A Karon Farko cikin Shekaru 14, An Zabi Najeriya a Majalisar IMO Ta Duniya
- An zabi Najeriya ta shiga cikin rukunin C na Majalisar harkokin sufurin teku ta duniya watau IMO na shekarun 2026–2027
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce wannan nasara tana nuna yadda duniya ke amincewa da tasirin Najeriya a harkar sufurin teku
- Najeriya ta bayyana cewa za ta yi aiki tare da ƙasashen duniya wajen kare teku da inganta tsaro da sufurin ruwa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Bayan shekaru 14 da rasa kujerarta, Najeriya ta koma Majalisar Kula da Harkokin Teku ta Duniya watau IMO.
Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa an zabi Najeriya a Majalisar International Maritime Organisation (IMO) bayan tsawon lokaci da rasa wannan gurbi.

Source: Twitter
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, 29 ga watan Nuwamba, 2025, kamar yadda Channels tv ta kawo labarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa an zabi Najeriya ne a rukunin C, inda za ta shafe wa'adin shekaru biyu daga 2026 zuwa 2027 a Majalisar DMO.
Onanuga ya ce Najeriya ta samu nasarar komawa IMO ne a zaben da aka gudanar a taron majalisar da aka yi a birnin Landan na Birtaniya a ranar Juma’a, 28 ga Nuwamba, 2025.
Shugaba Tinubu ya ji dadin nasarar Najeriya
Shugaba Bola Tinubu ya yi farin ciki da wannan ci gaba, yana mai bayyana nasaran a matsayin shaida ta irin tasirin Najeriya a harkokin tekun duniya,
Ya ce zaben da aka yi wa Najeriya ya nuna irin rawar da take takawa wajen tsare-tsare na zirga-zirgar jiragen ruwa a duniya.
Shugaban ya ce nasarar ta nuna yadda ƙasashen duniya suka aminta da tsarin tsaron tekun Najeriya, kare muhalli, bin doka sau da kafa da ingantaccen tsarin gudanar da harkokin ruwa.
Tinubu ya yabi Oyetola da NIMASA

Kara karanta wannan
Majalisa ta tsoma baki da Jonathan ya makale a kasar da sojoji suka yi juyin mulki
Shugaban Tinubu ya yaba da kokarin Ministan Ruwa da Tattalin Arzikin Teku, Dr. Adegboyega Oyetola, ma’aikatan ma’aikatarsa, hukumar NIMASA da tawagar diflomasiyyar Najeriya,
Tinubu ya ce wadannan sun cancanci yabo saboda jajircewa da dabarun da suka yi wajen tabbatar da nasarar Najeriya a zaben, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Ya ce sabon kudirin IMO ya yi daidai da manufofin gwamnatinsa na bude damar tattalin arzikin ruwa, habaka cibiyoyin ruwa da karfafa yaki da fashin teku.

Source: Twitter
Tinubu ya tabbatar wa kasashen duniya cewa Najeriya za ta inganta tsaro a teku, taimaka wajen kare muhalli, da gina ingantaccen tsarin jigilar kayayyaki ta jiragen ruwa,
Ya gode wa dukkan kasashen da suka mara wa Najeriya baya, yana mai cewa ƙasar za ta:
“Cika amanar da aka dora mata ta hanyar bayar da jagoranci nagari da himma wajen ci gaban harkokin sufuri da tsaron teku a duniya.”
Tinubu ya nada jakadun Najeriya 3
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya aikawa majalisar dattawa da sunayen mutane uku da yake son ya nada jakadu domin tantancewa da tabbatarwa
Shugaba kasar ya ce an yi waɗannan naɗe-naɗen ne bisa tanadin sashe na 171 (1), (2)(c) da (4) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa garambawul.
Ya roki majalisar dattawa da ta duba kuma ta tabbatar da waɗannan naɗe-naɗe cikin gaggawa, inda aka mika sunayen ga kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar dattawa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

