"Shettima Musulmi ne": Fasto Ya Nemi a Cire Mataimakin Tinubu
- Faston da ke da'awar kisan kiristoci a Najeriya, Ezekiel Dachomo ya ce samun shugaban kasa da mataimakinsa duka Musulmai danniya a siyasa ne
- Ezekiel Dachomo ya zargi gwamnati da aiwatar da abin da ya kira tsarin siyasar Musulunci da nufin mayar da 'yan kasar nan Musulmai baki dayansu
- Ya yi kira ga Kiristoci su farka daga abin da ya kira barcin da suke yi, su kuma ki amincewa da kokarin da gwamantin Najeriya ke yi a kansu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Plateau – Shugaban yankin na cocin Church Of Christ in Nations Fasto Ezekiel Dachomo, ya bayyana cewa tsarin shugabanci a Najeriya daidai ya ke da yi wa kiristoci kisan kare dangi.
Ya ce abin takaici ne yadda aka samu Shugaban kasa Bola Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima dukkaninsu Musulmai, lamarin da ya kira barazana ga kiristoci.

Source: Facebook
A wata hira da ya yi da talabijin din Channels TV, Faston da ya yi shura wajen kai karar Najeriya ga Amurka a kan zargin kiristoci ya ce ana masu makarkashiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fasto ya taso Najeriya a gaba
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa Faston ya yi martani ne kan zargin hare-haren kisan kare dangi da ake zargin ana kaiwa Kiristoci a Najeriya, inda ya ce mulkin Najeriya ya tabbatar da hakan.
Ya ce:
“Shettima Musulmi ne, shugaban kasa shi ma Musulmi ne. Wannan ba kisan kare dangi bane ga Kiristoci a siyasar Najeriya? Maganin wannan shi ne a cire Shettima, kuma ina nan kan wannan matsaya."

Source: Twitter
Ya kara da cewa yana ganin ana aiwatar da wani tsari na siyasar Musulunci a Najeriya, ta hanyar musuluntar da kowa.
“Burinsu shi ne su mallaki kasa baki daya. Duk Kiristoci su farka daga barcinsu su rike Littafi Mai Tsarki, domin wadannan mutane na kokarin tilasta ko wane Kirista ya zama Musulmi."

Kara karanta wannan
Martanin Barau da gwamnatin Kano ta nemi a cafke shi saboda zargin ingiza rashin tsaro
Yadda Faston ya zaburar da 'yan uwansa
Rabaran Dachomo ya ce ba ya goyon bayan Kiristoci su ci gaba da yin shiru, domin a cewarsa, al’amuran da ke faruwa a kasar suna nuni da cewa akwai wani yunkuri na tsoratarwa da tilastawa.
Ya ce:
“Duba yadda wannan abu (yan ta'adda) ke tafiya zuwa Kwara. Me mutanen Kwara suka yi? Suna ganin duk wani abu da ya faru, sai a ce ramuwar gayya ce. Ba za mu ci gaba da yin shiru ba, saboda ba zan mika jikokinmu ga addinin Musulunci ba.”
Fasto ya je Amurka game da kiristoci
A baya, mun wallafa cewa jagora a cocin Katolika na Makurdi, Fasto Wilfred Anagbe, ya sake bayyana a gaban Majalisar Dokokin Amurka, inda ya jaddada zargin cewa Kiristoci na cikin matsala a kasar nan.
Wannan ziyarar tasa ta biyo bayan karar da kungiyoyi suka kai Majalisar Dinkin Duniya kan zargin farmakan da ake kai wa al’ummomin Kirista a wasu yankuna na kasar da niyyar karar da su baki daya.
A gaban kwamitin da ke gudanar da zaman bincike kan tsaro da hakkokin addini, Fasto Anagbe ya ce halin da ake ciki ya fi muni fiye da yadda ya bayyana a baya, saboda haka akwai bukatar a kawo dauki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

