciken ya samo asali ne daga umarnin Donald Trump wanda ya bukaci a tattara sahihan bayanai kan “kisan Kiristoci” da ake yi a Najeriya.

Kara karanta wannan

Majalisar Amurka ta sake tabo batun shari'ar Musulunci da hukumar Hisbah

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin zaman, manyan ’yan majalisa irin su Mario Díaz-Balart, Robert Aderholt da Riley Moore sun bayyana cewa bai dace wani ya ji tsoro saboda addinin da yake bi ba.

Sun jaddada cewa Amurka na da nauyin kare ’yancin addini a duniya yayin da ake nuna cewa Kiristoci na cikin hatsari musamman a yankin Arewa da tsakiyar Najeriya.

Matsayar wasu 'yan majalisar Amurka

Wasu ‘yan majalisa sun kara bayyana cewa hare-haren da ake kira rikicin manoma da makiyaya ba haka suka ke ba, cewar rahoton Vanguard.

Sun ce akwai wani babban shiri da kungiyoyi irin su Boko Haram, ISWAP da wasu yan ta'adda ke yi domin korar Kiristoci daga yankunan su.

A nasa bangaren, Chris Smith ya ce zama Kirista ko Musulmi mai saukin ra'ayi a Najeriya ya zama kamar zama cikin hadari ne, saboda kungiyoyin yan ta’adda na kai hare-hare ba tare da tsoro ba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bukaci N150m kudin fansar babban Sarki da suka sace

Ya ce gwamnatin Najeriya tana da kundin tsarin mulki da ke tilasta ta kare rayuka, amma hakan ba ya faruwa yadda ya kamata.

Amurka ta taso Najeriya a gaba kan zargin kisan Kiristoci
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Hare-haren 'yan bindiga na damun Amurka

Haka kuma, shugabar USCIRF, Vicky Hartzler, ta kawo misalai na hare-hare da kashe-kashe da suka faru kwanan nan, ciki har da sace dalibai 303 a St. Mary’s a Jihar Niger da kuma harin da aka kai coci a Kwara.

Ta ce Musulmai ma ba a bar su ba, domin su ma suna fuskantar kisa da garkuwa da mutane a wasu yankuna.

Shaidu daga kungiyoyin kare ‘yancin addini sun kuma gabatar da rahotanni masu ban tausayi, ciki har da yadda aka kai wa kauyuka hari, aka kona gidaje da coci-coci, aka kashe fastoci, aka bar mata da marayu.

Amurka: Tinubu ya ware tawaga kan tsaro

Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da kafa tawagar Najeriya da za ta shiga kwamitin hadin guiwar tsaro tsakanin kasar da Amurka.

Tawagar za ta aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma a ziyarar da manyan jami’an tsaro na Najeriya suka kai Washington DC.

Kara karanta wannan

'Manyan mutane 5 ke daukar nauyin 'yan ta'adda a Najeriya,' Malami ya fasa kwai

Sabon tsarin ya samo asali ne bayan barazanar Donald Trump na aika sojojin Amurka zuwa Najeriya saboda zargin kisan Kiristoci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.