Gwamnati za Ta Kwace Kadarorin Ganduje, Patience Jonathan da Wasu Manya a Abuja
- Hukumar gudunarwar birnin tarayya, Abuja ta fitar da sunayen mutane da hukumomi masu gidaje 1,095 da aka soke takardun mallakarsu
- An ji cewa hukumar za ta fara aiwatar da kwace kadarorin bayan karewar wa’adin kwanaki 14 da aka ba wa wadanda abin ya shafa
- Sunayen wadanda da abin ya shafa sun haɗa da tsofaffin gwamnoni, 'yan majalisa, sanatoci, manya irinsu Madam Patience Jonathan
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Hukumar Abuja ta bayyana sunayen mutane da kungiyoyi da suke da alaka da kadarori 1,095 da aka soke takardun mallakarsu saboda gazawar biyan haraji da sauran kudin da doka ta tanada.
Kadarorin da abin ya shafa suna cikin manyan unguwannin Abuja da suka haɗa da Asokoro, Maitama da Garki da Wuse.

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta wallafa cewa a wadannan yankuna ne ake samun gidaje da kadarori masu tsadar gaske.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a kwace filayen wasu manyan kasa a Abuja
Sanarwar ta bayyana cewa za a fara aiwatar da matakan kwace filayen bayan karewar wa’adin kwanaki 14 da aka ba wa masu kadarorin, wanda ya cika a ranar 25 ga Nuwamba, 2025.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa an sanar da wannan mataki ne a cikin sanarwar da hukumar Abuja ta fitar.
Hukumar ta ce daga cikin jerin, kadarori 835 sun gaza biyan harajin da aka dora a kan gidaje ko filayensu, yayin da 260 suka gaza biyan kudin sabawa ka’ida da kuma kudin sauya amfani da ƙasa.
Ganduje da sauran wanda za a kwace filayensu
A jerin sunayen da aka wallafa, akwai shahararrun mutane daga ciki har da manyan ‘yan siyasa da suka taɓa rike muhimman mukamai a Najeriya.
Daga cikin su akwai: Abdullahi Ganduje, tsohon gwamnan Kano; Donald Duke, tsohon gwamnan Cross River da Patience Jonathan, matar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan;

Kara karanta wannan
Nuhu Ribadu ya gana da wakilan CAN da iyayen daliban Neja, an ji abin da suka tattauna
Sauran sun haɗa da David Mark, tsohon shugaban majalisar dattawa da Iyiola Omisore, tsohon mataimakin gwamnan jihar Osun.

Source: Facebook
Hukumar Abuja ta ce duk kadarorin da ke cikin jerin an dade da sanar da su halin da filayen ko gidajensu ke ciki, amma suka yi kunnen ƙashi.
Wannan ya sa gwamnati ta ɗauki matakin soke takardun mallakar, wanda ya ba ta ikon ɗaukar mataki kai tsaye domin dawo da bin doka a birnin tarayya.
Hukumar ta kara jaddada cewa matakin da ta ɗauka ba wai don cin zarafi bane, sai dai domin tabbatar da cewa duk masu mallakar filaye a Abuja suna bin ƙa’idoji, da biyan hakkokin gwamnati.
Ta kuma yi kira ga sauran masu filaye su tabbatar da sabunta bayanansu da biyan kudin da ake binsu, domin guje wa sake samun irin wannan mataki a nan gaba.
Shugaba Tinubu ya takawa Wike burki
A baya, mun wallafa cewa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taka wa Ministan Abuja, Nyesom Wike birki a kan kwace filayen da aka fara aiwatarwa a babban birnin tarayya.
Shugaban kasar ya umarci a ba su wa’adin kwanaki 14 domin su biya bashin harajin filin da ake binsu tare da sabunta takardun kadarorin nasu a maimakon a kwace su kai tsaye.
Wannan sabon umarni na shugaban kasa ya ba wa masu kadarori damar numfasawa, wanda ake ganin zai tabbatar da cewa gwamnati ta yi adalci kafin ci gaba da kwace filayen.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

