'Yan Bindiga Sun Aiko Sako Mai Tada Hankali, Garuruwa Sama da 10 na cikin Hadari

'Yan Bindiga Sun Aiko Sako Mai Tada Hankali, Garuruwa Sama da 10 na cikin Hadari

  • Mazauna kauyuka fiye da 12 da ke yankin karamar hukumar Yabo a jihar Sakkwato sun shiga tashin hankali da zaman dar-dar
  • Hakan dai ya biyo bayan harajin da wata dabar 'yan bindiga ta kakaba masu, wanda ya fara daga Naira miliyan uku zuwa 20
  • A wani sautin murya da ya fara yaduwa, 'yan bindigan sun nemi mutanen kauyen Makale su biya N20m ko su kawo musu hari

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sakkwato, Nigeria - 'Yan bindiga sun jefa mutane cikin tashin hankali da fargaba bayan turo wani sako a jihar Sakkwato da ke Arewacin Najeriya.

Barazanar 'yan bindigan na zuwa ne a daidai lokacin da matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a Arewa, musamman bayan hare-haren da aka kai jihohin Kebbi, Kwara da Neja.

Jihar Sakkwato.
Taswirar jihar Sakkwato Hoto: Legit.ng
Source: Original

Daily Trust ta ruwaito cewa wata kungiyar 'yan bindiga ta yi wa al'ummar kauyen Bakale da ke yankin Kilgori, karamar hukumar Yabo a Jihar Sakkwato barazanar kashe su.

Kara karanta wannan

Ba dadi: 'Yan bindiga sun sake ta'addanci a wasu kauyukan Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakon da 'yan bindiga suka turo a Sakkwato

'Yan bindiga sun yi barazanar zafafa hare-hare na garkuwa da mutane da kashe-kashe matukar mutanen kauyen Bakale suka gaza biya kudin haraji Naira miliyan 20.

A cikin wani sautin murya da wakilinmu ya samu, shugaban wata dabar ’yan bindiga ya umurci dagacin kauyen da ya tara mutanen yankin domin sanar da su bukatar da suka gabatar.

A sautin, an ji shugaban ’yan bindigan yana tambayar dagacin kan umarnin da ya ba shi a baya:

“Ka gana da su? Sun yarda su bi umarninka?”

'Yan bindiga sun kakaba haraji a kauyuka

Bayan da dagacin ya ba shi amsa, sai shugaban ’yan bindigar ya ba shi sabon umarni cewa, “Ka sake tara su, ka fada musu muna bukatar harajin Naira miliyan 20.”

Ya ci gaba da cewa:

“Ba ma son kai muku hari. Shi ya sa muka saka wannan kudi. Idan kun biya, wallahi za ku zauna lafiya. Ba za mu bar wata kungiya ta kai muku hari ko ta sace mutanenku ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da amarya da sauran 'yan biki a Sokoto

Amma idan ba ku biya ba, za mu kawo hari, mu kashe ku, mu yi garkuwa da mutanenku. Wannan shi ne sakonmu.”

Sunayen kauyukan da ke fuskantar hadari

Wani jagoran al’umma, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya tabbatar da cewa irin wannan haraji na tilas ya zama ruwan dare a wasu garuruwa da ke makwabtaka da Sakkwato.

Rahotanni sun nuna cewa an kakaba irin wadannan haraji a kauyuka da dama da ke cikin yankunan Kilgori da Torankawa.

Kauyukan da 'yan bindigan suka kakaba harajin sun hada da Bazar, Alkalije, Gari, Bakale, Dagel, Adarawa, Kwaidaza, Kilgori Runji, Tudu, Tile, Kibiyare, Barmadu da wasu makamantansu.

Rahoto ya nuna cewa yan bindigar sun sanya harajin tsakanin N3m zuwa N20m, gwargwadon girman kowanne kauye, cewar Daily Post.

Gwamna Ahmed Aliyu.
Gwamnan jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu a fadar gwamnatinsa Hoto: Ahmed Aliyu
Source: Facebook

'Yan bindiga sun kai farmaki a Sakkwato

A wani rahoton, kun ji cewa wasu miyagun ’yan bindiga dauke da mugayen makamai sun kai farmaki kauyen Kurawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sakkwato.

'Yan bindigan sun kashe mutum biyu tare da yin garkuwa da mutane 15, ciki har da wasu mata huɗu masu shayarwa da jariransu.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun bukaci N150m kudin fansar babban Sarki da suka sace

Wasu mutum biyu kuma, ciki har da wani jami’in rundunar tsaro ta jihar Sakkwato sun samu raunuka inda suke karɓar magani a asibiti.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262