Bayan Wata 1, Likitocin Najeriya Sun Dauki Sabon Mataki kan Yajin Aiki da Suke Yi
- Likitocin NARD sun dakatar da yajin aikin da suka fara kusan wata guda, bayan sabuwar yarjejeniya da gwamnatin tarayya
- Duk da dakatar da yajin aikin, likitocin sun gargadi gwamnati cewa za su sake daukar mataki idan ba a biyan bukatunsu ba
- Yajin aikin ya bar cibiyoyin kiwon lafiya sama da 91 cikin matsanancin yanayi, yayin da likitoci 11,500 suka janye daga aiki
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kungiyar likitoci masu neman kwarewar aiki (NARD) ta dakatar da yajin aikin da ta shafe kwanaki 29 tana yi a fadin Najeriya.
Dakatarwar ta biyo bayan wani taron gaggawa na majalisar zartarwar NARD ta kasa da aka gudanar a ranar Asabar.

Source: Twitter
Likitoci sun janye yajin aiki bayan kwana 29
Shugaban kungiyar NARD, Dr. Muhammad Suleiman, ya tabbatar da janyen yajin aikin a shafinsa na X da yammacin Asabar.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kogi ta sha alwashi bayan 'yan bindiga sun tattaro fasto da masu ibada a coci
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yarjejeniyar da Aka Cimma da Gwamnati
Dr. Suleiman ya bayyana cewa an rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniya (MoU) da ta kunshi matsayin bukatu 19 da kungiyar NARD ta gabatar.
Ya ce gwamnati ta amince da warware manyan matsalolin da suka hada da biyan bashin karin albashi, biyan bashin shekaru na karin girma, aiwatar da alawus na kwararru, da mayar da likitocin Lokoja biyar bakin aikinsu.
Shugaban kungiyar likitocin ya ce an tsara cewa za a kammala warware wadannan matsalolin a cikin makonni biyu zuwa hudu.
Abubuwan da suka rage a bukatun likitoci
A cewar shugaban NARD, abubuwan da yanzu haka ake kokarin aiwatar da su sune:
- Biyan bashin karin girma: har yanzu CMD/MD ba su kammala lissafi ba, kuma an sa wa’adin makonni 4 don biyan kudin.
- Bashin albashi: an amince za a biya cikin makonni 4.
- Alawus din kwararru: ofishin shugaban ma'aikata ya bada umurni, hukumar NSIWC ta fara aiwatarwa.
- Likitoci biyar na Lokoja: an ba da umarni a maido da likitocin bakin aikinsu a asibitin koyarwa na Lokoja cikin makonni 2.
Suleiman ya kara da cewa an riga da an aiwatar da wasu bukatu, ciki har da alawus din aiki na PAT, da kuma na CONMESS 3 ga likitoci.
Dalilin dakatar da yajin aiki

Source: Twitter
Majalisar NEC ta ce likitoci sun dakatar da yajin aikin na makonni hudu domin bai wa gwamnati damar kammala aiwatar da alkawuranta.
Amma kungiyar ta jaddada cewa za ta koma yajin aiki nan take idan aka yi wasa da wannan dama.
Shugaban kungiyar ya ce duk kurakuran da suka faru ya dauka a wuyansa, matsayinsa na shugaban likitocin NARD.
Tun da aka fara yajin aikin, asibiti 91 sun shiga matsanancin yanayi saboda likitoci 11,500 sun dakatar da yajin aiki.
Wannan adadi na likitoci masu neman makamar aiki ya kunshi kaso mai yawa daga cikin likitoci 56,000 da ke cikin rajista a Najeriya.
'Akwai bukatar gwamnati ta cika alkawari' Dr. Shamsu
A zantawarmu da Dr. Shamsu Muhammad daga jihar Katsina, ya ce lokaci ya yi da gwamnati za ta nuna damuwarta kan halin da kiwon lafiya yake ciki, ta hanyar cika alkawarin da ke a yarjejeniyar da ta cimma wa da NARD.
Dr. Shamsu ya ce:
"Ya zama wajibi ga gwamnati ta cika bukatun likitocin gaba ɗaya yanzu da aka janye yajin aikin. Batutuwa kamar ƙarancin walwala, bashin albashi, da kuma matsalar hijirar likitoci zuwa kasashen waje na ci gaba da jawo tabarbarewar kiwon lafiya a kasar nan.
"Biyan bukatun likitocin shine kawai hanyar riƙe ƙwararrun likitoci da kuma gina ingantaccen tsarin kiwon lafiya ga dukkan 'yan ƙasa.
"Yajin aikin da ke faruwa akai-akai na haifar da mummunar illa ga marasa lafiyar Najeriya waɗanda suka dogara ga asibitocin gwamnati kawai.
"Ana dakatar da manyan tiyata, ana rufe dakunan shan magani, kuma aikin yau da kullum na tsayawa. Wannan na haifar da tabarbarewar lafiya da ma mutuwar marasa lafiya da za a iya kauce masu."
Dr. Shamsu ya ce yanzu ya kamata gwamnati ta ba da fifiko ga yarjejeniyar da ta cimmawa da likitocin da kuma daukar duk matakan da suka dace don inganta walwalar ma'aikatan lafiya.
'Yan Najeriya sun fara kukan tsadar jinya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, yajin aikin kungiyar likitoci ya fara jefa mutane marasa lafiya cikin wahala musamman masu karamin karfi.
Rahoto ya nuna cewa mutane sun fara karkata zuwa asibitocin kudi domin samun kulawa amma suna kuka kan tsadar kudin jinya.
Kungiyar NARD ta tsunduma yajin aiki ne a ranar Asabar, 1 ga watan Nuwamba, 2025 kuma ta ce ba za ta janye ba sai an biya bukatunta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


