Tinubu Ya Lissafa Abubuwa 2 da Ya Dauka da Muhimmanci domin Jin Dadin 'Yan Najeriya
- Bola Tinubu ya ce dokar ta-ɓaci da ya ayyana kan tsaro ba sanarwa ba ce kawai, yaƙi ne da dukkan nau’o’in matsalar tsaro
- Shugaban kasar ya jaddada cewa gwamnatinsa ta bai wa muhimman abubuwa biyu fifiko domin inganta rayuwar 'yan Najeriya
- Ya tabbatar da cewa ba zai yi kasa a guiwa ba wajen tallafawa mutane masu karamin karfi da masu kananan sana'o'i
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kogi, Nigeria - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sake tabbatarwa 'yan Najeriya cewa gwamnatinsa na aiki tukuru wajen inganta rayuwarsu.
Bola Tinubu ya kuma bayyana abubuwa biyu da gwamnatinsa ta fi bai wa fifito a halin yanzu domin 'yan kasa su yi rayuwa cikin farin ciki da jin dadi.

Source: Facebook
Abubuwa 2 da Bola Tinubu ya ba fifiko
The Nation ta ruwaito cewa Tinubu ya jaddada cewa tsaro da walwalar 'yan Najeriya ne manyan abubuwan da gwamnatinsa ta fi maida hankali a kansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana haka ne a Lokoja, a wurin bikin cika shekaru 10 da rasuwar Prince Abubakar Audu, tsohon Gwamnan jihar Kogi.
Tinubu, wanda Ministan Yada Labarai da Wayar da kan Jama'a, Alhaji Mohammed Idris, ya wakilta, ya ce an ɗauki muhimman matakai domin magance kalubalen tsaro a ƙasar.
Matakan da Tinubu ya dauka kan tsaro
Shugaban ƙasar ya ce ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro na nuna irin muhimmancin da gwamnati ke bai wa kalubalen da ake fuskanta, in ji rahoton jaridar People Gazette.
Ya ce:
“Ba sanarwa kawai ba ce, yaƙi ne damuka dauri damarar yi da dukkan nau’o’in rashin tsaro a kasar nan."
Tinubu ya ce gwamnati ta fara kokarin kara yawan jami’an tsaro, samar masu da makamai na zamani, da ƙara inganta ayyukan leken asiri domin su yi aiki yadda ya kamata.
Shugaba Tinubu ya ce an bayyana Najeriya a matsayin ƙasa mai gaba da addini, amma hakan kuskurene, yana mai karawa da cewa:
“Muna kara sanar da duniya gaskiyar abubuwan da ke faruwa a Najeriya, ƙasa ce da Musulmai da Kiristoci ke rayuwa tare cikin kwanciyar hankali.”
Shugaban ƙasar ya ce gwamnati za ta ci gaba da aiki har duniya ta gane ainihin tsarin zaman lafiyar Najeriya.
Matakan Tinubu a bangaren walwala
Game da harkokin walwalar 'yan Najeriya, Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa na kara fadada shirye-shiryen tallafi da kuma farfado da kananan sana'o'i a Najeriya.
Tinubu ya ce:
“Muna fadada shirye-shiryen tallafi domin taimakawa mafi rauni, tare da inganta ƙananan masana’antu da kasuwanci.”

Source: Twitter
A cewarsa, gwamnati ta zage damtse wajen tallafa wa kanana da matsakaitan 'yan kasuwa, horar da matasa domin samun kwarewa ta zamani, inganta hanyoyin mota da layin dogo, da samar da wutar lantarki.
Najeriya za ta tona masu alaka da yan ta'adda
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ce ba da jimawa ba za ta fitar da sunayen mutanen da ke daukar nauyin ta’addanci a Najeriya.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnati ya ayyana dokar ta-baci kan tsaro da nufin kara ƙaimi wajen murkushe kungiyoyin da ke barazana ga zaman lafiyar ƙasa.
Hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce gwamnatin ta shirya yadda za ta tona duk wani mai alaka da daukar nauyin ta'adda.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


