Babbar Magana: Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar Ya Yi Murabus

Babbar Magana: Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar Ya Yi Murabus

  • Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ya rubuta wasika ga Bola Tinubu inda ya ajiye mukaminsa a yau Litinin 1 ga watan Disambar 2025
  • Tsohon gwamnan Jigawan ya yi murabus ne daga FEC a yau Litinin kuma Shugaba Tinubu ya amince da hakan ba tare da bata lokaci ba
  • Ana jiran shugaban kasa ya sanar da wanda zai maye gurbin Badaru a majalisar zartarwa ta tarayya kafin karshen mako da muka ciki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan Tsaro na Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus daga muƙaminsa na minista.

Badaru wanda ya fito daga jihar Jigawa shi ne babban ministan tsaro a Najeriya da dare kujerar bayan hawan Bola Tinubu kan karagar mulki.

Ministan tsaron Najeriya, Badaru ya yi murabus
Tsohon gwamnan Jigawa da ya yi murabus daga mukamin minista. Hoto: Defence Headquarters Nigeria.
Source: Facebook

Wannan bayani ya fito ne daga Bayo Onanuga, mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan yada labarai wanda ya wallafa a shafin X a daren yau Litinin 1 ga wata Disambar 2025.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da babban hafsan tsaron Najeriya da ya kora daga aiki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hare-hare da Najeriya ke fuskanta a yanzu

Badaru Abubakar mai shekara 63, ya kasance gwamnan jihar Jigawa daga 2015 zuwa 2023, sannan aka nada shi minista a ranar 21 ga Agusta, 2023.

Murabus ɗinsa ya biyo bayan ayyana dokar ta-baci kan tsaro da Shugaba Tinubu ya yi, inda ya bayyana cewa za a ƙara fayyace manufar wannan mataki a nan gaba.

A ‘yan makonnin nan, Najeriya ta fuskanci tashin hankali iri-iri, musamman kashe-kashe da sace-sace na mutane da dalibai.

Tinubu ya gana da tsohon hafsan tsaro

Tun kafin murabus ɗin Badaru ta bayyana, Shugaba Tinubu ya gana da tsohon hafsan tsaro, Christopher Musa a fadar shugaban kasa da ke birnin Abuja.

Janar C.G Musa mai ritaya na daga cikin wadanda Tinubu ya sallama daga shugabancin rundunar tsaro inda ya maye gurbinsu da wasu.

Sai dai har yanzu ba a tabbatar ko wannan ganawar na da nasaba da kujerar Badaru wanda ya yi murabus ba ko sabanin haka.

Kara karanta wannan

'Ni ne mafi girman Kirista a gwamnati': Akpabio ya fadi yadda ya taso a kaskance

Ministan tsaro ya fadi dalilin ajiye mukaminsa
Tsohon ministan tsaro a Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar. Hoto: Ministry of Defence Nigeria.
Source: Facebook

Murabus: Badaru ya rubutawa Bola Tinubu wasika

A cewar Onanuga, an gano murabus ɗin ne cikin wata takarda da Badaru ya aikawa Shugaba Bola Tinubu a ranar 1 ga Disambar 2025.

Ya ce tsohon gwamnan Jigawa ya bayyana cewa ya ajiye aikin nasa ne bisa dalilan lafiya inda Tinubu ya amince da hakan.

Mai magana da yawun fadar shugaban kasa ya ce Tinubu ya karɓi murabus ɗin tare da jinjinawa Badaru bisa hidimar da ya bayar ga kasar.

Ana sa ran Shugaba Tinubu zai sanar da majalisar dattawa sunan wanda zai gaji Badaru a cikin wannan makon.

Badaru ya sha alwashin kawo karshen ta'addanci

A baya, an ji cewa Ministan tsaron Najeriya, Badaru Abubakar ya jagoranci kaddamar da sababbin jiragen yaƙi samfurin ATAK-129 a jihar Katsina da ke fama da matsalolin tsaro.

Kara karanta wannan

Jonathan ya gana da Tinubu, ya fada masa abin da ya faru da shi a Guinea Bissau

Badaru ya ce jiragen za su taimaka wajen kawo karshen ƴan bindiga da dukkan nau'in miyagun da ke kawo cikas a zaman lafiya tare da tabbatar da kare kare rayuka.

Ya kuma jinjinawa dakarun sojoji bisa sadaukarwar da suke yi domin tabbatar zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya wanda ya ce tabbas ana samun nasara sosai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.