An Gwabza Fada tsakanin Sojoji da 'Yan Boko Haram Sama da 300 a Borno
- 'Yan ta'addan Boko Haram dauke da makamai sun yi yunkurin kai wani ta'addanci a a garin Chibok na jihar Borno
- Dakarun sojojin Najeriya sun yi gaggawar maida martani ta hanyar fafatawa da 'yan ta'addan cikin kwarewa sosai
- Fafatawar da suka yi ta sanya 'yan ta'addan ja da baya, yayin da jiragen yaki suka rika bin su suna jefa musu bama-bama da suke guduwa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Dakarun sojojin Operation Hadin Kai (OPHK), sun dakile wani mummunan hari da mayakan ISWAP/Boko Haram suka kai wa garin Chibok na jihar Borno a daren Asabar.
Bayan sun kori maharan, jiragen yakin NAF sun yi gagarumin luguden wuta kan ’yan ta’addan da suka tsere, inda suka halaka da dama daga cikinsu.

Source: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan Boko Haram sun kai farmaki a Borno
Wata majiyar tsaro ta ce ’yan ta’adda fiye da 300 ne suka kawo hari daga bangarori da dama da misalin karfe 3:00 na dare, da niyyar korar sojoji da mamaye yankin.
Sojojin, bisa shiri, sun mayar da martani cikin kwarewa, inda suka yi artabu da maharan na tsawon sa’o’i biyu, suka tilasta musu janyewa zuwa Timbuktu Triangle.
Majiyar ta ce:
“Sojojin sun kasance cikin shiri kuma sun dakile harin ba tare da asarar rai ko kayan aiki ba."
Sojojin sama sun kashe 'yan Boko Haram
Da maharan suka fara ja da baya, sojojin kasa suka nemi taimakon sojojin sama, wanda hakan ya sa aka aika da jiragen yaki na NAF cikin gaggawa zuwa hanyar da ’yan ta’addan suka bi.
Jiragen yakin sun yi luguden wuta, inda suka kashe mayaka da dama tare da tarwatsa tafiyarsu.
Majiyoyin sun bayyana cewa NAF ta kai hari guda hudu ta sama a kan hanyar janyewar maharan, inda dukkan harin ya samu jagoranci daga bayanan sirri na sojojin da ke kasa.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun saki bidiyo, an ga mata da miji na kuka da hawaye suna rokon 'yan Najeriya

Source: Original
Harin farko ya kai ga tarin ’yan ta’addan da ke kokarin sake taruwa, sannan sauran hare-haren suka bi ragowar mayaka da suka shiga cikin dazuzzuka.
Baya ga hare-haren da jiragen sama suka kai, jirage marasa matuka sun kai wasu hare-hare da suka ci gaba da bin diddigin ’yan ta’addan, inda aka kuma halaka wasu daga cikin su tare da rushe tsarin gudunsu.
Majiyoyin sun tabbatar da cewa hadin gwiwar sojoji na kasa da sama ya tabbatar da cewa ’yan ta’addan sun samu mummunar asara, sannan an hana su yin wani sabon shiri bayan mummunan shan kaye.
Sojoji sun samu yabo
Wani mazaunin Borno, Aliyu Kabir, ya shaidawa Legit Hausa cewa ya yaba da nasarar da dakarun sojojin suka samu kan 'yan ta'addan Boko Haram.
"Nasarar da samu samu abin a yaba ce. Dakarun sojojin mu suna matukar kokari wajen tunkarar wadannan miyagun. Muna jin dadi sosai duk lokacin da muka ji aun samu nasara."
"Muna addu'ar Allah ya ci gaba da ba su nasara da kariya a kan wadannan tsinannun mutanen."
- Aliyu Kabir
Sojoji sun ragargaji 'yan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun yi raga-raga da 'yan ta'addan da suka buya cikin daji a jihar Taraba.
Dakarun sojojin sun shiga dazukan Zambana da kauyen Ayu domin kakkabe ‘yan ta’adda bayan rahotannin barazanar tsaro da ta tilasta wa mazauna yankin tserewa.
Jami'an tsaron sun yi sun yi artabu da ‘yan ta’addan tare da tilasta musu guduwa, lamarin da ya kara raunana karfin su na kai hari ko tsayawa a yankin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

