Jami’an tsaro sun cafke Abdul-Kareem da laifin doke Maigidansa a Ikeja

Jami’an tsaro sun cafke Abdul-Kareem da laifin doke Maigidansa a Ikeja

‘Yan Sanda sun damke Mawakin nan da ya yi fice, Eedris Abdul-Kareem, inda ake zarginsa da laifin yi wa Mai gidan hayansa mai suna Oladipo Abimbola duka.

Rahotanni sun ce wannan Bawan Allah, Oladipo Abimbola, ya kai karar Mawakin gaban ‘Yan Sanda ya na mai zarginsa da ci masa zarafi da kuma taso shi a gaba.

Uban dakin Mawakin, ya shaidawa hukuma cewa sabani ya shiga tsakaninsa da Tauraron ne a Ranar 3 ga Watan Junairun 2020 a wata Unguwa da ke Garin Ikeja.

Mista Oladipo Abimbola ya fadawa ‘Yan Sanda cewa ya umarci kamfanin wutar lantarki na IKED su datse layin wutan gidan Eedris saboda rashin biyan kudin wuta.

A cewar Oladipo Abimbola, kamfanin da ke da alhakin raba wutan lantarkin a yankin ya na bin Eedris Abdulkarim bashin kudin wutan da ya taru ya kai N535, 000.

KU KARANTA: Shinkafa ya nemi Jami'an tsaro su cafke tsohon Gwamnan Zamfara

Jami’an tsaro sun cafke Abdul-Kareem da laifin doke Maigidansa a Ikeja
‘Yan Sanda sun kama Mawaki Eedris Abdul-Kareem a Legas
Asali: Facebook

Tauraron Mawakin ya shiga har gidan Uban dakin na sa ne ya same shi a tsakar gida, ya shake shi domin ya yi masa duka, yayin da aka yi masa maganar bashin kudin.

Mai gidan ya kuma bayyana cewa bai da masaniyar cewa Mawakin ya ba haya a lokacin da ya saki gidan na sa, ya ce Matar Mawakin ce ta kama gidan da sunansa.

A na sa bangaren, Eedris Abdul-Kareem ya zargi wannan Mai gida da lalata da Matarsa a lokacin da ba ya gida. Eedris ya ce an yi kokarin hana shi, amma ba a dace ba.

Mawakin ya kuma zargi Uban dakin na sa da cewa an taba kama shi a wani wuri da laifin kai wa wata ‘Daliba farmaki. Har yanzu dai ‘Yan Sanda su na na bincikensu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Asali: Legit.ng

Online view pixel