Sace Dalibai a Neja: Ribadu Ya Bada Tabbaci bayan Ganawa da Shugabannin Kiristoci

Sace Dalibai a Neja: Ribadu Ya Bada Tabbaci bayan Ganawa da Shugabannin Kiristoci

  • Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya je jihar Neja domin jajantawa kan sace dalibai
  • Malam Nuhu Ribadu ya gana da shugabannin kungiyar Kiristoci da iyayen daliban da 'yan bindiga suka sace yayin ziyarar
  • ​Ya bayyana cewa yaran suna cikin koshin lafiya kuma gwamnatin tarayya ba za ta sake yarda irin hakan ta kara faruwa ba

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Neja - Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ya yi magana kan daliban da 'yan bindiga suka sace a jihar Neja.

Nuhu Ribadu ya bayyana cewa dalibai da ma’aikatan da aka sace daga St. Mary’s Private Catholic Primary and Secondary School, Papiri, a karamar hukumar Agwarra ta jihar Neja, suna cikin koshin lafiya.

Nuhu Ribadu ya ce daliban Neja za su dawo gida
Nuhu Ribadu da shugaban CAN na jihar Neja, Bishop Bulus Yohanna Hoto: Dan Kunda, Nuhu Ribadu
Source: Twitter

Jaridar TheCable ta kawo rahoto cewa Nuhu Ribadu ya bayyana hakan ne yayin ziyarar jajantawa da ya kai ga shugaban cocin Katolika ta Kontagora kuma mai makarantar, Bishop Bulus Yohanna.

Kara karanta wannan

Nuhu Ribadu ya gana da wakilan CAN da iyayen daliban Neja, an ji abin da suka tattauna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daliban Neja sun fada hannun 'yan bindiga

'Yan bindiga sun kai hari a makarantar ne a ranar 21 ga watan Nuwamba 2025, inda suka yi garkuwa da mutane 315 ciki har da dalibai 303 da malamai 12.

Daga baya, kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Neja ta tabbatar da cewa dalibai 50 daga cikin wadanda aka sace sun tsere daga hannun masu garkuwa da mutanen.

Me Ribadu ya ce kan daliban Neja?

Nuhu Ribadu ya ce yaran suna cikin ƙoshin lafiya, kuma za a sako su nan kusa domin haduwa da iyayensu.

“Wannan lokaci ne mai matukar nauyi da radadi gare mu, musamman bayan jin kukan iyaye da tattaunawar da muka yi da ku."
"Amma mun ɗauki alhakin faruwar hakan, domin nauyin kare ku yana kanmu.”

- Malam Nuhu Ribadu

Ya kara da cewa shugaban kasa ya umarce su da su je su gana da shugabannin cocin.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta biya kudin fansa kafin ceto 'daliban Kebbi? Majalisa ta yi bayani

“Shugaban kasa yana cikin damuwa kamar yadda dukkanmu muka shiga damuwa. Ya dakatar da duk wata tafiya da yake shirin yi saboda lamarin nan.”

- Malam Nuhu Ribadu

Ribadu ya sha alwashi kan tsaro

Ribadu ya jaddada cewa gwamnatin tarayya ba za ta kara lamunta da ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane ba.

“Ya isa haka, abin ya isa haka. Ba za mu yi kasa a guiwa ba. Kada mu bari miyagu su raba mu. Kada mu bari mugunta ta shige mu.”

- Malam Nuhu Ribadu

Nuhu Ribadu ya kai ziyara jihar Neja
Nuhu Ribadu da sauran shugabanni yayin ziyara a Neja Hoto: Dan Kunda
Source: Facebook

Ya bayyana cewa kasashen duniya na nuna goyon baya ga Najeriya wajen yaki da ta’addanci da ’yan bindiga.

“Kasashe da dama, ciki har da Amurka, suna goyon bayan Najeriya. Muna godiya ga kasashen Turai kamar Faransa, Birtaniya da sauransu."
"Duniya ta hada kai domin kawo karshen wannan barna da ta addabi Najeriya tsawon shekaru 20.”

- Malam Nuhu Ribadu

Tun da farko, Bishop Yohanna ya gode wa Shugaba Bola Tinubu kan kokarin da ake yi, sannan ya mika rahoto ga NSA kafin su shiga ganawar sirri ta tsawon kusan minti 30.

Kara karanta wannan

Tinubu ya nada shugaban NIA da ya shiga badakalar $43m lokacin Buhari a matsayin Jakada

Ribadu ya gana da Ministan tsaron Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya kai ziyara zuwa kasar Amurka.

Nuhu Ribadu ya gana da Ministan tsaron Amurka, Pete Hegseth, da Shugaban Hafsoshin Tsaron Amurka, Janar Dan Caine, a yayin ziyarar tasa.

Ganawar ta su ta mayar da hankali kan barazanar Shugaba Donald Trump cewa zai tura sojojin Amurka zuwa Najeriya domin yakar abin da ya kira cin zarafin Kiristoci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng