Abubakar Malami Ya Yi Bayani game da 'Kudin Abacha' da EFCC ke Zargin Ya Yi Wasosonsu

Abubakar Malami Ya Yi Bayani game da 'Kudin Abacha' da EFCC ke Zargin Ya Yi Wasosonsu

  • Tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami ya musanta zargin da hukumar EFCC kan dawowar kuɗin Abacha da yawansu ya kai Dala miliyan 322.5
  • Ya ce maganar hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ba ta da tushe, domin har yanzu ba a kammala dawo da kudin ba
  • Malami SAN ya bayyana cewa zargin da EFCC ta yi na cewa ya yi wata makarkashiya domin samun cin hanci a kan kudin ba gaskiya ba ne

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Tsohon Babban Lauyan gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya mayar da martani kan zargin EFCC game da dawo da kuɗin Sani Abacha na $310m da riba da aka samu da ya maida kudin $322.5m.

Kara karanta wannan

"Shettima Musulmi ne": Fasto ya nemi a cire mataimakin Tinubu

A cewarsa, EFCC na zargin cin zarafi da safarar kuɗi, amma Malami ya bayyana cewa wadannan zarge-zargen ba su da tushe, ballantana makama.

Abubakar Malami ya karya zargin hukumar EFCC
Abubakar Malami, tsohon Ministan shari'a a Najeriya Hoto: Abubakar Malami SAN
Source: Twitter

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Abubakar Malami ya bayyana cewa EFCC ta ce wani lauya dan Switzerland, Enrico Monfrini, ya riga ya kammala dawo da kuɗin kafin ya shiga ofis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubakar Malami ya karyata hukumar EFCC

A cikin dogon sakon da tsohon Ministan ya wallafa, ya bayyana cewa batun an kammala dawo da 'kudin Abacha' ba gaskiya ba ne saboda kudin ba su shiga asusun gwamnati ba.

Ya ce:

“A shekarar 2016… ba a ajiye wani kuɗi a asusun Tarayya ba. Saboda haka babu wani dawo da kuɗi da aka kammala, babu batun maimaita wani sha'anin dawo da kudi.”
"Har ila yau, a Disamba 2016, lauyoyi da dama, ciki har da Monfrini, sun nemi aikin dawo da kuɗin.
“Ya saba hankali a ce wani lauya zai nemi a ba shi wannan aiki a Disamba 2016 yayin da ake zargin ya riga ya dawo da kuɗin shekaru biyu da suka gabata.'

Kara karanta wannan

Malami: Yadda ta kaya tsakanin ministan Buhari da EFCC bayan ya amsa gayyata

Yadda aka dawo da 'kudin Abacha'

Malami ya ce Monfrini ya nemi $5m wato 40% na kuɗin da aka dawo da su, daga baya aka rage zuwa 20%, wanda gwamnatin Buhari ta ki amincewa da shi.

Abubakar Malami ya ce bai yi badakala da kudin Abacha ba
Tsohon babban Ministan shari'a a Najeriya, Abubakar Malami Hoto: Abubakar Malami SAN
Source: Facebook

Ya kara da cewa daga baya, aka samu lauyoyin Najeriya da suka bayyana cewa za su yi aikin a kan a ba su 5% idan sun yi nasarar dawo da kudin.

Abubakar Malami ya ce:

“Najeriya ta samu nasarar adana 15% na kuɗin da aka dawo da su."

Malami ya jaddada cewa kuɗin da aka dawo da su sun kasance a bangarori daban-daban, ciki har da $322.5m daga Switzerland a 2017–2018 da $321m daga Jersey a 2020.

EFCC ta gayyaci Abubakar Malami

A wani labarin, kun ji cewa tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami (SAN), ya tabbatar da cewa Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gayyace shi.

Kara karanta wannan

Malami: EFFC ta gayyaci ministan Buhari kwanaki bayan cewa zai yi takara a 2027

A wata sanarwa da tsohon Ministan ya fitar a ranar Juma’a, Abubakar Malami ya bayyana cewa yana da cikakken kwarin guiwa game da tsabtar ayyukansa a lokacin da yake rike da mukami.

Tsohon ministan a mulkin Muhammadu Buhari ya ce zai ci gaba da sanar da ‘yan Najeriya duk wani ci gaba game da shari’ar domin guje wa yada labaran ƙarya ko bayanan da ba su da tushe.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng