Sojoji Sun Yi Musayar Wuta da 'Yan Ta'adda a Kano, An Nemi Wasu Mutane An Rasa

Sojoji Sun Yi Musayar Wuta da 'Yan Ta'adda a Kano, An Nemi Wasu Mutane An Rasa

  • Sojojin Operation MESA sun fafata da 'yan bindiga cikin dare, inda suka ceto mutum bakwai da aka yi garkuwa da su
  • An rahoto cewa 'yan bindigar sun kai hari wani kauye ne a jihar Kano, inda suka kashe dattijuwa, suka sace mutane
  • Rahotanni sun nuna cewa sojoji da 'yan ta'addan sun yi dauki ba dadi, kafin miyagun su tsere zuwa wani gari a Katsina

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Dakarun Operation MESA a karkashin Brigade ta 3 sun samu nasarar ceto mutane bakwai da aka yi garkuwa da su a karamar hukumar Tsanyawa, jihar Kano.

Sojojin sun samu wani kiran gaggawa daga mazauna Yakamaye Cikin Gari, a lokacin da 'yan bindigar suka kai masu hari cikin dare.

Sojoji da 'yan bindiga sun fafata a jihar Kano.
Dakarun sojojin Najeriya suna sintiri a wani kauye. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

'Yan bindiga sun sace mutane a Kano

Kara karanta wannan

Dubun masu garkuwa da mutane ta cika: An cafke hatsabiban 'yan bindiga a Zamfara

Harin ya faru da misalin karfe 11:30 na daren ranar 29 ga Nuwamba 2025, wanda ya tayar da hankalin jama’ar yankin sosai, in ji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami’an tsaro daga rundunar sojojin kasa, sojojin sama, da ’yan sanda, sun yi gaggawar kai dauki domin dakile ’yan bindigar da suka kai farmakin.

Rahotanni sun tabbatar da cewa zuwan sojojin cikin gaggawa ya hana yiwuwar karin barna a yankin, duk da cewa an riga an sace mutane.

Kafin zuwan jami'an tsaro, ’yan bindigan sun kashe wata mata mai kimanin shekaru 60 a kokarin firgita jama’ar yankin.

Mazauna yankin sun bayyana cewa sun shiga cikin tashin hankali, domin maharan sun bude wuta kan mai uwa da wani ba tare da tsoron zuwan jami’an tsaro ba.

'Yan bindiga sun kara da sojoji, sun tsere Katsina

Kyaftin Babatunde Zubairu, kakakin rundunar soji ta 3 Brigade ya bayyana cewa sojojin sun bi sawun ’yan bindigar har zuwa hanyar Rimaye, inda aka yi artabu.

Dakarun sun yi amfani da manyan makamai da dabaru na musamman wurin murkushe 'yan ta'addar, wanda ya bai wa wadanda aka sace damar samun kariya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da amarya da sauran 'yan biki a Sokoto

A cikin wannan fafatawa ne, aka samu damar kubutar da mutane bakwai da aka sace, wadanda a yanzu suke hannun gwamnati ana duba lafiyarsu, in ji rahoton Punch.

Sai dai bayan bincike, an gano cewa akwai mutum hudu da har yanzu ba a san inda suke ba, yayin da aka ce ’yan bindigar sun tsere zuwa Kankia da ke jihar Katsina.

'Yan ta'adda sun tsere zuwa Katsina bayan sun ji azaba daga hannun sojoji a Kano
Taswirar jihar Kano, inda 'yan bindiga suka yi artabu da sojoji bayan sun sace mutane. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sojoji sun kara tsaro a jihar Kano

Kwamandan Brigade ta 3 ya jinjinawa dakarun bisa jarumtar da suka nuna, yana mai cewa wannan aiki na nuna cigaban tsaro da ake samu a Kano.

Ya yi kira ga jama’an Kano da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai cikin lokaci domin taimakawa wajen dakile laifuffuka tun kafin su faru.

A yanzu haka, rundunar sojoji da ’yan sanda sun kara yawan sintiri domin gano sauran mutanen da ake zargin sun bace.

'Yan bindiga sun yi ta'asa a jihar Kano

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun sace akalla mutane takwas a kauyen Biresawa da ke karamar hukumar Tsanyawa, jihar Kano.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai hari a Kano, sun yi kisa da sace mutane

Wata majiya mai tushe ta sanar da cewa 'yan bindigar sun kai hari kauyen Biresawa da misalin karfe 11:00 na daren Litinin zuwa 12:00 na safiyar Talata.

An kuma rahoto cewa kauyukan da 'yan bindigar suka farmaka a ranar sun hada da Sarmawa, Yan Chibi da kuma Gano, duk a karamar hukumar Tsanyawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com