An Gano ‘Dalilin’ Murabus din Badaru, Matawalle ma Zai Iya Rasa Kujerarsa

An Gano ‘Dalilin’ Murabus din Badaru, Matawalle ma Zai Iya Rasa Kujerarsa

  • Wasu majiyoyi sun ce Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle zai iya bin sahun tsohon minista, Mohammad Badaru Abubakar
  • An ce akwai yiwuwar cewa Shugaba Bola Tinubu zai sake korar wasu manyan jami’an tsaro bisa bin dabarun tsaro da Amurka
  • Majiyoyi daga Fadar Shugaban Ƙasa sun ce Amurka ta nemi a sake tsarin tsaro gaba ɗaya domin kawo karshen masu tayar da ƙayar baya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Akwai rahotannin da ke nuna cewa aiwatar da tsarin tsaron da Shugaban Amurka Donald Trump ya fara tasiri a gwamnatin Bola Tinubu.

Mai girma Donald Trump kan lamarin tsaro na iya jawo Shugaba Bola Tinubu ya sauke ƙarin manyan jami’ai a harkar tsaro.

Bayan murabus din Matawalle, ana zargin sallamar Matawalle
Tsohon ministan tsaro, Badaru Abubakar da Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle. Hoto: Defence Headquaters Nigeria.
Source: Twitter

Ana tunanin 'dalilin' murabus din Badaru

Majiyar Fadar Shugaban Ƙasa ta shaida wa jaridar BusinessDay cewa murabus ɗin Badaru wani bangare ne na yunkurin da ake yi domin magance matsalar tsaro da ta dabaibaye ƙasar nan.

Kara karanta wannan

'Yan bangan Najeriya sun budewa sojojin kasar Nijar wuta, Hedikwatar tsaro ta yi bayani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta ce “za a ji ƙarin abubuwa nan gaba” bayan ayyana dokar ta-baci a bangaren tsaro.

Wannan na zuwa ne bayan murabus ɗin Abubakar Badaru, Ministan Tsaro, wanda aka ce ya yi ne bisa dalilai na rashin lafiya.

Bayo Onanuga, mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, ya bayyana cewa Badaru ya ce matsalolin lafiya ne suka tilasta masa barin mukamin.

Dalilin Tinubu na dagawa Badaru kafa

Sai dai wasu daga cikin majiyoyi sun ce akwai matsin lamba daga waje, wanda hakan ya sa Tinubu ya canja ra’ayi duk da kusancin da ke tsakaninsa da Badaru tun lokacin neman takarar shugaban ƙasa.

Wata majiya ta tuna cewa Badaru tare da tsofaffin gwamnoni Atiku Bagudu na Kebbi da Nasir El-Rufai na Kaduna su ne suka goyi bayan Tinubu wajen samun tikitin APC a 2023.

Ana zargin Tinubu zai iya kokar Matawalle daga mukaminsa
Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle. Hoto: Dr. Bello Matawalle.
Source: Original

Zargin shirin sauke Matawalle daga kujerarsa

Bincike ya tabbatar da cewa akwai yiwuwar sauke karamin tsaro, Bello Matawalle nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

Ribadu ya fadi manyan kasashen da ke taimakon Najeriya a yaki da ta'addanci

Amurka dai tun bayan tashin hankali a Najeriya ta bukaci Shugaba Tinubu ya sake tsarin tsaron ƙasar gaba ɗaya ko kuma ya fuskanci yiwuwar mamayar sojojin Amurka.

Wannan ya biyo bayan ayyana Najeriya a matsayin “kasashe masu babbar matsala" da Amurka ta yi, cewar Daily Post.

Majiyar ta ce gwamnatin Amurka ta nemi a cire duk wanda ke da wani alaka a tarihi musamman kan cin hanci ko hulɗa da ƙungiyoyin ta’addanci, hakan ya sa ake sake duba komai a fannin tsaro.

A halin yanzu, an tabbatar da cewa Tinubu ya gana a boye da Christopher Musa, tsohon babban hafsan tsaro, kafin murabus ɗin Badaru.

Ana rade-radin cewa Musa zai dawo cikin gwamnati a wani sabon matsayi da ba a bayyana ba tukuna.

Majiyar ta kuma ce Shugaban Ƙasar ya ƙuduri aniyar rage matsalar tsaro kafin zaɓen 2027, domin ya fi mayar da hankali kan farfaɗo da tattalin arzikin da ya durƙushe.

Matawalle ya zaburar da sojoji a Zamfara

An ji cewa karamin ministan tsaron Najeriya, Bello Matawalle, ya ziyarci hedkwatar rundunar Operation Fansan Yamma mai aikin samar da tsaro a yankin Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

An gano wanda zai iya maye gurbin Badaru a matsayin ministan tsaro

Tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya sanar da dakarun sojojin sakon da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ba shi.

Karamin ministan tsaron ya bayyana cewa jarumtar dakarun sojojin rundunar ta sanya tarwatsa sansanoni da dama na manyan jagororin 'yan bindiga.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.