'Yan Bindiga Sun Saki Bidiyo, An Ga Mata da Miji na Kuka da Hawaye Suna Rokon 'Yan Najeriya

'Yan Bindiga Sun Saki Bidiyo, An Ga Mata da Miji na Kuka da Hawaye Suna Rokon 'Yan Najeriya

  • Wasu ma'aurata da suka fada hannun masu garkuwa da mutane sun roki 'yan Najeriya su taimaka su hada kudin fansa Naira miliyan 50
  • 'Yan bindigan sun sace mata da mijin a lokacin da suke hanyar komawa gida a jihar Edo ranar 22 ga watan Nuwamba, 2025
  • A wani faifan bidoyo, an ga ma'auratan su na kuka su na rokon 'yan Najeriya su taimaka masu da kudin fansar da za a ba 'yan bindiga

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Edo, Nigeria - ’Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ma’aurata, Segiru Were da matarsa Zainab, a Aviele, kusa da Auchi, Karamar Hukumar Etsako ta Yamma da ke jihar Edo.

Bayanai sun nuna cewa maharan sun sace ma’auratan ne a ranar 22 ga Nuwamba, 2025 yayin da suke dawowa daga garin Edo zuwa gidansu da ke Aviele.

Kara karanta wannan

An gwabza fada tsakanin sojoji da 'yan Boko Haram sama da 300 a Borno

Jihar Edo.
Taswirar jihar Edo da ke Kudancin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Premium Times ta ruwato cewa masu garkuwan sun nemi kudin fansa Naira miliyan 50 kafin su sako mata da mijin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bidiyon ma'auratan ya fara yawo

A wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, an ga ma’auratan suna roko cikin hawaye, suna neman ’yan Najeriya su taimaka su tara N50m da ’yan bindigar suka bukata a matsayin kudin fansa.

Bidiyon, wanda mai fafutukar kare hakkin bil’adama, Harrison Gwamnishu, ya wallafa a X, ya nuna masu garkuwa suna nuna bindiga a kan ma’auratan yayin da suke rokon jama’a.

Mata da miji sun roki 'yan Najeriya

A cikin faifan bidiyon, an ji magidancin na cewa:

“Don Allah ku taimaka mana. Sun ce sai an biya su Naira miliyan 50, yanzu mun iya tara Naira miliyan 7 ne kawai. Matata tana da ciki, don Allah ku taimaka mana.”

Har ila yau an ga Zainab tana kuka sosai, tana zaune a kasa kusa da mijinta, kuma alamu sun nuna tana cikin gajiya da rauni.

Kara karanta wannan

Neja: An saki sunayen dalibai da ma'aikata 265 da har yanzu suke hannun ƴan bindiga

Wani mutum da ya ce 'danuwa ne ga Segiru Were, ya bayyana a bayan bidiyon cewa wani shaidar gani-da-ido ya sanar da su cewa makiyaya ne suka sace ma’auratan.

Dakarun yan sanda.
Dakarun 'yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: Nigeria Police
Source: Getty Images

Yan bindiga na neman kudi N50m

Gwamnishu ya ce ’yan bindigar sun tura bidiyon ga iyalan wadanda suka yi garkuwa da su sannan kuma sun tabbatar da bukatar Naira miliyan 50 kudin fansa.

Da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan jihar Edo, Moses Yamu, a daren Alhamis, ya ce a tura masa sakon tes amma har yanzu bai turo amsa kan lamarin ba.

Waus' yan bindiga sace mutane 11 a Kwara

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan bindiga sun kai farmaki garin Isapa da ke yankin karamar hukumar Ekiti a jihar Kwara da yammacin ranar Litinin da ta gabata.

An tattaro cewa 'yan bindigar sun sace akalla mutane 11 a harin, wanda hakan ya daga wa mutane hankali saboda yadda maharan suka tafi da wata mai juna biyu.

Rundunar yan sandan Kwara ta tabbatar da aukuwar lamarin, tana mai cewa Kwamiahinan yan sanda zai kai ziyar garin domin ganin abin da ya faru da idonsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262