Sufurin Jiragen Sama: Gwamnatin Tinubu Za Ta Karrama Dan Kano da Wasu Mutane 40
- Najeriya ta shirya taron murnar cika shekaru 100 da fara sufurin jiragen sama tun bayan saukar jirgi na farko Kano a 1925
- Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya bayyana cewa bikin na musamman zai karrama gwaraza 41 a fannin sufurinjirage
- Legit Hausa ta tattaro sunayen wadanda za a karrama, ciki har da mai kamfanin Kabo Air, watau Marigayi Muhammadu Dan Kabo
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A ranar Litinin, 1 ga Disamba, 2025, Najeriya za ta gudanar da babban taro na kasa domin bikin cika shekaru 100 da fara sufurin jiragen sama a ƙasar.
Wannan bayani ya fito ne daga wata sanarwa da mai ba Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, shawara kan harkokin yada labarai, Tunde Moshood, ya fitar a Abuja.

Source: Twitter
Bikin tunawa da saukar jirgin farko a Kano
Bikin zai gudana da misalin ƙarfe 10:00 na safe a African Hall da ke cikin babban dakin taron Bola Ahmed Tinubu, Abuja, in ji rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce za a yi duba kan tarihin samun ci gaban sufurin jiragen sama tun bayan zuwan jirgi na farko da ya sauka a Kano a 1925.
Haka kuma, bikin zai zama dandalin haɗuwa tsakanin kamfanonin jirage, hukumomin sufurin sama, masu kula da filayen jirage, kamfanonin kayan aiki, da kwararru daga bangarori daban-daban.
Akwai shirin gabatar da jawaba na musamman, haska fina-finan tarihi, da kuma gabatar da ayyukan da suka danganci ci gaban fannin sufuri.
Gwamnati za ta karrama Dan Kabo da wasu 40
Daya daga cikin manyan abubuwan da za su dauki hankali a bikin shi ne karrama manyan jarumai 41 da suka taka gagarumar rawa wajen bunkasa bangaren jiragen sama.
Festus Keyamo ya bayyana su a matsayin “gwarazan da hangen nesansu da sadaukarwarsu ta gina tushen cigaban jiragen sama a Najeriya.”
Sunayen sun haɗa da matuka jirage, injiniyoyi, kwararrun masu kula da zirga-zirgar jirage, shugabanni da masu kafa kamfanoni, kamar marigayi Alhaji Muhammad Adamu Dan Kabo na jihar Kano.
Sunayen mutane 41 da za a karrama

Source: Facebook
Duba cikakkun sunayen a kasa, kamar yadda Minista Keyamo ya wallafa hotunansu a shafinsa na Facebook:
- Capt. Robert Hayes
- Capt. Prex Porbeni
- Mrs. Folashade Odutola
- Dr. Taiwo Afolabi OON
- Capt. Fola Adeola
- Dr. Seindemi Fadeni
- Capt. Chinyere Kalu
- Chief Wale Babalakin
- Harold Demuren
- Akin Olateru
- Capt. Ado Sanusi
- Mr. George Urensi
- Mrs. Deola Yesufu
- Engr. Babatunde Obadofin
- Dr. Ayo Obilana
- Pa Odeleye AC
- Capt. Toju Ogisi
- Pa Abel Kalu Ukonu
- Capt. Felix Iheanacho
- Capt. Peter Adenihun
- Capt. Jonathan Ibrahim
- Chief Gabriel Osawaru Igbinedion
- Sir Joseph Arumemi
- Olumuyiwa Bernard Aliu
- Capt. Dele Ore
- Alhaji Dan Kabo
- Capt. Wale Makinde
- Capt. Ibrahim Mshelia
- Capt. Dapo Olumide
- Ms. Bimbo Sosina
- Chief Allen Onyema
- Capt. Benoni Briggs
- Mrs. Deola Omikunle
- Dr. Thomas Ogungbangbe
- Capt. Edward Boyo
- Dr. Gbenga Olowo
- Elder Dr. Soji Amusan
- Engr. Awogbami Clement
- Sen. Musa Adede
- Georg Eder MBA
- Chief Mbazulike Amaechi

Kara karanta wannan
An kashe mutum 2 da ƴan bindiga suka je sace dalibai a Kogi? Gwamnati ta yi martani
Kayamo ya fadi dalilin Tinubu na ba shi minista
A wani labarin, mun ruwaito cewa, ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya rubuta budaddiyar wasika ga shugaban Amurka, Donald Trump.
Keyamo ya rubuta wasika inda ya ce Najeriya ba kasa ba ce da gwamnati ke zaluntar Kiristoci, kuma shi Kirista ne mai tsayin daka a cikin kasar.
Keyamo ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya nada shi ne minista ne saboda kyakkyawar dabi'a, kishin kasa da tushensa a matsayin Kirista.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

