Sauki Ya Samu: Dangote da Wasu 'Yan Kasuwa 2 Sun Sauke Farashin Litar Man Fetur

Sauki Ya Samu: Dangote da Wasu 'Yan Kasuwa 2 Sun Sauke Farashin Litar Man Fetur

  • Matatar Dangote da manyan dillalan mai sun sauke farashin fetur zuwa N840 bayan danyen man Brent ya faɗi zuwa $62
  • Rahoton masana’antu ya nuna cewa raguwar kuɗin tace mai ta sanya wa dillalan Najeriya sauya farashin sayar da fetur
  • Wannan na zuwa yayin da kasashen OPEC+ suka tabbatar da dakatar da ƙarin samar da mai a Janairu zuwa Maris na 2026

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Rahotanni sun bayyana cewa wasu manyan 'yan kasuwa a Najeriya, ciki har da matatar Dangote, sun sauke farashin man fetur zuwa N840.

Manyan 'yan kasuwar sun sauke farashin fetur din ne bayan an samu saukin farashin danyen man Brent a kasuwar duniya, wanda gangarsa ta koma $62.

Matatar man Dangote da wasu dillalai sun sauke farashin fetur
Wani bangare na matatar man fetur din Dangote da ke Legas. Hoto: Bloomberg / Contributor
Source: Getty Images

Dangote ya sauke farashin litar fetur

Binciken da jaridar Vanguard ta gudanar ya nuna cewa ragin farashin danyen mai ya jawo ragin kuɗin tacewa, wanda hakan ya sa manyan dillalan fetur suka sauke farashi a tashoshin su.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace mai martaba sarki a jihar Kwara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya tabbatar da cewa matatar Dangote, wacce ke da ƙarfin tace ganga 650,000 a rana, ta rage farashin lita zuwa N840.

Baya ga matatar Dangote, manyan kamfanonin da ke dillancin mai, irin su AIPEC da NIPCO suma sun daidaita farashinsu zuwa N840.

Sai dai wasu dillalan man suna ci gaba da sayar da litar fetur din a farashin da ya haura N840:

  • Rainoil na sayarwa kan N844.
  • Sigmund na sayarwa kan N858.
  • Master Energy na sayarwa kan N858.
  • Northwest na sayarwa kan N850.

Ya aka yi farashin danyen mai ya faɗi?

Masana sun bayyana cewa wannan sabon farashi ya nuna yadda canjin farashin danyen mai ke shafar tashoshin rarraba man fetur a Najeriya.

Raguwar farashin Brent zuwa $62 ta samo asali ne daga ƙarancin buƙatu da kuma tsoron faduwar farashin makamashi a ƙasashen Turai a lokacin sanyi.

Har ila yau, rahoton Forbes ya nuna cewa kasuwannin duniya sun rage sayen danyen mai saboda yawaitar ajiya da kuma matsalolin tattalin arziki a wasu manyan ƙasashe.

Kara karanta wannan

Kaduna: Limamin addini ya mutu a hannun 'yan ta'adda kafin a biya kudin fansa

Masana sun ce wannan na iya ci gaba muddin samar da danyen mai ya zarce buƙatar kasuwanni.

Rahoto ya nuna cewa an samu faduwar farashin gangar danyen mai zuwa $62 a duniya.
An samu saukar farashin danyen mai a kasuwar duniya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

OPEC+ ta zauna gabanin shiga 2026

A gefe guda, kasashen OPEC da suka hada da Saudiyya, Rasha, Iraki, UAE, Kuwait, Kazakhstan, Algeria da Oman sun gudanar da taro ta intanet a ranar 30 ga Nuwamba 2025 domin duba yanayin kasuwar mai da hasashen farko na shekarar 2026.

A sanarwar bayan taron, ƙungiyar ta tabbatar da matakin da ta ɗauka tun 2 ga Nuwamba 2025 na dakatar da ƙarin samar da mai daga Janairu zuwa Maris 2026, in ji rahoton OPEC.

Sun kuma ambaci yiwuwar dawo da ganga miliyan 1.65 da suka rage a baya idan aka samu bukatar hakan a kasuwar duniya, ko kuma su ƙara rage man idan farashin ya ci gaba da sauka.

Dangote ya sauke kudin lita zuwa N820

Tun da fari, a farkon Nuwamba, 2025, Legit Hausa ta rahoto cewa, matatar Dangote ta sauke farashin litar fetur daga N877 zuwa N828.

Kara karanta wannan

An fara cika umarnin Tinubu game da janye 'yan sanda daga tsaron manyan mutane

Saukar farashin ya zo ne bayan lokaci da matatar ta dauka bata yi irin wannan sauyin ba domin daidaita farashin cikin gida da yanayin kasuwar duniya.

Majalisar manyan masu kasuwancin makamashi (MEMAN) ta tabbatar da saukar farashin, inda ta ce hakan zai jawo saukar farashi a gidajen mai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com