Shugaban Hukuma a Kano Ya Caccaki Ganduje, Ya Goyi bayan Abba a Kama Tsohon Gwamna

Shugaban Hukuma a Kano Ya Caccaki Ganduje, Ya Goyi bayan Abba a Kama Tsohon Gwamna

  • Shugaban hukumar KASA, Kabiru Dakata, ya zargi wasu 'yan siyasa da nuna gazawar gwamnatin Abba Kabir Yusuf
  • Ya ce abin da ya fi damun masu adawa shi ne ci gaban da Gwamna Abba yake kawowa ta fannoni da dama a jihar
  • Dakata ya nuna goyon baya ga kiran da gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta yi na a gaggauta cafke tsohon gwamnan

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Shugaban hukumar tallace-tallace da saka alluna ta Kano (KASA), Kabiru Dakata, ya yi zarge-zarge a kan wasu siyasan jihar.

Kabiru Dakata ya bayyana cewa wadannan ƴan siyasa, daga cikinsu har da tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje suna takaicin ci gaban da gwamnatin Kano ke kawo wa jama'a.

Kara karanta wannan

Kano ta dauki zafi, Ganduje ya yi magana bayan gwamnatin Abba ta nemi a kama shi

Kabiru Dakata ya zargi Ganduje da yi wa Kano makarkashiya
Tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje, Gwamna Abba Kabir Yusuf, Kabiru Dakata Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje/Kabiru Dakata
Source: Facebook

A wani sako da ya wallafa a shafin Facebook a ranar Asabar, Dakata ya yi zargin wasu na aiki tukuru don kawo cikas ga gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kabiru Dakata ya caccaki Abdullahi Ganduje

Kabiru Dakata ya yi bayani ne bayan da gwamnatin Kano ta bayyana bukatar a kama Dr. Abdullahi Umar Ganduje saboda wasu kalamai.

Ya shaidawa Legit cewa:

“Sun yi duk abin da za su iya don kawar da gwamnanmu mai farin jini ta hanyar kotu, Allah ya kunyata su.”

Ya ce waɗannan mutane sun kafa abin da ya kira sarki na ƙarya, sannan sun so kafa gwamnatin a cikin gwamnati, kuma yanzu suna shirin kafa Hisbah ta bogi.

Dakata ya goyi bayan neman a kama Ganduje
Tsohon gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Source: Facebook

Ya ce duk waɗannan abubuwa na da manufar hana Gwamna Abba ci gaba da canza Kano ta fuskar kawo masu ayyukan alheri.

Ya ce:

“Babban tashin hankalin mutanen nan shi ne ƙoƙarin da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf yake wajen kawo ci gaba a jihar ta fannoni daban-daban da suka shafi rayuwar al’umma: ilimi, lafiya, ruwan sha, da bada jari ga mata da matasa, da kuma abin da ya shafi gina gari.”

Kara karanta wannan

Martanin Barau da gwamnatin Kano ta nemi a cafke shi saboda zargin ingiza rashin tsaro

Ya ƙara da cewa:

“Tun farko sun yi makirci da sharri. Sun yi ƙoƙarin amfani da kotu su kawar da shi, Allah ya kunyata su.”
"Daga nan suka kirkiri Sarkinsu na karya… yanzu kuma sun zo suna so su yi Hisbah ta bogi.”

Dakata ya yi ikirarin cewa irin wannan dabara na iya buɗe ƙofa ga ’yan daba, yana mai cewa ana son a yi amfani da hakan don tayar da hankalin zaman lafiya a Kano.

Martanin jama’a kan sukar Ganduje

Jama'a da dama ne suka yi martani ga ikirarin da Dakata ya yi na zargin cewa su Ganduje na yi wa Kanawa bakin ciki ayyukan ci gaba.

Almustapha Abdulmajid Sani ya ce:

“Ana so a ce an yi Askarawan Kwankwasiyya da Kwankwasiyya marshal don yi wa waccan gwamnatin makamashiya… Hmmmm munafunci dodo ne. Mun san irinku, mun iya banbance kugin ciki da na gwaiwa.”

Shi kuma Abubakar Yalleman ya ce:

“Ni kuskuren da Ganduje yayi shi ne cewa zai yi Askarawan Gandujiyya irin na Kwankwasiyya… Amma jingina abin da addini ne zai siyasantar da shi.”

Kara karanta wannan

Babbar magana: Gwamnatin Kano ta bukaci a kama tsohon shugaban APC, Ganduje

Gwamnati ta nemi a kama Ganduje

A baya, mun wallafa cewa gwamnatin Kano ta nemi a kama Abdullahi Umar Ganduje saboda wasu kalamai da take ganin suna iya tayar da tarzoma.

Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana cewa wadannan maganganu sun ba wa ƴan ta'adda kwarin gwiwa.

Gwamnatin ta ce, kadan bayan wadannan kalaman — kasa da awanni 48 — an samu rahotannin cewa ‘yan bindiga sun kutsa wasu kauyuka a iyakar jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng