'Yan Sanda Sun Gwabza Kazamin Fada da Ƴan Bindiga a Abuja, An Samu Asarar Rayuwa
- Rundunar ’yan sanda ta ce ta kashe wasu ’yan bindiga uku bayan musayar wuta ta fiye da mintuna talatin a Abuja
- An rahoto cewa wani babban dan bindiga mai suna Sani Boko da aka kama ne ya fallasa mugun shirin 'yan bindigar
- An kwato bindigogin AK-47 uku da harsasai, yayin da jami'an 'yan sanda da sojoji ke ci gaba da farautar wadanda suka arce
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya ta tabbatar da kashe mutane uku da ake zargi ’yan bindiga ne a musayar wuta bayan wani yunkurin kai hari a Abuja.
Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh, ta bayyana haka a wata sanarwa da ta rabawa manema labarai a ranar Litinin.

Source: Twitter
An cafke rikakken dan bindiga a Abuja
SP Josephine ta ce rundunar ta samu bayanan sirri cewa wasu miyagu na shirin kai harin garkuwa da mutane da yawa a ranar Litinin, 1 ga Disamba 2025, in ji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwar, jami’an 'yan sanda sun bi sahun masu garkuwar kuma suka kama wani babban dan bindiga da ake nema ruwa a jallo, Sani Mohammed Umar, wanda aka fi sani da “Boko” a ranar 30 ga Nuwamba 2025 da misalin 2:11 na rana.
Adeh ta ce bincike ya tabbatar da cewa wayar da aka samu a hannunsa ita ce ke taimaka musu wajen tsara harkokinsu.
Sani Umar ya amsa cewa shi da tawagarsa suna da hannu a hare-haren ACO, Dupa, Gwagwalada, da kuma fashi da makami a Gwagwalada, Kuje da Kwali.
'Yan sanda sun fafata da 'yan bindiga
Bayan kama sa Umar ya bayyana cewa sauran ’yan bindigan suna jiran shi a kan tuddai Gada Biyu, Kwali, domin kaddamar da sabon hari.
Sai dai, wannan bayanin sirrin ne ya sa jami’an 'yan sanda suka yi gaggawar zuwa wurin, inda ’yan bindigan suka bude musu wuta kai tsaye.
’Yan sanda sun mayar da martani cikin zafin nama, kuma an samu musayar wuta ta kusan mintuna 30 kafin jami’an su fatattaki 'yan ta'addar.
Sanarwar ASP Josephine ta nuna cewa an kashe uku daga cikin ’yan bindigar, wasu kuma sun tsere da raunukan harbin bindiga.

Source: Twitter
Abuja: 'Yan sanda sun kwato makamai
Bayan an gama musayar wutar, ’yan sanda sun kwato bindigogin AK-47 uku, gidajen harsasai uku, da harsasai 33 masu tsayin 7.62mm.
ASP Josephine Adeh ta ce yanzu haka 'yan sanda na sojoji na gudanar da bincike tare da bin sawun wadanda suka arce don kamo su.
Ta jaddada cewa rundunar 'yan sandan Abuja ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen dakile kungiyoyin masu garkuwa da mutane da ke addabar al’umma.
Wasu 'yan bindiga sun kai hari a Abuja
A wani labari, mun ruwaito cewa, ‘yan bindiga sun kai sabon hari Gidan-Bijimi, da ke Abuj, inda aka yi garkuwa da mata shida da namiji ɗaya.
Mazauna yankin sun tabbatar da cewa ‘yan bindigar dauke da AK-47 sun shiga gidaje biyu, suka bude wuta kan mai uwa da wabi.
Wannan hari ya faru ne duk da umarnin Ministan Abuja, Nyesom Wike na ƙara tsaro, wanda ya hada da jibge karin soji, DSS da ‘yan sanda.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


