Neja: An Saki Sunayen Dalibai da Ma'aikata 265 da har Yanzu Suke Hannun Ƴan Bindiga
- An sabunta sunayen wadanda aka sace daga makarantar St. Mary da ke Neja, ida har yanzu suke hannun 'yan bindiga
- Rahotanni sun nuna cewa mutum 315 aka fara tabbata da an sace su, amma daga baya aka ce 50 sun dawo gida
- Kungiyar Dioces ta Kontogora ta ce dalibai da ma'aikata 265 ne ke hannun 'yan bindigar, ciki har da 'yan nazire
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Neja - Shugabannin Katolika na Kontagora sun fitar da cikakken jerin dalibai da ma’aikatan makarantar St. Mary, Papiri, da har yanzu suke hannun ’yan bindiga.
A sabon jadawalin da aka sabunta daga na ranar 24 ga Nuwamba, an tabbatar da cewa dalibai da ma'aikata 265 ke nan a cikin daji, ba su dawo ba tun bayan harin.

Source: UGC
Jadawalin ya hada da malamai guda biyar, ma’aikatan bakwai, ɗaliban sakandare 14 da kananan yara 239 daga Naziri da Firamare, in ji rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Harin ya faru ne a ranar Juma’a, 21 ga Nuwamba 2025, lokacin da ’yan bindiga suka mamaye makarantar suka yi awon gaba da daruruwan yara da malamai.
CAN ta kara bayani kan wadanda aka sace
A baya, Kungiyar CAN ta sanar cewa mutum 50 daga cikin wadanda aka sace sun gudo, sun dawo gida kuma har sun hadu da iyayensu a ranar Lahadi.
CAN ta bayyana cewa bincike ya nuna jimillar mutum 315 aka sace, fiye da adadin farko, saboda wasu da ake tunanin sun tsira daga baya aka gano suma an sace su.
Shugaban CAN na Jihar Neja, Bishop Bulus Yohanna, ya karyata jita-jitar da ke cewa makarantar ta samu gargadin harin kafin ya faru, yana mai kiran labarin matsayin bogi da ba shi da tushe.
Matakan gaggawa daga Tinubu da hukumomin tsaro
A gefe guda, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta baci a fannin tsaro, yana mai umartar cikakken kakkabe dazuzzuka a jihar Kwara da kewaye.
Ya umarci rundunar Sojin Sama ta ƙara yawan sintirin sama a sassan da ake zargin ’yan ta’adda ke boye, domin hana karin wasu hare-hare.
Matakan sun biyo bayan yawaitar hare-hare a yankin Arewa ta Tsakiya — daga sace dalibai zuwa hari kan al’ummar karkara da wuraren ibada.
A halin yanzu, jami’an tsaro sun tsunduma cikin dazuzzuka da dama, duk da cewa ba a san tabbataccen wurin da aka kai yaran ba, in ji rahoton Premium Times.
Cikakken sunayen daliban da ke hannun 'yan bindiga

Source: UGC
Diocese ta fitar da jerin malamai da ma’aikata da suka hada da: Bitrus Yohanna, Cyril Bagudu, Mercy Yohanna, Justina Yakubu, Terry Francis, Emmanuel Ibrahim, Godwin James, Lydia Andrew, Hannatu Bulus, Yohanna Daniel Dogonyaro, Agnes Joseph, Anna Terry.
Daliban sakandare 14 da suka rage hannun 'yan bindiga su ne: Amos Kiloybas, Onah Benedict, Bulus Ezra, Anthony Linus, Dauda Zacharia, Bulus Gustave, Ejeh Mathew, Iliya John, Joshua Philip, Samaila Habila, Simon Christopher, Yohanna Cephas, Christopher Justice, Samuel Michael.

Source: Twitter

Source: Twitter

Source: Twitter

Source: Twitter

Source: Twitter

Source: Twitter

Source: Twitter
A cewar cocin, an tabbatar da dukkan sunayen nan ne bayan cikakken kirga da binciken da makarantar ta gudanar tare da iyaye da shugabannin al’umma.
Har ila yau, al’umma da dama sun fara barin yankin saboda tasirin tsoro da rashin tabbas da harin ya haifar.
'Dalibai 50 sun kubuto daga hannun 'yan bindiga
Tun da fari, mun ruwaito cewa, dalibai 50 da aka sace a makarantar St. Mary’s Papiri a jihar Neja sun samu nasarar kubutowa daga hannun 'yan bindiga.
Kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) ta bayyana cewa har yanzu dalibai 236 da wasu ma’aikata 12 da daliban sakandare 14 na hannun ’yan bindiga.
Most Rev. Bulus Dauwa Yohanna, wanda shi ne shugaban makarantar, ya ce suna da tsarin kwana da jeka-ka-dawo a makarantar, kuma sashen firamare na da dalibai 430, daga cikinsu 377 'yan makarantar kwana ne, 53 kuma ’yan je ka-ka-dawo ne.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


