Mawakin Najeriya Ya Rasa Shafukan Sada Zumunta bayan Waka game da Trump
- An dakatar da shafukan Facebook da Instagram na mawaƙi Eedris Abdulkareem kwanaki bayan ya saki waka kan Donald Trump
- Rahotanni da suka gabata sun nuna cewa mawakin Najeriyan ya shafe shekaru yana wakoki da suke caccakan salon shugabanci
- Babu wani bayanin da kamfanin Meta ya fitar kan dalilin dakatarwar, lamarin da ya ƙara janyo ce-ce-ku-ce tsakanin masoyansa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – An dakatar da shafukan Facebook da Instagram na fitaccen mawaƙin Najeriya kuma mai fafutuka, Eedris Abdulkareem.
Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tattaunawa game da sabuwar wakarsa a kan Donald Trump da ta yadu a kafafen sada zumunta.

Source: Instagram
Binciken da Daily Trust ta yi da daren Lahadi ya nuna cewa ba a iya shiga shafukan mawaƙin gaba ɗaya, duk da cewa har yanzu kamfanin Meta bai fitar da sanarwa kan dalilin dakatarwar ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan abin da ya faru ya kuma faɗaɗa tambayoyi game da rawar da kafafen sada zumunta ke takawa wajen sarrafa abin da jama’a ke wallafawa
Wakar, wadda aka fitar a watan Nuwamba 2025 a ƙarƙashin Lakreem Entertainment, ta yi kama da wasika kai tsaye zuwa ga shugaban Amurka Donald Trump.
Abin da aka fada a wakar Trump
A cikin wakar, Abdulkareem ya yi zargin cewa shugabannin Najeriya suna tara dukiya a aljihunsu, alhali talakawa na fama da matsanancin wahala a ko’ina.
Legit ta rahoto cewa ya kuma jaddada karuwar sace-sace, kashe-kashe da ta’addanci, yana nuna ƙarin tabarbarewar tsaro a ƙasar.
Mawakin ya bayyana wannan ta hanyar amfani da salo na wasika domin jawo hankalin duniya kan abin da ake fuskanta a rayuwar yau da kullum a Najeriya.
Wakar “Open Letter to Donald Trump” ta biyo bayan dogon tarihin wakokin fafutuka da Abdulkareem ya yi tun shekaru da dama da suka gabata.
Tun 2004, wakarsa “Jaga Jaga” ta soki gwamnati da cin hanci, har ma aka haramta ta lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
An haramta sa wakar Eedris a Najeriya
Jaridar Punch ta rahoto cewa a watan Afrilu 2025, Hukumar NBC ta sake hana yada wakarsa “Tell Your Papa.”
Umarnin, wanda Susan Obi ta sanya wa hannu a matsayin shugabar sashen kula da yada shirye-shirye, ya zargi wakar da karya ka’idojin watsa shirye-shirye.
Hakan ya tilasta wa dukkan gidajen talabijin da radiyo a kasar su dakatar da kunna wakar, lamarin da ya sake tayar da magana game da tabbatar da ’yancin fadin albarkacin baki.

Source: Instagram
Ko da yake ya sha fuskantar suka da kuma matakan takaita wakokinsa, Abdulkareem ya ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin muryoyin da ke da karfi wajen sukar gwamnati a Najeriya.
Yana kuma amfani da kiɗa a matsayin hanya ta bayyana damuwar talakawa tare da kalubalantar shugabanni su dauki matakin da ya dace.
'Yan Najeriya zu su yi aiki da Amurka
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da wani kwamiti da zai yi aiki da Amurka kan matsalolin tsaro.
Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu ne zai jagoranci tawagar Najeriya a tattaunawar da za a yi.
An kafa kwamitin ne bayan wasu manyan jami'an Najeriya sun ziyarci Amurka a kan zargin kisan Kiristoci da Donald Trump ya yi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


