Tsohon Hadimin Tinubu Ya ba Shugaban Ƙasa Shawarar Gujewa Takara a 2027

Tsohon Hadimin Tinubu Ya ba Shugaban Ƙasa Shawarar Gujewa Takara a 2027

  • Tsohon hadimin shugaban ƙasa, Hakeem Baba-Ahmed ya ce bai kamata Bola Ahmed Tinubu ya sake neman takara ba
  • Ya ce shugaban kasan bai nuna yunƙurin gyara Najeriya kamar yadda ake tsammani ba, saboda haka ya jingine batun sake neman zabe
  • Hakeem Baba Ahmed ya ba da shawarar a nemo matashi, mai ƙoshin lafiya kuma wanda ya san abin da ya ke yi don yin takara

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Hakeem Baba-Ahmed, tsohon kakakin kungiyar dattawan Arewa (NEF), ya ce Shugaba Bola Tinubu ya fasa neman wa’adi na biyu, ya kuma nemo wanda zai gaje shi daga cikin jam’iyyar sa.

Baba-Ahmed, wanda ya yi murabus a watan Afrilu daga matsayin mashawarcin mataimakin shugaban kasa kan harkokin siyasa, ya ce akwai matsala .

Kara karanta wannan

"Mutane suna da mantuwa," Sheikh Gumi ya yi magana kan zargin goyon bayan 'yan bindiga

Hakeem Baba Ahmed ya shawarci Tinubu ya ajiye maganar takara
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Hakeem Baba Ahmed Hoto: Bayo Onanuga/Hakeem Baba Ahmed
Source: Facebook

Ya yi wannan furuci ne a hirar da aka yi da shi a shirin Sunday Politics na Channels Television inda ya ce ya dace a nemawa ƙasa mafita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An shawarci Bola Tinubu kan takara

Jaridar The Cable ta wallafa cewa Hakeem Baba Ahmed ya ce duk da kwarewar shugaban kasa a dabaru da tsare-tsare, bai nuna irin yunƙurin da ake bukata don gyara Najeriya ba.

Ya ce:

“Ina ba da haƙuri, amma dole na sake faɗin haka. Lokacin da na bar gwamnatin sa, ɗaya daga cikin abubuwan da na faɗa wa mutane shi ne, ‘Ina fatan Shugaba Tinubu ba zai sake tsayawa takara a 2027 ba."
“Tinubu ya samu damar sa, amma bai tafiyar da ƙasa yadda ya kamata ba.”

Tinubu ya samu damarsa – Hakeem Baba Ahmed

Hakeem Baba-Ahmed ya tuna da maganar shugaban kasa ta “emi lokan”, yana mai cewa ya samu damar da yake nema, amma bai gudanar da ƙasa cikin inganci ba.

Kara karanta wannan

'Maganganun Tinubu ne suka jawo': Ministan Buhari kan karuwar rashin tsaro

Ya ce:

“Tinubu da muka sani, Tinubu mai wannan basirar tsara abubuwa, bai nuna irin wannan yunƙuri na gyara abubuwa ba.”
Ana son Tinubu ya fara neman magajinsa
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

A cewarsa, kamata ya yi shugaban kasan ya nemo matashi, mara matsalar lafiya, mai nutsuwa da mayar da hankali domin ya zama ɗan takarar jam’iyyar sa.

A kalamansa:

“Ya kamata ya nemo wanda zai maye gurbinsa daga cikin jam’iyyar, matashi, mai ƙoshin lafiya, mai himma, ya tallafa masa ya tsaya.”

Ya ce idan Tinubu zai iya tafiyar da gwamnati yadda ya kamata, zai iya jan hankalin mutane daga PDP su shiga APC, saboda yana da dukkanin ƙarfin da ake bukata—amma hakan bai faru ba.

Ya ƙara da cewa halin da Najeriya ta tsinci kanta a ciki ya tabarbare matuƙa, kuma ba zai yiwu a ci gaba da tafiyar da al’amura kamar komai na tafiya daidai ba.

Matakin Tinubu ya rikita ƴan siyasa

A baya, mun ruwaito cewa bayan umarnin da Bola Tinubu ya bayar na janye jami’an 'yan sands daga gadin manyan mutane, 'yan siyasa sun fara nemawa kansu mafita.

Kara karanta wannan

Ahmad Gumi ya bada sharadin tsayawa Nnamdi Kanu a fito da shi daga kurkuku

An fara samun gaggawar ƙaruwa a buƙatar ma’aikatan NSCDC domin tsaron gidaje, iyalai da jigilar mutane, yayin da wasu jihohi kamar Ondo ke ƙara ɗaukar ma’aikatan Amotekun.

Sufeta-Janar Kayode Egbetokun ya tabbatar cewa an cire jami’an tsaro 11,566 daga gadin manya, domin mayar da su kan ayyukan tsaron jama’a da inganta tsaron rayuka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng