Bayan Nada Sabon Minista, Tinubu Ya Shiga Taron Gaggawa da Manyan Hafsoshin Tsaro
- Shugaba Bola Tinubu ya shiga taron gaggawa da hafsoshin soji da hukumomin leken asiri a fadar shugaban kasa da ke Abuja
- Taron ya zo ne bayan murabus din Badaru Abubakar da kuma nadin Christopher G. Musa, domin ya zama sabon ministan tsaro
- Bayan taron, babban hafsan tsaro na kasa, Janar Olufemi Oluyede ya bayyana abubuwan da suka tattauna da Tinubu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya shiga muhimmin taron tsaro da manyan hafsoshin soji da jami’an tsaro a fadar shugaban kasa, Abuja, a yammacin Talata.
Hafsoshin sun isa fadar shugaban kasar ne da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, inda aka sanya labule ba tare da an bar ’yan jarida sun halarta ba.

Source: Twitter
Taron na ranar Talata na zuwa ne awanni kadan bayan Tinubu ya mika sunan tsohon shugaban rundunar soji, Janar Christopher Musa (ritaya), don ya zama sabon ministan tsaro, in ji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu ya gana da manyan hafsoshin tsaro
Shugaban hafsoshin tsaro, Janar Olufemi Oluyede, ya jagoranci sauran hafsoshin tsaro zuwa taron da aka gudanar a Aso Rock.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai shugaban rundunar sojin kasa, Laftanar Janar W. Shaibu, shugaban rundunar sojin sama, AVM Sunday Aneke, da shugaban sojin ruwa, Vice Admiral I. Abbas.
Har ila yau, shugaban hukumar leken asiri ta kasa (DIA), Laftanan Janar Akomaye Undiandeye, Darakta Janar na DSS, Oluwatosin Ajayi, da IGP Kayode Egbetokun sun je taron.
Taron ya kunshi bayanan sirri da tsare-tsaren tsaro masu muhimmanci, sannan ana tunanin ya shafi batun murabus din Abubakar Badaru da kuma nadin Christopher Musa.
Tinubu ya bada sababbin umarni kan tsaro
Bayan taron, CDS Janar Oluyede ya ce tattaunawar ta kasance mai zurfi inda shugaban kasar ya bada sababbin dabaru da tsauraran umarni wajen kawar da barazanar tsaro.
Ya ce an samu sabon daidaiton aiki tsakanin rundunar soji, ’yan sanda, da DSS domin tabbatar da cewa ’yan Najeriya za su yi bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara cikin kwanciyar hankali.
A makon da ya gabata, Tinubu ya ayyana dokar ta baci kan tsaro bayan yawaitar sace-sacen dalibai da hare-haren 'yan bindiga, in ji rahoton Channels TV.
Ya kuma sanar da daukar karin ’yan sanda 20,000, kafa runduna mai kula da dazuka, da kara tsaro a makarantu, coci-coci, masallatai da yankunan da suke da rauni.

Source: Twitter
An hango Alex Otti a fadar shugaban kasa
Wakilin jaridar Punch ya rahoto cewa ya hango Gwamnan Abia, Alex Otti, lokacin da yake shiga ofishin shugaban kasa kafin ko bayan taron tsaro.
Gwamnan ya isa dauke da jakar takardu sannan ba a tabbatar ko shi ma ya shiga taron ba. Otti ya yi kaurin suna kwanakin nan bayan ziyarar da ya kai wa Nnamdi Kanu a gidan yarin Sokoto.
Yayin da ba a tabbatar da dalilin ziyararsa ga Tinubu ba tukuna, masana siyasa sun ce akwai yiwuwar tana da alaka da tattaunawar neman sassauci kan shugaban IPOB, Nnamdi Kanu.
Ministan tsaro, Badaru ya yi murabus
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ya rubuta wasika ga Bola Tinubu inda ya ajiye mukaminsa.
Tsohon gwamnan Jigawan ya yi murabus ne daga FEC a ranar Litinin kuma Shugaba Tinubu ya amince da hakan ba tare da bata lokaci ba.
Murabus ɗin Badaru ya biyo bayan ayyana dokar ta-baci kan tsaro da Tinubu ya yi, inda ya bayyana cewa za a ƙara fayyace manufar wannan mataki a nan gaba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


