Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Babban Hafsan Tsaron Najeriya da Ya Kora daga Aiki
- Bola Ahmed Tinubu ya karbi bakuncin tsohon babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Chirstopher Musa (mai ritaya) a fadar shugaban kasa
- Musa, wanda Tinubu ya sallama daga aiki a watan da ya gabata, ya isa Aso Rock da karfe 7:00 na dare kuma kai tsaye ya wuce ofishin shugaban kasa
- Har yanzu babu wani bayani kan makasudin wannan ganawa amma dai ta zo a daidai lokacin da matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da tsohon babban hafsan tsaron Najeirya da ya sallama daga aiki kwanakin baya, Janar Christopher Musa (mai ritaya).
Wannan ganawa na zuwa ne a daidai lokacin da al'amuran tsaro ke kara tabarbarewa a Najeriya musamman a jihohin Kwara, Neja da Kebbi sakamakon hare-haren da aka kai a baya-bayan nan.

Source: Facebook
Bola Tinubu ya gana da Janar C.G Musa
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa an ga Janar Musa ya isa fadar shugaban kasa da misalin ƙarfe 7:00 na daren yau Litinin, inda jami’an tsaro suka raka shi zuwa sashen ofishin Shugaban Kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har zuwa lokacin hada rahoton nan, ba a bayyana dalilin ganawa da Bola Tinubu da Chirstopher Musa ba.
Wannan shi ne karo na farko da tsohon hafsun tsaron ɗin ya gana da Shugaba Tinubu a fili tun bayan saukarsa daga mukamin babban hafsan tsaron Najeriya a ranar 24 ga Oktoba, 2025.
Ganawar ta zo ne a daidai lokacin da ake fama da ƙarin tashin hankali a Arewa, ciki har da sace dalibai a jihohin Kebbi da Neja, da kuma harin da aka kai wa masu ibada a Eruku, Jihar Kwara.
Yadda Tinubu ya sauke Janar Christopher Musa
A watan da ya gabata ne Shugaba Tinubu ya yi sauye-sauye a shugabancin rundunonin tsaro, inda ya sauke wasu hafsoshinn tsaro, ciki har da Janar Musa.
Sababbin nade-naden da aka yi Janar Olufemi Oluyede, babban hafsan tsaron kasa (wanda ya maye gurbin Musa), Manjo Janar W. Shaibu, a matsayin babban hafsan sojin kasa.
Sai kuma babban hafsan rundunar sojojin sama, Air Vice Marshal S.K. Aneke da Rear Admiral I. Abbas, wanda ya zama shugaban sojojin ruwa.

Source: Twitter
Sai dai duk da wannan sauye-sauye da shugaban kasa ya yi, matsalolin tsaro a ƙasar sun cigaba da ƙamari, cewar rahoton Daily Trust.
Janar Musa, wanda ya isa fadar shugaban kasa da daddare, ya shiga ofishin shugaban kasa tare da wani babban jami’in tsaro da ya raka shi, sai dai babu wani bayani a hukumance kawo yanzu.
Bola Tinubu ya ayyana dokar ta baci
A wani rahoton, kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan tsaro a fadin Najeriya, matakin da ake ganin zai kawo karshen duk wani nau'in ta'addanci.
Mai girma Tinubu ya bada umarnin a dauki karin jami’an ’yan sanda da sojoji, domin dakile ta’addanci, ’yan bindiga da kuma karuwar sace-sacen dalibai.
Tinubu ya umarci DSS da ta gaggauta tura dakarun tsaron daji da aka riga aka horas, domin zakulo ’yan ta’adda da ’yan bindiga da ke ɓoye.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

