PDP Ta Manta da Adawa, Ta Koma Neman Taimako wajen Shugaba Tinubu
- Jam'iyyar PDP ta yi martani kan mafakar da gwamnatin Najeriya ta ba jagoran 'yan adawa a kasar Guinea-Bissau, Fernando Dia Da Costa
- PDP mai hamayya ta bukaci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya dauki irin wannan mataki a Najeriya domin ceto dimokuradiyya
- Sannan jam'iyyar ta nuna cewa idan shugaban kasar bai dauki matakin da ya dace ba, kasar nan na iya komawa karkashin jam'iyya daya
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta mika bukatarta ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
PDP ta nemi Tinubu ya ceto adawa a Najeriya kamar yadda ya bada gudunmawar mafaka da kariya ga ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa a Guinea-Bissau, Mr. Fernando Dia Da Costa.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun PDP na kasa, Kwamared Ini Ememobong, ya fitar a shafin X.

Kara karanta wannan
Sace dalibai a Neja: Ribadu ya bada tabbaci bayan ganawa da shugabannin Kiristoci
PDP ta yi wannan kira ne a matayin martani kan mafakar da aka bai wa jagoran adawar Guinea-Bissau bayan juyin mulkin da ya biyo bayan zaɓen da ya jawo cece-kuce a kasar.
Najeriya ta ba dan adawa mafaka
Ministan harkokin kasashen waje, Ambasada Yusuf Tuggar dai ya bayyana cewa an ba Fernando Dia Da Costa mafaka ne domin kare rayuwarsa, kare muradun dimokuraɗiyyar mutanen Guinea-Bissau.
Hakazalika ya ce mafakar da aka ba jagoran 'yan adawar na nuna jajircewar Najeriya wajen wanzar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da rage rikice-rikice a yankin Yammacin Afirka.
Wace bukata PDP ta nema wajen Tinubu?
Sai dai a cewar mai magana da yawun PDP na kasa, Kwamred Ini Ememobong, ya kamata Tinubu ya dauki irin wannan mataki a gida, domin wanzar da zaman lafiya da dimokuraɗiyya a Najeriya.
“Wannan ya haɗa da dakile ayyukan masu adawa da dimokuraɗiyya da ke cikin majalisar ministocinsa da tafiyar siyasarsa, waɗanda ke fitowa wajen kirkira, ɗaukar nauyi, da hura rikice-rikice a manyan jam’iyyun adawa.”

Kara karanta wannan
Guinea Bissau: Gwamnatin Tinubu ta faɗi halin da Jonathan ke ciki bayan ya maƙale
"Ko da yake ba a tsammanin shugaban kasa zai tallafa wa jam’iyyun adawa, akwai nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora masa na tabbatar da cewa fagen siyasar kasar nan ya kasance kowa na da 'yanci kuma akwai adalci."
“Yanzu haka, fagen yana kara matsewa ta hanyar tilasta wa jami’an da aka zaɓa su koma jam’iyyar gwamnati, da kuma ɗaukar nauyin rikice-rikice a jam’iyyun adawa.”
- Ini Ememobong

Source: Instagram
PDP ta bayyana cewa irin falsafar da ta sa Najeriya ta shiga cikin rikicin Guinea-Bissau ita ce ya kamata ta jagoranci halayen shugaban kasa a gida, domin kare dimokuraɗiyyar Najeriya daga durƙushewa da kuma hana komawa tsarin jam’iyya guda daya.
"Dole ne shugaban kasa ya yi gaggawar kare dimokuraɗiyya a Najeriya. Ba zai yiwu ya riƙa bayyana kansa a matsayin mai kare dimokuraɗiyya a yankin Yammacin Afirka, yayin da a gida kuma ake bari ayyukan da ke ƙalubalantar dimokuraɗiyya su bunkasa ba.”
- Ini Ememobong
PDP ta soki Shugaba Bola Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP ta caccaki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan jakadun da ya nada.
PDP ta bayyana cewa mafi yawan sunayen da ke cikin mutanen da aka nada don zama jakadu, ba su cancanci su wakilci Najeriya ba.

Kara karanta wannan
"Mutane suna da mantuwa," Sheikh Gumi ya yi magana kan zargin goyon bayan 'yan bindiga
Ta bayyana matukar damuwa kan ganin sunan tsohon shugaban hukumar zabe ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, a cikin wadanda za a nada jakadu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng