Gwamna Abba Kabir Ya Ziyarci Wuraren da aka Yi Artabu da 'Yan Bindiga a Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci sansanonin JTF a wasu yankuna a jihar Kano domin ƙarfafar rundunar wajen yaƙi da ’yan bindiga
- Abba Kabir Yusuf ya tabbatar wa dakarun da cikakken tallafin gwamnati, musamman a bangaren kayan aiki da inganta dabarun yaki
- Hokomomin tsaro sun ce matakan da ake ɗauka na haɗin gwiwa sun rage yawan hare-haren ’yan bindiga a yankunan Shanono da Tsanyawa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano – Gwamnatin Jihar Kano ta ƙara tsaurara matakan tsaro tare da rundunar JTF a ƙauyukan Shanono da Tsanyawa, domin murƙushe ayyukan ’yan bindiga da ke barazana ga zaman lafiyar al’umma.
Wannan na zuwa ne yayin da gwamnati ta bayyana cewa sababbin matakan haɗin guiwa da inganta sintiri sun fara haifar da raguwar kai hare-hare.

Source: Facebook
A cikin sanarwar da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a Facebook, gwamnatin jihar ta bayyana cewa ana ƙara inganta dabarun gano barazanar tsaro tun kafin tasowar ta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jawabin Abba Kabir ga jami'an tsaro a Kano
Yayin ziyarar, Abba Kabir Yusuf ya tabbatar wa dakarun cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ba su dukkan kayan aikin da suka dace, gami da ingantaccen sufuri, kayan aiki na zamani da duk wani abu da zai taimaka wajen ƙarfafa JTF.
Gwamnan ya ce:
"Gwamnatinmu za ta ci gaba da mara muku baya a kowane mataki, kuma ba za mu huta ba har sai an dawo da zaman lafiya a wannan yanki gaba ɗaya."
Ya ƙara da cewa za a inganta hanyoyin shiga ƙauyuka domin sauƙaƙa zirga-zirgar jami’an tsaro, tare da shirin ƙarfafa al’umma ta hanyar shirye-shiryen tsaro.
An samu raguwar hare-hare a Kano
Hukumomin tsaro sun tabbatar da cewa haɗa kai tsakanin gwamnati, JTF da al’umma ya riga ya haifar da sauyi, musamman wajen rage yawan yunƙurin kai hari daga ’yan bindiga da ke neman kutsawa daga ɓangaren iyakar Kano da Katsina.
Sun bayyana cewa inganta dabarun sintiri da ƙarin jami’ai sun bai wa JTF ƙarfi wajen mayar da martani cikin gaggawa da kuma hana hare-hare tun kafin su auku.

Source: Facebook
Kiran gwamnatin Kano ga al’umma
Gwamnan ya yi kira ga mazauna yankunan da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro bayanai masu amfani, tare da kasancewa masu sa ido wajen kare yankunansu.
Rahoton VON ya nuna cewa ya ce:
"Muna kira ga al’umma su kasance masu haɗa kai da hukumomin tsaro. Duk bayanan da kuka bayar na taimaka wa wajen ceton rayuka."
A madadin shugabannin hukumomin tsaro, Birgediya Janar A.M. Tukur, ya yaba wa gwamnan bisa tallafin kayan aiki da goyon baya da ya ba dakarun JTF.
Abba ya yi magana kan tsaro a Kano
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Kano ya gana da kwamitin tsaro yayin da ake cigaba da fuskantar barazanar 'yan bindiga a wasu yankunan jihar.
Abba Kabir Yusuf ya ba da tabbacin cewa jami'an tsaro suna saka ido a kan dukkan wuraren da ake fama da rashin tsaro a fadin jihar Kano.
Baya ga haka, gwamnan ya bukaci jama'a da su guji yada jita-jita game da labaran da ake wallafawa a kafafen sada zumunta domin kaucewa firgita jama'a.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


