Nuhu Ribadu Ya Gana da Wakilan CAN da Iyayen Daliban Neja, An Ji Abin da Suka Tattauna
- Gwamnatin tarayya ta fara zama da wadanda harin 'yan bindiga a makarantar Kotolita ta Papiri ya shafa domin tattaunawa kan ceto daliban
- Mai ba shugaban kasa shawara jan tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya gana da jagororin CAN na reshen jihar Neja da iyayen daliban da aka sace
- Wannan taro na zuwa ne bayan iyayen daliban sun koka kan rashin sanar da su halim da ake ciki a kokarin ceto 'ya'yansu daga hannun 'yan ta'adda
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Niger, Nigeria - Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya fara tattaunawa da wadanda harin 'yan bindiga a makaranta katolika ya shafa a Neja.
Nuhu Ribadu ya gudanar da muhimmin taro da shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) na Jihar Neja da tawagarsa, hukumar makaranta da iyayen ɗaliban da ’yan bindiga suka sace.

Kara karanta wannan
Sace dalibai a Neja: Ribadu ya bada tabbaci bayan ganawa da shugabannin Kiristoci

Source: Facebook
Jaridar Leadership ta rahoto cewa an gudanar da wannan zama ne a yayin da fushin jama’a ke ƙaruwa kan yadda aka yi garkuwa da ɗaliban makarantar ta kiristoci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abubuwan da Nuhu Ribadu ya tattauna da CAN
Bayanai sun nuna cewa taron ya maida hankali wajen tattaunawa game da yadda ake kokarin ceto su, haɗin gwiwar hukumomin tsaro, da kuma rawar da al’umma ke takawa wajen ganin an dawo da daliban lafiya.
A ranar 21 ga Nuwamba, ’yan bindiga sun kai farmaki makarantar Katolika ta Papiri a jihar Neja da sassafe, inda suka yi awon gaba da fiye da ɗalibai 300 da kuma malamai 12.
Wannan na daga cikin manyan sace-sacen ɗalibai da suka faru a Najeriya a ’yan shekarun nan.
CAN: Adadin daliban da aka sace a Neja
Kungiyar CAN ta tabbatar da cewa dalibai 315 da malamai 12 aka tafi da su yayin da kimanin dalibai 50 suka gudo daga hannun yan bindiga bayan kwana biyu.
Wannan hari ya faru ne kwanaki kaɗan bayan an yi garkuwa da ’yan mata 25 da ke karatu a makarantar sakandiren Maga a Jihar Kebbi.
Lamarin da ya ƙara tayar da hankalin jama’a game da matsalar tsaro da ke kara ta'azzara a makarantun Arewacin ƙasar nan, kamar yadda Vanguard ta kawo.
Iyayen daliban Neja sun yi zanga-zanga
A ranar Asabar, iyayen ɗalibai suka gudanar da zanga-zangar lumana a harabar makarantar, suna zargin gwamnati da sakaci, jinkirin ɗaukar mataki da rashin bayani kan halin da ake ciki bayan kwashe kwanaki takwas da sace 'ya'yansu.
Sun nemi gwamnati ta hanzarta ɗaukar mataki tare da samar da ingantaccen bayani game da yadda aikin ceto ke tafiya.
Domin lallashin su da kuma tattaunawa kan kokarin ceto daliban, Nuhu Ribadu ya gana da shugaban CAN na Neja da tawagarsa, da iyayen yaran da aka sace.

Source: Facebook
Tinubu ya tura sojoji dazukan Neja da Kwara
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya umurci sojoji su fantsama cikin dazuzzukan jihohin Kwara da Neja da Kebbi don murƙushe ’yan ta’adda.
Wannan mataki ya zo ne bayan harin 'yan ta'adda a Eruku da kuma garkuwa da dalibai a jihohin Neja da Kebbi a cikin mako guda.
Shugaba Tinubu ya kuma umurci rundunar sojan sama ta fadada ayyuka sintiri ta sama a cikin dazuzzukan Kwara domin gano maboyar ’yan ta’adda.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

