Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Yi Magana kan Barazanar 'Yan Bindiga a Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Yi Magana kan Barazanar 'Yan Bindiga a Kano

  • Gwamnatin Kano ta ce babu wani sahihin bayanan leken asiri da ke nuna barazanar tsaro a jihar kamar yadda ake fada
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu cikakken rahoto daga shugabannin tsaro bayan taron majalisar tsaro ta jihar Kano
  • Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya gargadi jama’a da su guji yada jita-jita da rade-radi da ka iya tayar da hankula a jihar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa labaran da ke yawo kan wai akwai wata barazanar tsaro da ke tunkarar jihar ba su da tushe.

Gwamnatin ta kuma tabbatar da cewa Kano na cikin kwanciyar hankali da cikakkiyar kulawar jami’an tsaro.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwaman Kano, Sunusi Dawakin-Tofa, ya fitar a Facebook.

Kara karanta wannan

Barazanar 'yan bindiga: Gwamnatin jihar Kano ta yi magana kan 'yan acaba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron tsaron Kano da matakan da aka dauka

Sanarwar ta ce gwamnatin Kano ta ƙarfafa haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro, cibiyoyin bayanan leken asiri da sauran sassan al’umma domin tabbatar da tsaro.

An bayyana cewa an ƙara sanya idanu a dukkan sassan jihar, musamman wasu wuraren domin gudanar da aiki yadda ya kamata.

An ce dukkan rundunonin tsaro sun samu umarni na musamman, an tura su wurare dabam-dabam, kuma suna aiki ba dare ba rana domin ganin ba a samu wani gibi ba.

Gwamnan Kano ya ce ko wane yanki na Kano yana ƙarƙashin sa ido, tare da amfani da cikakken tsarin tsaro da aka kammala tsara wa.

Gargadin gwamnan Kano ga jama'a

Gwamnatin Kano ta yi kira ga mazauna jihar su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da tsoro ko ruɗani ba.

Ta kuma nemi mutane su yi amfani da shafukan sada zumunta cikin hikima, su guji yada bayanan da ba su da tushe.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kogi ta sha alwashi bayan 'yan bindiga sun tattaro fasto da masu ibada a coci

Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin gwamna Abba Kabir Yusuf na ƙara ƙoƙarin inganta tattara bayanan sirri, ƙarfafa haɗin gwiwar hukumomin tsaro da amfani da sababbin dabaru.

Gwamnatin Kano ta ce ana yin haka ne domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a dukkan sassan jihar.

Kakakin 'yan sandan jihar Kano
Mai magana da yawun 'yan sandan jihar Kano. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Punch ta ce gwamnati ta ce ba za ta lamunci duk wani yunƙuri na tada tarzoma ko barazana ga tsaro da zai kawo cikas ga zaman lafiyar Kano ba.

A ƙarshe, sanarwar ta jaddada cewa Kano ba za ta lamunci firgita al’umma ko yada bayanan karya ba, tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi:

“Kano ba za ta tsinci kanta cikin tsoro ko ruɗani sakamakon jita-jita ba.”

Barau ya yi maganar tsaro a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya yi magana kan tsaron Kano.

Barau ya bukaci Abba Kabir Yusuf ya gaggauta daukar mataki domin magance hare-haren 'yan bindiga da ake kai wa jihar.

Hakan na zuwa ne bayan Abba Kabir Yusuf ya nemi jami'an tsaro su cafke Barau Jibrin da Abdullahi Umar Ganduje kan wasu kalamansu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng