Jerin Wasiyyoyi 9 da Sheikh Dahiru Bauchi Ya Bar Wa Musulmai kafin Ya Rasu

Jerin Wasiyyoyi 9 da Sheikh Dahiru Bauchi Ya Bar Wa Musulmai kafin Ya Rasu

  • Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bar wasiyyoyi da dama ga iyalansa da daukacin al'ummar musulmi, har da wadanda ba 'yan Tijjaniyya ba
  • 'Dan marigayin, Dr. Abubakar Surumbai Sheikh Ɗahiru Bauchi ya tattaro wasiyyoyi tara da malamin Musuluncin ya yi kafin ya koma ga Allah SWT
  • Fitaccen malamin ya rasu a ranar Alhamis ta makon jiya kuma an yi masa jana'iza a garin Bauchi kamar yadda addinin musulunci ya tanada

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi, Nigeria - Ana ci gaba da juyayin rasuwar babban malamin addinin musulunci kuma jigo a darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Sheikh Dahiru Bauchi ya yi bankwana da duniya ne da safiyar ranar Alhamis da ta gabata, 27 ga watan Nuwamba, 2025 a wani asibiti.

Kara karanta wannan

Jerin gwamnonin da suka halarci jana'izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi Hoto: Sayyid Ibrahim Dahiru Bauchi
Source: Twitter

BBC Hausa ta yi hira da 'daya daga cikin 'ya'yansa, Dr. Abubakar Surumbai Sheikh Ɗahiru, inda ya bayyana wasu daga cikin wasiyoyin da malamin ya bar wa musulmai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dubban musulmi daga ciki da wajen Najeriya ne suka halarci jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi da aka yi a filin idi a jihar Bauchi washe garin ranar da ya rasu bayan sallar Juma'a.

Aminin marigayin, Sheikh Shariff Ibrahim Saleh ne ya jagoranci yi wa Dahiru Bauchi sallah kamar yadda ya bar wasiyya.

Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta shafi kowa

Da yake jero wasu daga cikin wasiyyoyin da mahaifinsu ya bar wa al'ummar musulmi, Dr. Abubakar Surumbai Sheikh Ɗahiru, ya ce yawanci malamin ya bayyana wasiyoyinsa ne a cikin karatuttukan da ya yi a zamanin rayuwarsa.

Dr. Surumbai ya ce rashin Sheikh Dahiru Bauchi ya shafi Musulmai da Kirista, domin kowa da irin amfani da gudummuwar da ya ba shi musamman wajen hadin kasa.

Kara karanta wannan

Allahu Akhbar: An yi jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi, an birne gawarsa a masallaci

'Dan malamin ya ce:

"Shiekh Dahiru Bauchi ya karar da rayuwarsa wajen ibada da kokarin shiryar da bayin Allah. Don haka a cikin karatuttukansa ne za mu fahimci wasiyoyinsa, da kuma irin wasiyoyin da yake yawan faɗa."

Jerin wasiyyoyi 9 daga Dahiru Bauchi

Wasiyyoyi tara da Dr. Surumbai ya tattaro daga karatuttukan Sheikh Dahiru Bauchi sun hada da:

1. Yana yawan yi wa Musulmi wasiyya da jin tsoron Allah

2. Ya yi wasiyya da yawaita karatun Alkur'ani Mai Girma da tilawarsa

3. Tsarkake niyya da yin abu don Allah

4. Gujewa kwadayi: Ma'ana mutane su kaucewa kwadayin abin duniya

5. Riko da Darikar Tijjaniyya

6. Riko da Wazifa

Kara karanta wannan

Tuna baya: Gargadin Dahiru Bauchi lokacin da Ganduje ya tube Sanusi II a Kano

7. Tabbatar da hadin kan 'ya'yansa da duka zuriyarsa bayan ya bar duniya

8. Wasiyyar hadin kai tsakanin almajiransa gaba daya

9. Tabbatar da haɗin kan Musulmin duniya baki ɗaya ko da kuwa akwai saɓanin fahimta.

Sheikh Dahiru Bauchi.
Babban malamin darikar Tijjaniyya, Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi Hoto: Mubasshir Ibrahim Kobi
Source: Facebook

Sheikh Pakistan ya yi ta'aziyyar Dahiru Bauchi

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban hukumar NAHCON na kasa, Sheikh Abdullahi Saleh Pakistan ya bayyana jimaminsa kan rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi.

Sheikh Pakistan, wanda shi ne shugaban kungiyar Izala na jihar Kano ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin, tare da bayyana gudummuwar da ya bada ga alhazan Najeriya.

Malamin na Izala ya kara da cewa shawarwarin Dahiru Bauchi sun taimaka matuƙa wajen tabbatar da alhazai sun yi abin da addini ya umarta yayin aikin hajji.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262