Wata Sabuwa: IPI Ta Sa Kafar Wando Daya da Sufetan Yan Sanda da Gwamnoni 2 a Najeriya

Wata Sabuwa: IPI Ta Sa Kafar Wando Daya da Sufetan Yan Sanda da Gwamnoni 2 a Najeriya

  • Kungiyar 'yan jarida ta IPI ta nuna damuwa kan yadda wasu shugabanni ke take hakkin ayyukan manema labarai a Najeriya
  • IPI ta sanya gwamnoni biyu a shugabnn rundunar yan sandan Najeriya a jerin wadanda ba su mutunta 'yan jarida a kasar nan
  • Ta kuma karrama shugaban DSS na kasa, Adeola Oluwatosin Ajayi saboda yadda yake daukar shawarwari da gyara idan ya yi kuskure

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ƙungiyar 'yan jarida ta kasa da kasa 'International Press Institute' (IPI) reshen Najeriya ta karrama Shugaban Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS), Adeola Oluwatosin Ajayi.

Sai dai kungiyar ta kuma sa kafar wando daya da wasu gwamnoni, wadanda ta sanya a cikin bakin littafinta, saboda ba su mutunta harkokin aikin jarida a jihohinsu.

Sufetan yan sanda.
Sufetan 'Yan Sandan Najeriya, IGP Kayode Hoto: PoliceNG
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa IPI ta kaddamar da kundin ne ta hannun Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, a ranar Talata a taron shekara-shekara karo na 2 da kungiyar ta gudanar a Nigeria.

Kara karanta wannan

PDP ta manta da adawa, ta koma neman taimako wajen Shugaba Tinubu

IGP da gwamnonin da suka fusata IPI

Kungiyar ta saka Sufeto-Janar na ƴan sanda (IGP), Olukayode Egbetokun, tare da gwamnonin jihohi biyu a wannan kundi na wadanda ba su mutunta aikin jarida.

Gwamnonin da suka shiga sahun farko da IPI ta sa kafar wando daya da su, su ne Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Umo Eno; da Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago.

A cewar kungiyar IPI, Sufetan Yan Sandan Najeriya, Egbetokun ya ki sauraron kiran da ƙungiyar ta yi masa da ya dakatar da tsare ’yan jarida barkatai da jami’ansa ke yi a fadin ƙasar.

Zunubin da gwamnoni 2 su ka yi wa IPI

Gwamna Eno kuwa ya hana ma’aikatan Channels TV dauko rahoton abubuwan da ke faruwa a Fadar Gwamnatin Jihar Akwa Ibom.

A bangaren Gwamna Bago kuma, laifinsa shi ne ya ba da umarnin rufe gidan rediyon Badeggi FM, mallakin ’yan kasuwa.

Kara karanta wannan

Tsohon hafsan tsaro, Janar Irabor ya fadi 'yan siyasa masu rura wutar matsalar tsaro

Duk da roƙon IPI Nigeria da ta yi cewa su sake duba wadannan matakai da ba su da hurumin dauka, gwamnonin biyu sun nace kan matakan da suka dauka.

Gwamna Eno da Bago
Gwmana Umo Eno na Akwa Ibom, Gwamna Umaru Bago na Neja da Sufetan Yan Sandan Najeriya Hoto: Pastor Umo Eno, Mohammed Umaru Bago
Source: Facebook

Kungiyar IPI ta karrama shugaban DSS

A gefe guda, an karrama shugaban DSS saboda kasancewarsa shugaba mai sauraron shawarwari, wanda ya kan karɓi korafe-korafe daga IPI kuma ya yi gyare-gyare lokacin da aka nuna masa kuskure, in ji Tribune Nigeria.

Daya daga cikin muhimman nasarorinsa shi ne cire sunan Lanre Arogundade, daraktan cibiyar yan jarida ta kasa da kasa, daga jerin sunayen da ake sa ido a kansu bayan kusan shekaru 40.

Gwamna Bago ya soki masu taimakon yan bindiga

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Neja, Muhammad Umaru Bago, ya ce 'infomomi' na taka muhimmiyar rawa wajen bai wa ’yan ta’adda damar kai hare-hare.

Gwamna Bago ya fadi haka ne lokacin da ya jagoranci tawagar gwamnatinsa zuwa ziyarar jaje ga Sarkin Borgu bisa sace daliban da aka yi a makarantar Katolika a Papiri.

Ya kuma nuna damuwarsa kan yadda ’yan bindiga suka mamaye gandun dajin Borgu, inda ya roki gwamnati ta tarayya da ta jiha su tserar da yankin daga hannun miyagu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262