An Gano Wanda zai Iya Maye Gurbin Badaru a Matsayin Ministan Tsaro

An Gano Wanda zai Iya Maye Gurbin Badaru a Matsayin Ministan Tsaro

  • Tun bayan ɓullar labarin murabus da Ministan tsaro, Badaru Abubakar ya yi, hankali ya koma kan wane ne zai maye gurbinsa
  • Rahotanni sun ce Shugaban kasa, Bola Tinubu ya sa labule da tsohon Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritaya
  • Fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da murabus da Abubakar Badaru ya yi, kuma ana kiran wanda Tinubu zai ayyana ya maye gurbin

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Ministan tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya mika takardar ajiye aikinsa daren jiya, a lokacin da ake fama da ƙarin tsanantar matsalolin tsaro a faɗin ƙasar.

Badaru mai shekaru 63 a duniya ya danganta matakin nasa da dalilan lafiya, kamar yadda Mshawarcin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Ribadu ya fadi manyan kasashen da ke taimakon Najeriya a yaki da ta'addanci

Ana sa ran Janar Christopher Musa mai ritaya ya zama sabon Ministan tsaro
Janar Christopher Musa mai ritaya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Political affairs Int'l
Source: Facebook

This Day ta wallafa cewa murabus na Badaru ya yi ya zo ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a kan tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yanzu haka ana sa ran Shugaban kasa zai ayyana cikakkun matakan da gwamnati ke ɗauka nan gaba.

Ana ganin Janar C.G Musa zai canji Badaru

Daily Nigerian ta wallafa cewa a halin da ake ciki, alamu sun nuna cewa tsohon hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Christopher Musa mai ritayaiya zama sabon Ministan tsaro.

Rahotanni sun ce an ga Janar Christopher Musa mai ritaya na ganawa da Shugaba Bola Tinubu jiya da dare, lamarin da ya ƙara zafafa hasashen da aka yi.

Tinubu ya sauke Janar Christopher Musa mai ritaya aga kujerar hafsan hafsoshin Najeriya a cikin babban sauye-sauyen rundunonin tsaro da Tinubu ya yi a ranar 24 ga Oktoba, 2025.

Ya zama sananne wajen jagorantar sake fasalin soji da kara zamanantar da yaƙi da ta'addanci a lokacin da yake kan kujerarsa.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ya yi murabus

Waye Janar Christopher G. Musa?

Kafin nadin sa a matsayin jagoran rundunonin tsaro a ranar 23 ga Yuni, 2023, Janar Musa ya yi fice a matsayin kwamandan fagen daga na Operation Hadin Kai a Arewa maso Gabas.

Ya kuma dage kan haɗa kai tsakanin soji da farar hula, yana ganin mahimmancin haɗa ayyukan jin kai da ci gaba da tsaro.

Ana sa ran Shugaba Tinubu zai bayyana sabon Ministan tsaro nan gaba
Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

A sabon sauye-sauyen bayanan tsaro da gwamnatin Tinubu ta gudanar a watan Oktoba, Musa ya miƙa ragamar hafsun tsaro ga Janar Olufemi Oluyede.

Ana sa ran cikin ‘yan kwanaki za a bayyana ko cewa ko Kamar Christopher Musa ne zai zama sabon Ministan Tsaro domin cike gurbin da Badaru ya bari.

Tinubu ya gana da Janar Christopher Musa

A wani labarin, kun ji cewa Bola Tinubu ya karɓi bakuncin tsohon babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa(mai ritaya, a fadar shugaban ƙasa a daren ranar Litinin.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Janar Musa ya isa Aso Rock da misalin ƙarfe 7:00 na dare, inda jami’an tsaro suka raka shi kai tsaye zuwa ofishin shugaban ƙasa domin gana wa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da babban hafsan tsaron Najeriya da ya kora daga aiki

Rahotanni sun nuna cewa wannan ganawar ta zo ne a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar tashin hankali a sassa da dama na Arewa, inda ake fama da kisan bayin Allah.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng