'Dan Majalisa Ya Karbi Mutane da 'Dan Bindiga Ya Saki bayan Sulhu a Katsina

'Dan Majalisa Ya Karbi Mutane da 'Dan Bindiga Ya Saki bayan Sulhu a Katsina

  • ’Yan bindiga sun saki mutane da dama da suka yi garkuwa da su a karamar hukumar Bakori da ke jihar Katsina
  • Jimillar mutanen da aka saki yanzu ta kai 82, ciki har da mata 17, jarirai 2 da maza 18 bayan makonni ana sulhu
  • Dan majalisa a yankin, Abdulraham Kandarawa ya ce sulhun al'umma ne ya haifar da nasarar, duk da cewa Gwamna ya musanta tattaunawa da su

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bakori, Katsina - Duk da ci gaba da kai hare-hare da ake a jihar Katsina da wasu yankunan Arewa, ana samun nasarar sulhu da yan bindiga.

Rahotanni sun tabbatar da cewa wani tantirin dan bindiga ya saki mutane 37 da ya yi garkuwa da su bayan yin sulhu da al'ummar karamar hukumar Bakori.

Kara karanta wannan

Ngige: Ministan Buhari ya fadawa Obi yadda 'yan ta'adda suka bude masa wuta

Dan bindiga ya saki mutane 37 a Katsina
Taswirar jihar Katsina da ke fama da matsalolin tsaro a Arewa. Hoto: Legit.
Source: Original

'Dan bindiga ya saki mutane a Katsina

Rahoton Punch ya ce an saki mutanen ne bayan dogon lokaci ana tattaunawa da neman sulhu, kamar yadda dan majalisa Abdulrahman Kandarawa ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kandarawa, wanda yake wakiltar mazabar Bakori a majalisar dokokin jihar, ya ce sakin ya kara yawan wadanda aka kubutar zuwa 82 gaba ɗaya.

Tun farko ya bayyana cewa mutane 45 sun riga sun samu ’yanci a cikin irin wannan shirin sulhu.

Yayin da yake zantawa da ’yan jarida a Katsina, ya ce mutanen da aka saki ana rike da su ne a yankin Sabe a Zamfara.

Ya ce kuma an sako su ba tare da an biya ko sisi na kudin fansa ba, sakamakon jayayya da sulhu da aka dade ana yi da ’yan bindigar.

Ya ce:

“Yau da ikon Allah mun karɓi mutanenmu baki ɗaya. Alhamdulillah, babu wanda ya rage a hannunsu.”
An yi nasarar ceto mutane 37 a Katsina bayan sulhu
Yan siyasa a Katsina yayin karbar mutane daga hannun yan bindiga. Hoto: @DanKatsina50.
Source: Twitter

Yawan mata da yara da suka kubuta

Kara karanta wannan

Daga cacar baki, matasa sun caccaka wa babban dan sanda wuka, ya sheka lahira

Majiyoyi sun tabbatar da cewa wadanda aka saki sun hada da mata 17, jarirai biyu da maza 18, cewar rahoton Bakatsine a X.

Kandarawa ya kara da cewa ’yan bindigar sun yi alkawarin sakin mutanen idan al’umma suka ci gaba da zama lafiya kuma suna cika alkawarin.

Ya yi kira:

“Muna kira ga jama’a su rungumi zaman lafiya. Idan muna da laifi, za mu gyara domin zaman lafiya ya tabbata.”

Ya yaba wa ’yan bindigan cewa sun kasance masu cika alkawari a wannan karon, tare da jaddada cewa ba a biya fansa ba.

Sai dai tun tuni, Gwamnan Katsina Dikko Radda ya sha nanatawa cewa ba gwamnati bace ke tattaunawa da ’yan bindiga, al’umma ce suka shirya sulhun.

Ya kuma yaba da dawowar zaman lafiya da irin wannan shirin ya haifar duk da cewa ana yawan samu korafe-korafe.

Yan bindiga: Tsohon mataimakin ciyaman ya tsira

An ji cewa wani tsohon mataimakin shugaban karamar hukuma a jihar Katsina ya shaki iskar yanci daga hannun yan bindiga.

A kwanakin baya 'yan bindiga suka yi garkuwa da dan siyasar a karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Ana jimamin sace dalibai, 'yan bindiga sun sake yin awon gaba da mutane a Neja

Majiyoyi sun ce yan bindigan sun rike Nasiru Abdullahi Dayi a hannunsu har na tsawon kwanaki 103 kafin ya shaki iskar 'yanci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.