Sojoji Sun Shafe Kwana 3 Suna Barin Wuta a Dazuka, Sun Kama 'Yan Ta'adda 51

Sojoji Sun Shafe Kwana 3 Suna Barin Wuta a Dazuka, Sun Kama 'Yan Ta'adda 51

  • Rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da jerin hare-haren hadin gwiwa daga 29, Nuwamba, 2025 zuwa 1, Disamba, 2025, inda ta dakile gungun ’yan ta’adda a sassa daban-daban
  • An kashe mutane 8 da ake zargi da ta’addanci, an kama 51 yayin da aka ceto wasu 27 a fafutukar da ta shafi Arewa maso Gabas, Arewa ta Tsakiya, Arewa maso Yamma da Kudancin kasar
  • Daga cikin nasarorin da suka samu, sojoji sun kwato bindigogi, harsasai, wayoyin sadarwa, wasu kayan da aka sata, abubuwan fashewa da kuma shanu 76 da aka sace a Plateau

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Rundunar sojin Najeriya ta ce ta samu gagarumar nasara a wani tsari na musamman da ta aiwatar tsakanin 29, Nuwamba, 2025 da 1, Disamba, 2025, wanda ya mayar da hankali kan wargaza sansanonin 'yan ta'adda.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta kwace filayen Ganduje, Patience Jonathan da wasu manya a Najeriya

A jerin farmakin da suka kai, sojojin sun kashe wasu mutane takwas da ake zargi da zama ’yan ta’adda, tare da cafke 51 da ke da alaka da ta’addanci, fashi, fataucin miyagun kwayoyi da sauran laifuka.

Wasu dakarun Najeriya a bakin aiki
Sojojin Najeriya a fagen fafatawa da 'yan ta'adda. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Twitter

A sakon da ta wallafa a X, rundunar sojojin kasa ta ce ta ceto mutane 27 da suka hada da mata, kananan yara da maza da aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban.

Sojoji sun farmaki mayakan ISWAP a Borno

A jihar Borno, sojoji sun kashe ’yan ISWAP/JAS guda hudu a cikin jerin farmaki na kwanton-bauna da wargaza sansanoni daban daban.

An kwato bindigogi AK-47 guda uku, jerin harsasai, sojojin sun kuma fatattaki ’yan ta’adda da suka yi yunkurin kutsawa kusa da Chibok.

Nasarar da sojoji suka samu a wasu jihohi

A jihohin Plateau, Taraba, Benue, Kogi, Kaduna da Delta, sojoji sun ceto mutane 20, ciki har da mata, kananan yara da maza da aka yi garkuwa da su.

A Panyam an kama masu garkuwa da mutane guda biyu, yayin da aka damke masu fataucin mutane hudu a Sardauna da masu taimaka wasu 'yan ta'adda uku a Ukum.

Kara karanta wannan

Tashin hankali a Kano: Mummunar gobara ta cinye shaguna 500 a wata babbar kasuwa

A Taraba, sojoji sun kashe mutane hudu da ake zargi da tsattsauran ra’ayi a karamar hukumar Karim Lamido, tare da kwato bindiga AK-47 kirar gida, wasu bindigogi, harsasai 25 da babura biyu.

Sojojin Najeriya a filin daga
Wasu sojojin Najeriya da jiragen yaki. Hoto: Nigeria Airforce HQ
Source: Facebook

Haka kuma, a cikin samamen hadin gwiwa, an kama masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba guda 13 a Lau, an kama masu hada-hadar miyagun kwayoyi 25 a Bayelsa da Rivers, sannan an cafke wani dan bindiga a Plateau.

An kama masu safarar mai da makamai

Sojoji a Kudancin kasar sun lalata wani wurin tace mai ba bisa ka'ida da ke dauke gurbataccen mai kimanin lita 1,000, tare da kama wadanda ke da hannu a harkar.

Daga cikin manyan nasarorin da suka samu, sojoji sun kama wani shahararren mai safarar makamai Shuaibu Isah wanda aka fi sani da Alhaji, wanda yake kokarin karbar harsasai 1,000 daga abokan harkarsa da ake nema.

An yi sabani tsakanin sojojin Nijar da 'yan banga

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar tsaron Najeriya ta yi magana game da wani sabani da aka samu tsakanin 'yan banga da sojojin Nijar.

Kara karanta wannan

Duniya na kallo: Harin Kebbi da wasu hare hare da suka girgiza Arewa a Nuwamba

An bayyana cewa wasu 'yan banga ne suka budewa motocin sojojin kasar Nijar wuta yayin da suka shiga iyakar Najeriya ta jihar Katsina.

Rundunar tsaro ta ce tun da dadewa sojojin Nijar suna shiga Najeriya diban ruwa, sannan wannan karon an samu rashin fahimta ne kawai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng