Man Dangote Ya Yi Kaɗan, Ƴan Kasuwa Sun Shigo da Miliyoyin Litar Fetur daga Waje

Man Dangote Ya Yi Kaɗan, Ƴan Kasuwa Sun Shigo da Miliyoyin Litar Fetur daga Waje

  • Rahoton NMDPRA ya nuna cewa matatar Dangote ta samar da lita miliyan 512 a Oktoba, ƙasa da buƙatar jama'an ƙasar
  • 'Yan kasuwa sun shigo da lita miliyan 828 na fetur daga waje, yayin da buƙatar fetur a ƙasar ta kai lita miliyan 56.7 a kullum
  • Dangote ya dage cewa matatarsa za ta iya samar da lita miliyan 45 na fetur, amma rahoton NMDPRA ya nuna akasin haka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - An samu karancin wadatar man fetur a Najeriya a cikin watan Oktoba, 2025 a cewar rahoton da hukumar kula da harkokin fetur ta NMDPRA.

Rahoton NMDPRA ya nuna cewa matatar man Dangote ta na samar da lita miliyan 17.1 na man fetur ne kawai a rana, adadin da bai kai rabin bukatar ƙasa ba.

Kara karanta wannan

Tashin hankali a Kano: Mummunar gobara ta cinye shaguna 500 a wata babbar kasuwa

Najeriya ta shigo da lita miliyan 828 na man fetur daga waje.
'Yan kasuwa sun shigo da fetur domin biyan bukatun masu sayen man a Najeriya. Hoto: Nurphoto
Source: Getty Images

An shigo da litar fetur 828m daga waje

A rahoton Fact Sheet na watan Oktoba da aka saki karshen makon nan, NMDPRA yi karin bayani game da samar da fetur a kasar, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NMDPRA ta bayyana cewa matatar Dangote ta samar da jimillar lita miliyan 512.4 na fetur a watan Oktoba, alhali kasar ta na bukatar lita biliyan 1.5.

Wannan ya sa Najeriya ta koma dogaro da shigo da fetur daga ƙasashen waje domin cike gibin, inda aka shigo da lita miliyan 828 don samar da lita miliyan 50 da ake buƙata kullum.

Rahoton ya nuna cewa yawan amfani da fetur a Najeriya ya karu zuwa lita miliyan 56.74 a rana, musamman bayan fara aikin matatar Dangode a Satumba, 2024.

Alƙawarin Dangote na samar da lita miliyan 45

A ranar 1 ga Nuwamba 2025, jami'n matatar Dangote sun sake maimaita cewa matatar ta fara samar da fetur din da zai wadatar da ƙasar ba tare da tangarda ba.

Kara karanta wannan

Fitaccen jarumin fim a Najeriya ya bayyana ana tsaka da jita jitar ya mutu

Jaridar Punch ta rahoto shugaban sashen hulɗa da jama’a na masana'antun Dangote, Anthony Chiejina, ya ce:

“Matatarmu na loda sama da lita miliyan 45 na fetur da lita miliyan 25 na dizal a kullum, abin da ya wuce bukatar Najeriya.”

A cewar Dangote, wannan ne ya sa gwamnatin tarayya ta fara tunanin sanya harajin 15% a kan shigo da man fetur da dizal, domin karfafa samar da su a gida da kuma rage dogaro kan ƙasashen waje.

Rahoton NMDPRA ya nuna cewa fetur din da matatar Dangote ta ke samarwa ya gaza bukatar 'yan Najeriya.
Matatar Dangote ta ce za ta rika samar da lita miliyan 45 a kowace rana, amma ana ganin akasin haka. Hoto: Bloomberg
Source: UGC

Najeriya ta koma dogaro da fetur daga waje

Sai dai alkalaman NMDPRA da aka fitar na watan Oktoba sun nuna cewa ba har yanzu ba a kai ga cimma wadatar man fetur a cikin gida ba tukuna.

Saboda Dangote ya gaza samar da wadataccen mai ya sa ’yan kasuwa da gwamnatin tarayya suka koma dogaro da shigo da fetur domin biyan bukatar jama’a.

Kuma rahoton hukumar ya nuna cewa, matatar Dangote ba za ta iya samar da lita miliyan 50 da kasar ke bukata ba a watan da gwamnati ta sanar da harajin shigo da mai.

Kara karanta wannan

Trump zai sake tunani kan kasashe 19 karkashin CPC bayan harin 'White House'

Gwamnati ta sanya harajin shigo da fetur

Tun da fari, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta amince da saka harajin shigo da man fetur da dizil na 15% domin karfafa masana’antun cikin gida.

Ana tunanin sabon tsarin zai iya haifar da karin farashin litar man fetur da N150, duk da cewa gwamnati ta ce tasirin ba zai wuce N100 ba.

Shugaban kasa ya umurci hukumomin da abin ya shafa su fara aiwatar da tsarin nan take, maimakon jiran wa’adin kwanaki 30 da aka tsara.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com